🌳🌳. ⚜. 🌳🌳
🌳. 🌳
👑👑
🌳🌳
🌳
MARAICHI❣
NA
Zainab Naseer Sarki
(Zeenaseer😘)🎊🎊🎊🎊🎊🎊🎊
I dedicated dis page to oll by fans Lov u so much Fata nagari gareku kuma ina muka murna da shigowa sabowar shekara Allah kasa munshiga cikinta tareda tarin alkhari daga Allah ubangiji subhanahu wata'ala.
Wish u appy new year and wlcm to 2017.
🎉🎉🎉🎉🎉🎉🎉
Another new year is here!
Another year to live!
To banish worry,doubt and fear,to love and laugh give🤗
HAPPY NEW YEAR
💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼😂😘.BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.
0⃣1⃣
Hadarine ya hado garin gaba daya yayi duhu,ga iska me karfi anata faman yi mutane sai faman sauri suke kar ruwa ya iske su.
Wasu suna gudu wasuna hada kaya.
Sai faman buga kofofin gidaje iskar akeyi.
Wani gida na hango gidan babbane ba laifi kofar gidan safe yake da siminti sai kofa maidan fadi,irin gidan nan ne dasai kin huce soro tukun zaki shiga cikin gidan.
Tsakar gidan babbace sai dakuna guda hudu acikinsa sai kitchen da ban daki.
Saikuma wani daki hanyar fita daga gidan wato daga cikin soran.
An malale tsakar gidan da siminti shima sai rijiya daga can nesa.
Ko wani daki ciki da rumfane.
Saka makwan iskan da akeyi ne gidan babu kowa cikinsa da alama duk suna cikin daki.
Dakin farko na leka zauna cikin falon na hango wata yr yarinya saman kujera ta takure da alama sanyi take ji kyakyawace tana da gashi amma fatar jikinta ba fara bace saide akirata da chocolate sanye take da riga fara me hannun singlet da chain a huyanta.
Saikuma wata yr karama akwance akan dayar kujerar da alama bacci takeyi shekarunta fazasu haura uku ba.ita kuma ta farkon nata shekarun basu gaza goma zuwa sha daya ba.
Cikin dakin na shiga wata mata na gani wanda shekarunta fasu gaza 30 ba kyakyawa fara tas dauke take da tsohon ciki haihuwa ko yau ko gobe.
Tsaye take jikin wardrobe da alama kaya zata dauka.
Fitowa tayi falon ta zauna kan daya daga cikin kujerun.
Nan ruwa ya sauka ba tsayawa sosai akeyin ruwan tareda walkiya.
Sapna matar ta furta tana kallon yar tat dake zaune saman kujera.
Taso ki amshi wannan rigar ki sanya tunda naga kamar garin ya fara daukar sanyi.
Kuma ki dauki hularki ki sanya bakya San zama da dankwali ko kadan.
Mikewa tayi tareda kara sowa wajan matar.amsar rigar tayi tareda da juyawa zata koma ta zauna.
Riko hannun ta matar tayi tare da fadin me nene kuma sapna.
Hawaye ne suka fara bin kuncinta kanta akasa tama kasa kallan matar.
Hannun ta tasanya ta goge hawayen tareda fadin mama cikin muryar ta me sanyi Safiya ce ta kwashe mun littattafaina gaba daya wai ba zanyi karatu ba ta zubar min dasu akan hanya da zamu dawo daga makaranta dan kar nayi pass a exam na huceta.
Amma meyasa baki gayamin ba tun daxu.
Cewa tayi inna fada gobe sai ta taru da frnds dinta sun yimin doka.
Haba Sapna duk da nasan safiya yayar kice be kamata ki tsaya kina yimata kukaba.
Gaba daya wannan miskilancin naki haushi yake bani wlh.
Kuma kinsan halin su sarai to Wallahi ki kiyaye ni narasa wata irin jarabace wannna Wallahi nagaji hakuri ya kare ina dalili gwarama nayi na haihu nabar gidan nan kullum nida yarana bamuda zaman lafiya.
Bara dan asabe ya shigo nagaya masa yadau mataki.
Huce kisanya rigar kiyi alwala ankusa sallah magrib.
Rigar hannun ta tashiga sawa.Ahankali ta bude idanunta tareda mikewa zaune.kaf idanun ta suka sauka kan Sapna dake tsaye tana saka riga.
Ya Sapna ina sweet dina da kikace zaki siyomin a makalantan Ku.
Kai Shaheeda daga tashin ki kya bari mana kici abinci.
Kanta ta makale jikin kafadarta alamun Aa.
Kinga karasa saka rigar ki dauko mata inde kin siyo mata dan kinsan halin wannan yarinyar da shegen taurin kai ki dauko mata dan yanzu abincinma saitace baza taciba.
Daki ta nufa ta dauko mata tareda mika mata.
Amsa tayi ta duba tareda cilli da ita ta huntsila kan kujerar ta fara kuka.
Maman tasuce toh uwar rigima menene kuma baga alewar nan ba.
Mama Wallahi dan tsinken jikinta ne ya fita shine ita wai baza tasha ba.
Kinga shaheeda ta taso kinji bazamu unguwa da Sapna ba mukadai zamu tafi taho kinji.
Jiya mata bayama tayi dan bama tasan kallan su kukanta take tsakani da Allah.
