MARAICHI

1K 44 0
                                    

🌳🌳      ⚜         🌳🌳
🌳                              🌳
              👑👑
                🌳

1⃣7⃣

°°°°°°°°{6:42am}°°°°°°°°
   Hafsat ce ta farka dan gabatar da sallah asbah.bayan ta idarne ta tashi Sapna itama tayi.
   Bayan sun idarne kwawacce ta koma ta kwanta sai 10am suka farka Sapna ce ta fara tashi dan tsananin yinwar da takeji.
    Ahankali ta mike ta shiga toilet tayi wanka sannan ta fito ta maida kayan jikinta danma Allah ya taima keta period dinta kwana daya yayi ya dauke.
    Komai bata shafaba tunda babu abunda aka kawo musu.zama tayi ta kunna TV tana kallo.
    Hafsat ma tashi tayi sannan ta kalleta tareda fadin harkin tashi kenan.
    Eh wallah kuma Har wanka nayi.
    Wanka kuma keda kifa fada rijiya aina zata sainan da irin 2wks dinan zakiyi wanka.
   Dariya suka aa gaba daya.
   Sannan ta mike tsaye tana fadin kinga yaya Har yanzu baizoba koma kuma nasan kinajin yinwa ko?
    Eh ta gyada kanta.
  Bara nima na dan watsa ruwa amma kamata yayi ace yazo.
   Bata jima da shiga toilet dinba.aka turo kufar.likita ce mace da nurse suka shigo dakin.
   Zamatayi kan kujera tareda kallan Sapna tana murmushi. Sannu yan mata tace ya jikin.
   Da sauki Sapna ta bata amsa.
   Masha Allah amma yanzu babu inda yake miki ciwo.
   Eh babu kaina ne kawai yake dan min ciwo lokaci zuwa lokaci.
   Toh insha Allah shima zai dena inkinasan maganinki yanzu mun sallameku zaku iya tafiya inna yar uwar taki.
   Ammm tana toilet amma yanzu za...
    Bata gama rufe bakintaba ta fito daga toilet din tana yafa veil din kanta.
   Gaishesu tayi sannan ta zauna.
  Ya saukin jikin likita tayi mata sannan ta gaya mata cewar an sallamesu kuma ta bata sauran magungunan Sapna.
   Godiya tayi musu tareda fadin dan Allah ko zaki bani aran fone dinki kinga Har yanzu ba wanda yazo daga gida ko lafiya.
    Ohk ba damuwa hannun ta tazira cikin aljihun rigarta ta dauko tare da mika mata.
   Sannan ta mike tace inkun gama saiki kawomin cikin office dake kallan dakin ku.
   Toh nagode ta masa sukuma suka fita.
    Numb.dan Asabe ta kira amma yaki dauka karshema akashe gajita tayi mutukar mamakin hakan.
    Haka Umma ma da taki kira shiru ba'a dagaba dan haka saita kira Jameel saurayin dazai aureta.
    Bayan sun gaisa take sanar masa cewa itace suna asibiti yazo ya maidasu gida dan Allah dan haryanzu gida shiru kuna ta kira ba'a daukaba.
    Ohk ganinan zuwa inka karaso saika kirani.
   Sannan ta katse wayar.
   
    Basu jima da gama wayarba ta kuma jin ya kira ta.
    Sallama tayi tare da karawa a kunuwanta.
    Yauwa kufito gani nan na iso koba asibitin da kuke zuwaba.
   Eh Shifa gamunan.
Sannan ta mike suka fito daga dakin.
  Knocking office din Dr.sukayi tare da shiga ta kuma yimata godiya ta bata wayar,sannan suka fito.
    Da yake tasan motarsa can nesa ta hangoshi sannan suka tako Har zuwa wajan.
    Da sallama suka shiga cikin motar hafsa gaba ta shiga ita kuma Sapna tana baya.
    Gashe shi tayi cikin fara'a ya amsa yana kallan ta ta mirror.
    Sannan yace waye bashi da Lafiya ne? Ya fada tare da yima motar key.
    Wallahi Sapna nace batajin ddi shina mukazo jiya aka kara mata drip yanzu kuma suka sallamomu.
     Ohk Allah ubangiji ya kara sauki ya fada idansa kan titi.
    Suna tafiya suna hira itade Sapna tana daga baya abun duniya duk ya isheta dan ita Har batasan Shiga cikin gidan.
    Basu jimaba ya suka karaso gidan.
A kofar gidan yayi parking da motarsa sannan sukayi sallama dashi suka shiga ciki.
     Da sallama suka shiga gidan,dakinsu Sapna ta nufa ita kuwa hafsa kitchen ta nufa dan samun abunda zasuyi breakfast dashi.
   Tea ta hada musu sannan ta dauko bread ta kawo musu sukaci suka koshi.
     Sannan Sapna ta shiga daki ta cire uniform din nata ta sanya kayanta marassa nauyi ta haye gado ta kwanta dan tan bukatar hutawa.
     Ita kuwa hafsa gaba daya ji take zuciyar ta kamar wanda aka matama rai duk haushi takeji kuma ba haushin kowa takeji ba inba na Sapna ba bama tasan ta ganta kusa da ita.
    Tsaki tayi tare da mikewa ta bar dakin.
    Dakin Umman ta tanufa.baga kowa cikin falonba dan tasan safiya na makaranta. Cikin dakin ta shiga.
    Umma na zaune gefan gado.
    Gaisheta tayi tareda fadin Safiya na makaranta ne.
    Eh tafada sannan tace yame jikin?
   Kai Umma nikuma ina ruwana da wata me jiki ita ta sani sannan ta mike tabar dakin danji take kamar ta kashe ummar datayi mata maganar sapnar.
    Dariyar mugunta ummar tayi tare da fadin yanzuma aka soma wasan harni za'a ma iya shege.
   Hahahhahahahha ta kuma kyalkyalewa da dariya kamar mahaukaciya.

ALLAH SARKI SAPNA 😢😢😢

😘😘😘😘😘😘😘😘😘😘
  01 Amal fansclub 💅🏻🌷

Written by Zeenaseer😘

MARAICHINơi câu chuyện tồn tại. Hãy khám phá bây giờ