MARAICHI

1.5K 80 1
                                    

🌳🌳        ⚜       🌳🌳
🌳                              🌳
               👑👑
                  🌳
        MARAICHI❣
                NA
  Zainab Naseer Sarki
      (Zeenaseer😘)

0⃣4⃣

ASALI☃


Alhaji Ibrahim Sunusi haifanfan garin kebbi state ne, mutun ne mai mutunci da Sanin ya kamata.yana da ilimin boko dana mahammadiya daidai gwargwado.
    Bayan ya gama karatunsa saiya fara kasuwancin sa nan garin kebbi.Allah ya samai hannu cikin sana'ar tasa ta saida kayan masarufi.nan ya bude katan shagwansa na saida kayan abinci.kuma alhmdullh yana ciniki sosai.
      Nan Allah ya hadashi da mace mai mutunci hankali da nutsuwa wato Rabi'at.bayan sunyi aure da shekara daya da rabi Allah ya basu haihuwar yar mace nan suka samata suna Maria sunan mahaifiyar sa,suke kiranta da Ummi.
     Saida mariya ta shekara 5 sannan Rabi ta kuma haihuwa da namiji nan suka sami suna Aliyu da yake ranar assabr aka haifesa sai suke kiransa da dan Asabe.
      Bayan dan Asabe yayi shekara 3.Alh.Ibrahim ya karo aure hauwa'u.
Rabi bata nuna damuwar ta ba kan auran da mijin nata ya kara.ita kuwa Hauwa ganin Rabi ta fita kyau ga hankali yasanya ta tsaneta kuma koda yaushe cikin janta fada take ko takama yaranta tana duka.
    Hakan yana mugun batama Rabi rai Amma saitayi shiru bata magana.saima ta hana yaranta fitowa kullum suna daki dan batasan tashin hankali.
    Gashi in ranar girkin tane bata gama abinci da huri yara suyita faman jin yinwa saide ta sama musu abinda zasuci.
    Koda ta sanarwa mai gidan nasu saiyace sai anayi ana hakuri ba sabawa tayi ba.
    Taji haushi sosai Amma saita daure.
    Shekara Hauwa daya da zuwa itama ta haifi yrta mace mai suka saka mata Halimatussadiya.
    Yarinya ta tashi cikin gata dajin dadi.
   Nan mai gidan nasu ya fara nuna banbanci dan yafi kaunar Sadiya kan sauran yaran nasa.
    Hakan bayama Rabi dadi amma saitaci gaba da hakuri watrana sai labari.
     Shekarar halima 2 ta kuma haihuwa amma itama wannan karan namiji ta Haifa.
    Tayi murna sosai dan gani take kamar sun zama kai daya da Rabi.
     Ana gobe suna Allah yayima yaro mutuwa.
     Nanfa hankalin Hauwa ya tashi kamar zatayi hauka Allah ya kasheta Rabi ce takashe mata danta.
    Itade rabi vanda kuka ba abunda suke ita da yaranta,haka suka hadu da danjinta suka rinka cewa ai mayyace ita tanaji kamar ta mutu dan bakin ciki Amma haka ta hakura ta shige dakinta.
    Tun daga wannan rana gaba mai tsanani da tsana ya kuma shiga tsakanin Rabi da Hauwa.
    Amma ita Rabi bataji ddin hakanba dande bayanda ta iya.
     
Yana shekara daya da mutuwar dan gidan Hauwa ta kuma haihuwar da namiji.murna ba'a magana.
Sai fana habaici take kamar ita taba kanta haihuwar kuma ta hana ta daukar dan karta kashe mata shi.
     Nan aka sama yaro Aminu suke ce masa Abba.
    Sun nunamai gata hakan yasa yaran yataso bashi da kunya ko kadan dan Har iyayan nasa baya ganin girmansu.
      Hakanne ya fara damun Alh. Ibrahim dan bayasan yara maras sajin magana tun yana dukansa haryama gaji ya rabu dashi.
     Bayan shekara 6 da haihuwar Abba.Rabi takuma haihuwar yarta mace.taji dadi sosai kuma tayi farin ciki,ranar suna yarinya taci Khadija amma Nana suka ce mata.
    Yarinya fara tas kyakyawa dan tafi kowa kyau agidan nan Ummi tasamu kanwa kullum tana goye da ita tana mata wasa.
      Haka rayuwa taci gaba gidan Alh. Ibrahim suna samun kulawa me kyau wajan baban nasu.dan babu abunda baya musu dan suji ddi.
    Yasanyasu amakaranta suna karatu tukuru.
    Shekarar Nana 2 ,Hauwa ta kuma haihuwar yrta mace itama aka sanya mata Hafsat.
    Tunda ga kanta babu wanda yakuma haihuwa acikin gidan Har lokacin da aka yima Maria Aure.
     Ta auri wani mai rufin asiri kuma saurayi Amma shi dan katsinane.
Nan suka kaita katsina.
Mutukar haushi Hauwa tana jinshi nan tasa Sadiya akan itama taso mu mai arziki ayi mata auran.
     Bayn andan kwana biyu da bikin Maria itama Sadiya takawo wani Alhaji mai kudi tace shitake so a aura mata.
     Hauwa taji ddi sosai nan tasa akayi mata auran itama Ashe yana da mata biyu itace ta uku.nan juwa aka kaita dande kowa part dinshi daban.
     Gidan ya rage daga dn Asabe sai Abba, Nana da Hafsat.
  