Kinga dauko tsinken inde yana nan ayi dubara inba hakaba Wallahi bazata barmu muyi bacci da ddin raiba.
Cikin jakar ta shiga dubawa dakyar ta lalubo tsinken ta mikawa Maman taso.
Danko alawar Sapna ayi dabara ko shinken zai gyaru.
Alawar data cilla karkashin kujera Sapna ta dauko tare da mikawa Maman tasu.
Ahankali ta maida tsinkin tayi er dabara ta mika mata.
Taso ki amsa gashi yanzu tsuntsu ya kawomin ita taho ki amsa karya kwace kayar sa yace ya fasa.
Tasowa tayi ta matso kusa da Maman tasu ta amsa tareda dubata sosai sannan ta yadda daga gurin tsuntsu take dan akwai tsinke ajikinta.
Yauwa yarinyar kirki yanzu kawo a ynma baby ta fada tare da nuna cikinta.
Aa bajan bachiba chima baya bani naci.
Kai yr kirki yacefa inya zo ke kadaice zaki rinka goyashi kina mai wanka in kika hanashi bazai yanda ki dauke shiba.
Itade Sapna na zaune tana daure gashinta tana murmushi tana kallan rigimar Shaheeda yarinya karama sai fada.
Wallahi mama banil bachiba kaya Jo din.kuma nila malin bashi abuna ma ko ya Sapna ta fada tareda maida hannayan ta baya ta langwabe kanta.
Itade Sapna mikewa tayi ta nufi toilet tareda fadin yanda kikaso.Bayan sun idar da sallah suna zaune a falo suna kallon cartoon mamansu na cikin daki.
Dan Asabe ne ya shigo dakin da sallah.
Da gudu Shaheeda ta sakko daga kan kujera ta dane shi ya dagata sama tana dariya.sannan ya zauna tareda dorata kan ciyarshi.
Yaya kacan yau ko cuncu ya kawomin alawa daga shama.
Haba ! Sarkin surutu kin bawa Sapna.
Zamowa ta danyi daga kan kujerar tareda fadin yaya ina yin,
Lafiya qlau Sapna ya skul din.
Lafiya qlau yaya gobe zamu fara exam.
Gud Allah ya kaimu ya kuma bada sa'a.
Maman suce ta fito daga dakin sanye da hijab.
Dan Asabe ne?
Nine inayini .
Lafiya qlau ya aiki.
Alhmdullh NA shigo sarkin labari tana bani.
Wani irin sarkin labari kuma sarkin rigima kai.
Dariya yayi tareda mika wa Sapna ledar hannun sa.
Ga ice cream nan aje asha.
Aikuwa Shaheeda naji ta koce ledar tareda komawa jikin Maman ta boye wai bazatsha ba tunda ta siyo mata alawa maras tsinke.
Rabu da ita Abu da yanzu zatayi bacci cigaba da kallanki.
Shima dariyar yayi.sannan yace babu wata matsala ko Aunty.
Wallahi babu komai saita ya rannan Sapna da safiya na rasa gane Kansu kullum cikin fada yauma sunje sunyi gaba daya ta kwashe littafan Sapna ta watsar kuma gobe zasu fara exam.
Shiru yayi nadan lokaci sannan yace jeki kira min safiyar.
Ahankali ta mike ta nufi dakin su safiyar abakin kofa sukaci karo tafito.
Dallacan ki bani guri mutun sai kace dabba.
Yaya dan Asabe ke kiranki.
Bata jira amsar taba ta huce ta koma daki.
Koda ta dawo bata koma kan kujerar ba kusa da yayan ta zauna tare da fadin gatanan zuwa.
Da sallama ta shigo sanin yayan nasu na dakin kuma tasan halinsa.
Jikinta a sanyaye ta zauna kusa da Sapna tareda fadin yaya gani.
Kallan su yashiga yi na dan lokaci kafin yace bana hanaku fada ba?
Safiya ce tace Wallahi yaya itace w..
Zaki min shiru kosainaci mutuncin ki,koma me ta miki ba mutane agidanne da bazaki gaya musu ba zaki zubar mata da lintafanta.
Tashi kije ki dauko mata naki.
Tsayawa tayi tana kumbure kumbure.
Ba magana nake miki ba?.
Yaya bata kwafar note kullum duk note enta incomplete ne.
Tsaye ta mike tayi baya tana kallonsa Har idanta sun fara ruwa.
Dama abunda kike kenan a skul din taku,shiyasa kenan kullum kina cikin en last 5.
Wallahi tallahi zaki gamu dani inde a wannan exam din kika fadi ke ko average kika ci nida kene.
Sapna kiyi hakuri kinji kuna yin karatun keda frnds dinki ni kadai nasan mezan siya miki wannan karan.
Mama dake zaune tana bama Shaheeda ice cream Har tayi bcci ajikinta.
Mama yayima saida safe sannan ya fita daga dakin.
Itama safiyar fita tayi tana kuka..❣❣❣❣❣❣❣
Muah........my pple in
01 Amal fansclub💅🏻🌷👑👑
Written by Zeenaseer😘
YOU ARE READING
MARAICHI
Non-FictionLabarine na yara gudu biyu,wanda zusu taso cikin rashin kulawa da gata na iyayansu,sakamakon matar mahaifinsu. Labarine me fada karwa,nisha dan tarwa yana dauke da tausayi, soyayya da kuma karamci...