MARAICHI

4.1K 140 86
                                    

🌳🌳        ⚜       🌳🌳
🌳                              🌳
               👑👑
                 🌳
      MARAICHI❣
            NA
Zainab Naseer Sarki
     (Zeenaseer😘)

3⃣0⃣
     
         Dis page goes to 💋💋Precious writer✍🏻
  Ubngiji Allah ba barmu tare ya kara basira da kuma kwarin ido ya kuma karemu daga Sharrin makiya da mahassada.
     Ya kuma daukakamu ya bamu abunda muke nema ya cika mana burikanmu na alkhair😍😍😍
   


         Bayan sun idar da sallah ta gyara fuskarta suka fita itada sapna suna hira gwanin ban sha'awa sai labarin makarantar su take bama sapna tana dariya Har suka karasa gidan.
    Da gudu Shaheeda ta shiga tare da rungume Najar tana murnar ganinta.
    Sapna murmushi kawai takeyi tana kallan yanda kanwar tata kema Aunty Najar shagwaba ita kuma tana biye mata.
    Zama tayi kan kujera tare da fadin Aunty ina yini.
   Lafiya qlau Sapna ya karatu da kuma en gidan.
   Kowa lafiya Aunty.
Toh masha Allah.
     Aunty kince innayi kokari zaki shiya min waya ko.
   Eh hakafa nace yr kirki.
   Toh mun kusa fara jarabawa zanyi kokari dan asiyamin waya.
   Sapna dake zaune tace ke kuma me zakiyi da waya.
   Kaiii! Ya Sapna kefa zan bawa.dan nima a makarnta in ana labari ince nima sis ina tana da waya.
   Dariya sukayi dukansu dan tabasu dariya barin yanayin yanda tayi maganar.
    Lallai wata yarinya nasan yayarta da yawa.Aunty Naja ta fada.
   Hira suka tayi wani lkcn Sapna na sako baki wani lkcn ko saide tayi dariya.
    Har kusan magrib sannan aka aiko ana kiran Shaheeda da yake in tazo dan Asaban cewa yake ta tafi gidan Naja saiyaje can ya dauketa.
    Nan ta mike ta fara saka takalminta.
  Har waje Sapna ta rakota dan zata tafi gida Har tayima Naja sallama.
    Yana cikin mota a zaune.
   Hannun ta rike dana Shaheeda ta karaso wajan duk da tasan ba wani kulata zaiyi bah.
    Har kusa da side dinsa tazo yayin da ita kuma Shaheeda ta zagaya dan shiga.
   
    Kamar zatayi kuka tace yaya ina yini.ko kallan idan take beyiba ya ja motar yabar gurin.
Tana kallan motar Har ta bar lafin wata kwallace ta kuma cuko idanta.
   Ahankali ta sanya hannunta ta goge tare da bin hanyar tafiya gida cikin nutsuwa.
   Ahankali motar sa tayi parking agabanta.
Fitowa yayi sanye yake cikin blueback jeans da White shirt.sai bakin space a idansa.
Kyakyawa ne Dogo amma baza a kirashi da baki ba irin chocolate colour din nanne gashi ya hada da Hutu shiyasa aina yin colour dinsa ya fito.
Guy din ya hadu sosai.
     Cikin takunsa na kasaita ya karo Har inda ita ke yatsa.
   Itama tunda ya fito take binshi da ido dan ya burgeta.
   Cikin sanyin murya ya furta yn mata sannufa.
   Batareda ta kula shiba ta fara neman hanyar hucewa.
    Gabanta ya shiga tare da zare glass din idanunsa.
    Ya kuma zaki tafi bakiji meke tafe dani bah.
    Ahankali ta furta kayi hakuri ina saurine magrib ta kusa kuma za'a iya yimin fada a gida.
   Toh shikenan naji ki yimin kwatancan gidan naku.
   Da Sauri ta dago kai ta kalleshi.
    Shima itan yake kallo gira ya daga mata alamun eh!
   Kanta ta sauke da sauri tare da fadin hakanma bazai yiyu ba pls ka barni na tafi ina tsoran karnayi dare.
    Ohk! Naji hannun sa ya sanya cikin aljihun sa tare da fito da wata yr madedeciyar waya kirar iPhone5 ya mika mata tare da fadin gashinan pls in kin koma gidan ina San yin magana dake.
    Kallan sa ta tsaya yi tare da fadin waya cefa ka bani.
   Eh fah nasani ai dan Allah ki karba mana.
     Kanta ta shiga girgiza tare da fadin gaskiya ka rike kayanka kayi hakuri na gode amma bazan iya amsaba.
    Nikuma saikin amsa ko kuma duk inda kikayi saina biki.
     Dan Allah ka rufamin asiri wlh inna amsa fada za'a yimin a gida.
    Babu wanda zai miki fada amma in baki amsa bane za'a miki fadan.
    Jikinta na dar dar ta amsa tare da hucewa gaba.
   Murya yadan daga tare da fadin ba sallama.
    Ita kuwa ganin lokacin da wowar Abba ya kusa ya sanya take sauri gashi yana neman bata mata lokaci.shiyasa ta amshi wayar.

