MARAICHI

1.2K 52 1
                                    

🌳🌳       ⚜        🌳🌳
🌳                              🌳
              👑👑
                 🌳
      MARAICHI❣
             NA
Zainab Naseer Sarki
     ( Zeenaseer😘)

2⃣9⃣


•••••• kallanta Shaheeda keyi da mamaki tare da fadin ya lafiya menene.
    Tsaye ta mike tana yarfe hannu tana durawa akai ta kasa tsayawa waje daya.
   Haba yaya wai meye duk kabi kika wani rude kamar wanda tayi kisan kai.
   Gaba daya ta kasa magana sai da ya kuma kwalla mata wani kiran sannan ta fice da sauri batare da tabi takan Shaheeda dake tsaye tana tmbayartaba.
    Da gudu itama ta bita suka fice tsakar gidan.
     
    Tsaye yake a tsakar gidan yana jiran fitowar ta daga cikin dakin yadaure fuska babu alamun murmushi atare dashi.
    Matsawa tayi gurinsa tare da durkusa jikinta na rawa murya na karkarwa tace yaya gani.
    Ita kuwa Shaheeda tana tsaye kofar daki tana mamakin yanda duk Sapna ta wani rude kan ya Abban babba da ita.
Ai gani take ko kita karama bazata rinka rawar jiki akan saba.
Tsaki taja dan tsabar jin haushin ta.

   Tun dazo me kikeyine kinaji ina kiranki kika yimin shiru.
    Am..m..um. Ba shiru nayiba na amsa bakaji bane.
   Toh kije ki yima Rahma duk abunda ya dace bata da lafiya ne.
   Toh ta fada da sauri.
Kanta a kasa.
    Harya juya zai tafi ya hango Shaheeda tsaye bakin kofa tana kallansa cike da jin haushi da tsanarsa.
Cikin tsawa yace ke baki iya gaida mutane bane.
    Kallansa tayi tare da zunbura baki alamun shagwaba sannan ta shige dakin ta kulle.
    Tsaki yayi ya fice dan zata iya bata masa lokaci.

   Mikewa tayi sannan ta fara knocking dakin dan Shaheeda ta bude.
   Ahankali ta mike daga kan kujera ta bude mata dakin.
   Tana shigowa itama ta zauna tare da sauke wata Ajjiyar zuciya sannan ta kalli Shaheeda da murmushi kafin tace bara naje na dawo yr kanwata.
    Tashi tayi tare da fadin aa wallah yaya saikin ci abunda na kawo miki maybe ma baki karyaba.
    Murmushi tayi tare da fadin you boss.
   Dukansu suka yi dariya.
Saida taci biscuit da juice din harta koshi sannan tace zan iya tafiya.
    Itama mikewa tayi tare da fadin mutafi tare saina tayaki aikin.

Tare suka fito daga cikin dakin sannan suka nufi part din Abban suna tafe suna hira Har suka karasa.
   Da sallama suka shiga cikin falon,ganin ba kowa ya sanyasu shigewa.zama shaheeda tayi kan kujera tana karewa dakin kallo ba laifi dakin yayi kyau ta fada a zuciyarta.
     Kitchen ta nufa ta fara gyarawa sannan ta dura abinci.
    Suna hira da dariyar su tana aikin itama tana tayata da wani abun Har ta kammala komai.
   Tunda suka shigo cikin gidan Rahma bata fito ba hakan ya ba Sapna damar sakin jikinta tayi aikinta a nutse harta gama.
     Saida suna gaf da gamawa sannan ta leko daga cikin dakin tace da Sapna ta kawo mata abinci.
    Zubawa tayi ta hada komai sannan ta bawa Shaheeda ta kai mata.
   Ansa tayi ta nufi dakin,da sallama ta shiga cikin dakin.
   Tana zaune a gaban mirror tana kwalliya.
  Anje mata abincin tayi tare da nufar kofa zata fita.
   Tunda ta shigo take kallanta ta mudubin yarinyar ta burgeta sosai duk da ba wata babba bace.
     Ke kuma daga ina haka zaki shigoma mutane daki babu sallam balle ki gaida mutun.
    Ya Sapna ce ta aikoni in kawo abinci koma na kawo.tana kaiwa nan ta fice daga cikin dakin.
    Cike da mamakin maganganun yarinyar ta juyo tana kallan kofar tana tunanin duk inda yarinyar nan ta fito kanwar Sapna ce dan suna kama amma Sapna ta dan fita kyau.
     Murmushi tayi tare da juyawa taci gaba da abunda take tana fadin kaya sun karu.

  Suna gama abunda ya kawosu bayan Sapna ta zuba musu abincin sunci sun koshi sannan suka fito daga part din.
   Suna kokarin shiga part dinsu sukaga Safiya taci uwar kwalliya zata fita.
    Ko kallanta Shaheeda batayiba.
   Har sun kusa hucewa Sapna tace Shaheeda baki gaida ya Safiya bah.
    Dan Allah yaya kitaho mu tafi itama ai bata mana maganaba.
    Ita kuwa Safiya tana jinsu tayi fice warta.
     Shigewar gida itama tayi Sapna ta bita a baya tana mamakin hali irin na Shaheeda tun tana karamarta ga shegiyar zuciya.
     Cikin daki ta sameta zaune.
   Shaheeda meyasa kika raina mutane ne.inaga tunda kikazo gidan nan ko Umma bakije kin gaidaba.
    Nifa yaya duk wanda baya sanki nima bana sanshi kuma duk in gidan nan basa sanki.
     Waya gaya miki kowa yana sona kawai de kinasan ace baki da kunya yanzu ki tashi muje ki gaida Umma.
    Nifa gaskiya ya bana santa kuma bazan gaida taba ta karashe maganar da kuka.
     Rungume ta tayi tare da fadin ya isa haka pls Amma ki dena rashin kunya kinji.
    Kai ta daga mata tare da fadin kema yaya ki daina kula su kinji toh ta fada.
      Yanzu muyi sallah saina rakaki ki gaida Aunty Naja ko?

😘😘😘😘😘😘😘😘😘😘
01 Amal fansclub 💅🏻🌷

Written by Zeenaseer😘

MARAICHIWhere stories live. Discover now