MARAICHI

1K 44 0
                                    

🌳🌳        ⚜      🌳🌳
🌳                              🌳
              👑👑
                 🌳
       MARAICHI❣
              NA
  Zainab Naseer Sarki
      ( Zeenaseer😘)

1⃣6⃣

     .....I dedicated dis page you people 😘😘😘
Dimples Hamagee,sadnas,momsultn,mmnwalid,Preety Queen, ummieJ,mmnsudies,leecy,feeyah,Billy garladanchi,FIDDY G,Aisha bulkachuwa,miemiebee,Aunty jidderh,jiddah❣
Happiness is lyk butterfly,u run after it,it keeps flying away.if u stand still it comes &sits on ur shoulders.I wishes u happier moments ever❣
   Allah ubangiji ya kuma dau kakaku ya saka muku da JANNATUL FIRDOUS💋
    And always remember Zeenaseer lovs u nd support u❤

⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
     Daganan kai tsaye gidan malamin suka nufa nan ya tabbatar musu da mukatarsu ta gama biya.
    Haka Umma ta dawo gida cikin farin ciki dajin ddi.

Bayan 3hrs.
  Har lokacin dan Asabe yana cikin asibitin dan gani yake inya tafi za'a aiko mai da sakon mutuwar Sapna dan yama Riga yadau alkawarin babu wanda zai sanar da wannan al'amari.
    Hafsa ce ta fara bude idanunta tana kalan dakin cike da mamakin ganin ta cikin sa.
   Ahankali ta mike zaune tareda dafe kanta idanunta a rufe.
Ido biyu sukayi da dan Asabe dake zaune kan kujera.
    Kara matsowa kusa da ita yayi tare da fadin sannu hafsa.
  Kai kawai ta iya dagawa.ahankali ta bude idanta daya kada yayi jajir murya na rawa kamar wacce zatayi kuka tace yaya Sapna ta mutu ko?
   Ta karashe maganar hawaye na zubowa daga idanunta.
    Ki kwantar da hankalin ki hafsa ki kwanta ki kuma hutawa.
    Tana kuka tana fadin amma yaya ya hankalina zai kwanta banasan wani Abu ya faru da ita dan Al.....
Kukanne yaci karfinta shiyasa ta kasa maganar.kuka taci gaba dayi.
    Shi kansa ji yake kamar ya fashe da kukan ya hutama zuciyar da yanda yakeji a yanzun.
    Da ker ya iya dafa kafadunta tare da fadin kiyi shiru Hafsa kibar kuka Allah shine maganin duk wata matsala. In......
    Wani iri yakeji cikin ranshi kasa karasa maganar yayi fita yayi daga dakin tare da janyo kofar.
    Jikin bango ya samu tareda dafa hannayansa gaba daya bayajin zai iya barin Sapna gurin danjin mahaifiyar ta yake tunanin maidata yana ganin nan ne kadai zata samu kulawa.
     Guri yasamu ya zauna dan gaba daya zuciyar sa ta dagule yanjin wani irin canji tattare dashi.

    Yana fita ta dago da kanta da jajayan idanunta duk hawaye ajikinsu.
     Waigowa tayi ahankali tana kalan Sapna dahar lokacin take kwance saman gado idanunta arufe tana bacci.
    Tausayinta hafsa keji sosai kamar tabdauke ta gudu da ita tabar gidanma gaba daya.

Bayan wasu yan lokuta.
    Ahankali itama ta fude idanunta tana daga kwancan dan bata motsa ko inaba ajikinta.
    Dakin raketa kallo ahaka.
  Hafsat ce ta fito daga cikin toilet ganin idanun Sapna abude yasa ta karasa wajanta.
   Zama tayi kusa da ita tana mata murmushi.
  Itama murmushi take yimata hawaye na zubowa ta gefe da gefan idanunta.
     Itama hawayen ne ya fara zuboma hafsa.
   Ahankali Sapna ta dago da hannunta ta fara share mata hawayan tana girgiza mata kai alamun tadena kuka.
    Hannun nata ta reke tare da hadewa da nata.
    Juyar da kanta tayi dayan gefan gadan tana kuka itama maras sauti.dan ita ji take tama gaji da rayuwar gidan gaba daya dama Allah zaisa ta mutu da ta koma wannan gidan.
    Dan Asabe ya shigo dakin da sallamarsa dauke da leda.murmushi ya sakrma Sapna tare da fadin sannu kinji.
   Kai kawai ta iya gyada masa dan batasan yin magana.
   Yaowa hafsa ga abincinan sai kuci kinga yanzu dare yayi saikuma da safe zanzo in Allah ya kaimu.
    Toh yaya saida safe.
Harya kai bakin kofa zai fita kafin.
    Ahankali ta firta yayah ka gaida gida Amma dan Allah kar agayama Shaheeda abunda ya faru.
    Batareda yace komaifa kawai ya fice tareda ja musu kofar.
    Sapna tashi kici abincin kinji ga magani nan da aka bada kisha.
   Hafsat ce ta taimaka mata ta mike zaune tare da sanya mata pillow abayanta.
    Ahankali ta dauko abincin ta shiga bata tana ci itama.
Tanayi tana bata ruwa harta fara koshi.
    Ya hafsa na koshi kema kici.
    Toh amma kema kidan kara mana ko yayane.
   Idan na kara amai zanyi.
    Toh bara nagama na taimaka miki kije toilet din ko?
    Gyada kanta tayi tana murmushi tareda jinginar da kanta jikin gadan tana kallan hafsa dake cin abincin.

   Tana gamawa ta kaita toilet tayo fitsari da alwala.
  Sallah tayi sannan ta kwanta lullube ta hafsa tayi da blanket tareda manna mata peck a goshi sannan tace gudnyt cwthrt.
    Murmushi tayi batare da tayi maganaba ta kuma kudindunewa dan sanyin da takeji.
   Komawa gadanta tayi itama ta kwanta.

😘😘😘😘😘😘😘😘😘😘
   01 Amal fansclub 💅🏻 🌷

Written by Zeenaseer😘

MARAICHIWhere stories live. Discover now