    Da sallama ta shiga cikin gidan fanin bai dawoba ya sanyata jin ddi.
   Alwala tayi dan gabatar da sallah magrib. Bayan ta idarne tana zaune tana addu'a taji karan waya.harta dan tsorata sai kuma ta tuna da wayar dazu.
    Mikewa tayi tare da kulle dakin dan kar Safiya ta ganta tana waya.
    Bata sha wahalaba dan gane yanda ake daga kiraba dan irin wayar Husnah ce komai da komai kuma tana ganin yanda ake amfani da ita.
      Da sallama ta kara a kunnan ta.
  Shima amsa mata sallamar yayi.
Sannan yace da fatan ina waya da sapna.
    Eh ta amsa tare da fadin amma ya akai kasan sunana.
    Murmushi ya danyi kafin yace bakiji hausawa na fadin Mesan abunka ya fika dabara bah.
    Uhmmm! Kawai ta iya cewa.
    Wato sapna a gaskiya na jima ina kaunarki amma Allah yayi sai yau muka hadu.tun ranar dana fara ganin ki na rinka bibiyarki harna gano ko ke wacece.
       Nide sunana Kamal kuma kuma iyayena haifaffun yn garin nanne amma muna zaune a Kaduna yanxu hakama naxo gidan kakanninane.
     Shiru tayi tanata faman sauraransa.
    Yanaji kinyi shiru bakice komaiba.
    Murmushi tayi tare da fadin toh me kakeso nace.
   So nake ki bani amsar bayata insan amatsayin da nake ciki.
    Kayi hakuri gaskiya kadan bani kona biyu.
   Shikenan insha Allah, nagode I Lov u sannan ya kashe wayar.
    Tsayawa tayi tana kallan wayar kamar karya dena magana.
    Murmushi takumayi tabbas babu macan da zataga Kamal bata kyasaba.
Amma ita ya zatayi yanzu itada ko sakewa batayi a gida bare a ganta tana hira da wani.
    Zuciyar tace ta bata shawarar kawai ta rabu da shi ta hutama kanta.
    Kashe wayar tayi gaba daya tare da zuwa ta boyeta cikin kayanta.
   

       Shi kuwa kamal yana gama waya da Sapna ya nufi fridge din  dakin tare da dauko katuwar kwalvar giya.ya bude ya kafa kai yasha ya koshi sannan yayi gyatsa.
    Sannan yayi murmushi tare da fadin burina ya kusan cika.
    Da wata mahaukaciyar dariya ya kuma kyalkyalawa sannan ya mike tare da daukar sauran kwalbar ya fita daga dakin yana sha yana maganganu shi kadai.

😘😘😘😘😘😘😘😘😘😘
  01 Amal fansclub 💅🏻🌷

Written by Zeenaseer😘

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Mar 10, 2017 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

MARAICHIWhere stories live. Discover now