🌳🌳 ⚜ 🌳🌳
🌳 🌳
👑👑
🌳
MARAICHI❣
NA
Zainab Naseer Sarki
( Zeenaseer😘)1⃣3⃣
Sai da Umma tamasa magana sannan ya rabu dasu amma gaba dayansu sunji jiki da ko motsin kirki da kyar sukeyi.
Gwara ita Sapna ta saba amma hafsa raban da a daketa harta mantah.
Sai faman huci yake ya kuma dakawa sapna tsawa baza ki tashiba saina miki wanda ya fi wannan.
Gaba daya bata iya kukan hawayene wani kebin wani gaba daya jikinta babu inda baya mata ciwo.
Jikinta na karkawa Har dingisawa take haka ta lallaba ta nufi part dinsa kamar ta mutu ta huta takeji.
Kafin ta karasa dakin ta tsaya ta fashe da wani irin kuka gaba daya batajin ddin rayuwata abun ya isheta tun kafin ta zama babba gaba daya sun lalata mata rayuwa konina taban dukane ajikinta.
Ba kowa tsakar gidan sai hafsa.
Da ker ta lallaba ta shige daki saboda kafarta data rike.
Toilet ta nufa ta hada ruwan zafi dan tabbas saita gasa jikinta gaba daya tausayin Sapna take ji haka ta daure ta gasa jikinta.
Riga maras nauyi ta sanya sannan tasha magani ta kunna fanka ta kwanta nan da nan zazzabi ya rufeta tabbas Sapna taci gaba da rayuwar gidan nan wata rana sai ta mutu.Saida tasha kukanta ta koshi sannan ta fude kofar dakin Har muryar ta ta dashe sabo da kuka.
Tana zaune kan kujera taci wasu en iskan kaya ba alamun murmushi a fuskarta.
Ahankali ta karaso kusa da ita tareda durkusawa Har lokacin hawayen na zubowa daga idanunta.
Dan girma Allah Anty kiyi hakuri yaya yama dakeni dan Allah ta kuma fashewa da kuka.
Ko kallanta batayi saida tayi kukanta mai isarta sannan tayi shiru.
Kin gama kukan ?
Eh ta gyada mata kai to tashi kije cikin wardrobe dina na manta ban baki inner wears dina ki wankemin dazu kuma sun taru da yawa.
Toh tamike ta nufi dakin da sauri.
Har takusa kaiwa bakin kofa tace keh dakata.
Saura kimin jika jika Wallahi in basu fitaba saikin sake wankewa ko zaki kwana kinayi bai dameniba.
Toh insha Allah, jikinta sai bari yake dan batasan yin ko kuskure
Daya akuma dukanta dan tana da tambacin ana kuma dukanta mutuwama zatayi.
Tana shiga ta daukosu masu uban yawa sai faman tsami suke.
Haka ta hada ta shiga baya inda suke dibar ruwa ta shiga wankewa iya,iyawarta Har aka kira sallah magrib bata gamaba sai gaf da insha ta gama sannan ta shigo falon da shiga inda zata shanya mata.
Batama lura dasuba ta kusa kaiwa corridor da zata shiga ta kira sunan ta.
Da sauri ta juyo dan tama tsorata.
Naam.
Tana kwance jikin Abba sai kace mage shikuma sai wani kallan TV yake kamar ta kashe su da haushi.
Zo muga irin wanki da kikamin karki ahanyamin kaya basu fitaba.
Nan danan jikinta yayi sanyi dan tasan ba mutunci gareta baza iya cewa basu fitaba.
Amma tas suka fita duk taji ciwo a hannunta saboda dirza su da takeyi.
Gashi ta mika mata bokitin tana karkawa.
Tassss! Baki da hankaline haka aka koya miki wanki agidanku.
Cilla mata bokin tayi Har kanta ya buga nan da nan gurin ta tashi.
Haba Dallah kalli kayan duk basubfitaba take fadawa Abba.
Shikuma yace da ita toh ai saiki tashi ki kuma wanke mata.
Kwallah fal idanta ta mike ta dauki bokitin ta koma dashi.Tana kuka tana wankin ga hannunta sai jini yake kanta ma yana ta ciwo kai ko inama ciwo yake mata gaba daya tama rasa abunda zatayi dan kukanma ta gaji da yinsa.
Sai 10pm ta gama wankin sannan ta dauka ta tafi dan ta nuna mata amma basa falon.
Tafiya tayi ta shanya mata kayan sannan ta fita zuwa daki.
Tana shiga bataga hafsa a falonba zama tayi kan kujera tana hutawa.
Idanunta ta lumshe hawayen na zuba ta gefan idanunta.
Ahankali ta fito daga dakin ganin Sapna zaune kan kujera ta karaso kusa da ita ta zauna tareda dafata.
Idanunta ta bude ahankali kwallar data makale takarsa zubowa.
Itama hafsa kwallar take ahankali ta sanya hanunta tana sharemata kwallar tareda girgiza mata kai alamun ta dena kuka.
Cikin muryar kuka tace dan Allah ya hafsa kiyi hakuri duk ni naja miki wall......
Rufe mata baki tayi da hannunta tareda rungume.
Ba laifinki bane Sapna nice naja miki duka dan Allah kiyi hakuri tana jikin hafsar tana ta faman kuka.
Ya hafsa wai meyasa kowa baya sona ko inayin Abu marar kyaune Wallahi zan dena dan Allah me nakeyi.
Shhhhh! Babu wanda ya tsaneki ki bar wannan maganar.kowa yana sanki kuma kece meyin Abu mekyau babu abunda kike mara kyau.
Kandarece Allah ya dora miki tun kina yarinyarki.ki rinka addu'a Allah ubangiji ya sa kicinye jarabawar nan kinji.
Gyada kanta tayi tare da fadin insha Allah.
Yawwa yr Albarka kuma ko baki da lafy kina daurewa kina zuwa makaranta kinji.
Maza kije kiyi sallah kizo kici abinci.
Ahankali ta raba jikinta dana hafsa ta mike ta nufi toilet.
Ahankali hafsa ta sauke Ajjiyar zuciya ta jingina da jikin kujerar tana tunanin yanda rayuwar Sapna zata kasance nan gaba.Saida ta yi wanka tayi sallah sannan taci abinci hafsa ta bata maganin tasha.
Kwanciya sukayi kan gado.
Bara nayi miki massage princess kai ya hafsa nice princess din.
Sosaima kuwa kinma fi princess agurina.
Ahankali ta rinka danna mata kafarta da jikinta.
Itama taji ddi sosai saida ta tuna da mamansu lokacin da suke mata ita da Shaheeda suna dariya.
Hawaye ne ya gangaro mata a haka Har bcci ya dauketa..
Saida hafsa taga tayi bacci sannan ta matsa kusa da fuskarta tana da dakallanta.
Ta kara fari duk ta fada fuskar tayi fayau dama ba Makeup take ba.
Addu'a tayi musu sannan ta safe jikinsu da ita...☺😘😘😘😘😘😘😘😘😘😘
01 Amal fansclub 💅🏻🌷Written by Zeenaseer😘

YOU ARE READING
MARAICHI
Non-FictionLabarine na yara gudu biyu,wanda zusu taso cikin rashin kulawa da gata na iyayansu,sakamakon matar mahaifinsu. Labarine me fada karwa,nisha dan tarwa yana dauke da tausayi, soyayya da kuma karamci...