Nana da Hafsat sun taso kamar yn biyu kasan cewar Nana bata da girman jiki sai kuka zama kusan kai daya da Hafsat.
    Duk da in suna gida Hauwa bata barinsu zama guri daya.Amma amakaranta suna tare sunyi mutukar shakuwa da juna.
     Komai tare sukeyinsa.ko dayace taga daya ta sanya kaya to itama irinsu zata saka.
Hakan yana yima Rabi ddi kuma dukansu ta dauke su amatsayi yayanta.
     Dan Asabe ma ya dage yanata karatu kuma alhmdullh yana da kokari sosai kuma yana dan zuwa kasuwar baban nasu.
     Shikuwa Abba irin yn isakn samarinnan ne.kullum yana gabtali baya zama agida.ga shegen San mata ga shaye shaye.
    Kuma ga shegiyar sata dn ko Babar shice ta anje Abu yana gani zai dauke Amma ita ko ajikinta dan ita ke kara daure masa gindi yayi abunda yaga dama.

     Alh.Ibrahim ya gina musu saban gida mekyau kowacce daki ciki da rumfa Har nashi.
   Nan fa ya cancado sabuwar Amarya maryam kyakyawa jajir da ita yr garin bauchi ce sunzo sunan yayarta data haihuwa nan ya ganta kuma itama ta amince akasha biki.
     Hauwa taji haushi sosai kishi kamar ya kasheta dan mugun haushin maryam din takeji.
     Kyakyawa da ita ga hankali, ilimi da nutsuwa.
Hakan yasa suka hade kansu da Rabi hankali kwance dan yayama take kiranta.
     Bata jima da zuwaba ta samu ciki dama itama Hauwa tasamu cikin amma saita Riga maryam din haihuwa.
     Wata rana Hauwa ta sanya Abba yayima maryam duka gashi lokacin cikinta ya fara tsufa.
    Tasha wahala sosai kamar zata mutu nan Alh. Ibrahim ya kori Abban daga gidan yakuma fada ya cireshi daga cikin yayansa.
     Nan Hauwa ta dunga hauka wai antsaneta tunda aka kori danta.
Haka tayi ta gama.
     Bayan kwana biyu ta haifi yarta safiya.itakuma itace mun muna acikin gidan.Amma haka Hauwa ta dauki San duniya ta Dora kan Safiya shiyasa itama ta tashi da hali irinna uwata.
     Bayan wata hudu da haihuwar Safiya itama maryam ta haihuwa aka sama yarinya Sapna. Ansha shagali sosai dayake danginta suna da kudi.
     Yarinya ta tashi cikin soda kauna gurin yanyanta kullum in bata bayan Hafsat tana gurin Nana dayake sun saba sosai dasu.
     Abunda ke hadata da uwanta bcci dashan nono.
   Haka itama taji ddi sosai.
  
Shekara ta biyar ta kuma haihuwa mace aka sanya mata Fatima suke kiranta Shaheeda da yake sunan mamantane.
    Haka rayuwar gidan taci gaba da gudana.
    Maria itama yaranta biyu ita kuwa Sadiya bata taba haihuwa ba.
  
BAYAN SHEKARA 2
RANAR TALATA.
    Allah yayima Alh. Ibrahim rasuwa babu ciwo ko dan kawai wayar gari akayi babu shi.
    Kowa yaji mutuwar nan sosai abun tausayi lokacin maryam Nada karamin ciki.
    Gida kullum cike yake da yan uwa da abokan arziki anata amsar ta'aziya.
     Haka yara kowa yayi kukan rashin babansa.Har Shaheeda da take karama ganin ana kuka itama takeyi.
    Haka akaita zaman makoki Har tsawan kwana 7.sannan kowa ya kama gabansa.
     Nan fa Hauwa ta fara tunanin yanda zata raba maryam da Rabi subar gidan.
   Haka kuwa akayi nan tashiga ta fita tayi musu asiri itade maryam bai fara aiki akantaba.
     Amma Rabi hauka tafara tuburan.nan hankalin yaranta danasu maryam ya tashi suka shiga nemamata magani abun abun tausayi dan duk wanda ya ganta saiya tausaya mata.
    Nan suka dauketa suka kaita gidan mahaukata.satinta uku a can aka aiko musu cewar ta kashe kanta.
     Hankalin kowa yayi mugun tashi nan itama aka maidota gida akayi jana'iza.sunyi kukan rashinta sosai.
      Bayan sadakar bakwai maria tace zata tafi da Nana ta zauna agurin ta Har zuwa auranta.
     Amma rasuna kawo musu ziyara.maryam da Hafsat sunyi kukan rashin Nana sosai dan tan kaunarsu itama haka suka tafi suna kukan rabuwa da juna.
     Haka rayuwa taci gaba in ansamu Hutu Nana kanzo ta jima dakin maryam take sauka.
     Kuma dan Asabe ke kula da gidan duk abunda sukeso shiyake musu amma Hauwa da suke kira Umma bata gani.
    Haka kuma danta Abba ya dawo gida Amma shi baya yawan zama agida kullum yana gantalin sa.

Su Hafsat suna level 200 ita da Nana kuma suna yawan waya.Amma Umma bata taba barinta taje katsinan ba.
     Sapna da Safiya kuwa suna primary 5 yanzu ne zasu shiga jss1.
    Shaheeda ce kawai bata shiga makaranta ba.
   
Ynxu dan Asabe zai gyara gidan saboda aure zaiyi ya mai dashi part biyu danashi Dana sauran matan.
     WANNAN KENAN😉

😘😘😘😘😘😘😘
01 Amal fansclub💅🏻🌷

Written by Zeenaseer😘

MARAICHIWhere stories live. Discover now