🌳🌳 ⚜ 🌳🌳
🌳 🌳
👑👑
🌳
MARAICHI❣
NA
Zainab Naseer Sarki
(Zeenaseer😘)1⃣8⃣
Pls kuyi hakuri kwana biyu ina busy ne amma insha Allah zanna kwari ko pg 1 narinka post.
Lov u so muah....💋⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
Falo hafsa ta koma ta kwanta saboda zuciyarta dake faman tafasa kamar wadda aka yima wani Abu.
Rasa meke mata dadi takeyi dan kwata kwata batajin ddin hakan.Bacci sosai tayi dan tana bukatar hakan kusan awa biyu ta dauka tana bacci sannan ta farka.
Ahankali ta mike ta nufi toilet dan yin azhr.
Bayan ta idar da sallah ne ta fara jin yinwa.
Mikewa tayi ta nufi dakin Umma dan taga kamar hafsa bata nan.
Da sallamar ta ta shiga dakin amma babu wanda ya amsa mata.
Ganin hafsa zaune ta hade rai.ya sanya Sapna kin karasawa wajanta daga bakin kujera tace ya hafsa yinwa nakeji.
Wata harara ta galla mata tare da fadin bari na zama abinci saiki cinyene.waye jakinki acikin gidan nan dazai zauna yana dafa miki abincin.
Ahankali ta mike cike da mamaki.Umma ta kallah daketa faman murmushi.
Haka ta fito daga dakin kamar kazar da kwai ya fashema aciki.
Dakinsu ta zauna saman kujera tare dayin tagumi dan gaba daya abun ya fata mamaki.
Kallan jikinta tashiga yi tare da fadin aikuwa me garine da bbu me sona.yanzu itama Hafsat ta dena sona.
Ina akesan na sanya kaina wannan wata irin rayuwa ce.
Fashewa tayi kuka me kara.dan gaba daya tagaji da zaman duniyar dama ta mutu ta huta.da wannan bakar rayuwa da take fuskan..
Yanzu kowa baya kaunarta inaga nan gaba idan ta kuma girma.
Kukan da takeyi ne taga bazai yimata maganin yinwaba ya sanya ta mike daga zaunan da take ta fito ta nufi kitchen.
Babu alamun abinci.gashi gabadaya bata Jin dadin jikinta.
Dabarace ta fado mata.
Fitowa tayi daga kitchen dinta ta sanya hijab dinta da takalmi ta nufi gidan Aunty Naja.Da sallamar ta tashiga cikin gidan.jin shirun kamar ba kowa ya sanyata nufi dakin.cikin falon ta shiga shima ba kowa.
Zama tayi kan kujera tana kalle kalle dan tasan tana daki.
Bata jimaba sai gata ta fito.
Murmushi sukayima juna.sannan Sapna ta gyadata.
Lafiya qlau Sapna kwana biyu ko lekoni bakyayi nasan da Shaheeda na kusa ko dayaushe tana tare dani.
Hmmmm! Wallahi Aunty ba haka bane banajin ddi ne kwana biyu amma yanzu jikin da sauki.
Allah sarki kuma baki sanar dani ba.Allah ya sauwake.
Ameen Ameen kawai ta fada tayi shiru dan tanasan tam bayarta abinci kuma tana tsuran kar tayi tunanin ko bata ci agida.
Babu de matsalar komai Sapna.
Ta fada tareda dafa kafadarta tana kallan fuskarta.
Hmm! Wallahi Aunty bbu komai kawai de inasan ki zubamin abincine a gida macaroni suka dafa nikuma bana sanshi.
Toh ta fada tare da mikewa dan tanajin tausayin sapnar.
Bata dau lokaciba ta hado mata abinci mai rai da lafiya da ruwa da juice.
Ta zauna tare da bismillah ta fara ci suna taba hira sama sama harta cinye duka.
Tasha juice din sannan tace Aunty dan Allah kiyi min kitso kaina ya jima ba kitso.
Toh Sapna gama cin abincin.
Kai Aunty na koshi wallahi ai naci dayawa.
Aa kiri kokari ki cinye sai in miki kitsan.
Da ker ta iya cinyewa sannan ta kwashe kwanikan ta gyara wajan.
Saida sukayi sallah suna hira sannan sukayi sallar la'asr din.
Sannan ta fara yimata kitsan.Sunayi suna hira har suka gama tayi mata kitso me kyau.
Sannan gyara gurin Aunty Naja nata yaba kyan kitsan.
Saida ta tsareta taci abincin dare bayan magrib sannan ta fito ta nufi gida.Tana ta faman sauri kar ayi mata fada.tana shiga sukaci karo da Abba a soran gidan.
Da sauri ta matsa baya tana dafe kanta.
Daga gidan ubanwa kike.
Da baya ta fara jah dan tasan bashi da imani zai iya dukanta.
Da sauri ya wartota tareda shigo da ita cikin gidan Har dakin Umma ya zaginta.
😘😘😘😘😘😘😘😘😘😘
01 Amal fansclub 💅🏻 🌷Written by Zeenaseer😘
YOU ARE READING
MARAICHI
Non-FictionLabarine na yara gudu biyu,wanda zusu taso cikin rashin kulawa da gata na iyayansu,sakamakon matar mahaifinsu. Labarine me fada karwa,nisha dan tarwa yana dauke da tausayi, soyayya da kuma karamci...