🌳🌳 ⚜ 🌳🌳
🌳 🌳
👑👑
🌳
MARAICHI❣
NA
Zainab Naseer Sarki
( Zeenaseer😘)0⃣8⃣
Cikin dakin suka tura tare da shiga gaba daya hankalin su atashe yake.
Kwance take saman gado tana faman tirje tirje manyane akanta sun rike ta da alama so take ta fice.
Gaba dayansu salati suke ita Hafsat ma kasa tsayawa tayi sai fita tayi.
Haka shima yaya din.
Hajiya da Bilkisu ma kukan suke famanyi.
Tirje tirje take famanyi duk ta hargitsa gadan haka harshan tama ta taune shi.
Wasu likitocine suka shigo da sauri.
Daya daga cikin sune yace dan Allah hajiya kudan fita waje mana.
Da ker Bilkisu ta janye Hajiya zuwa waje sunata jin ihunta amma hakanan suka hakura duk kuka suke.
Bayan mintina kadan sukaji shiru.
Yayan ne ya kawo musu ruwa suka sha.
Cikin muryar kuka hajiya ta kalli naja tareda fadin Ashe haka taketa famanyi shikenan maryamana ta haukace shikenan ta karashe magana da kuka.
Yayane yaya karfin halin lallashinta insha Allah zata samu sauki hajiya addu'a take bukata.
Yanzude likitan yace sunyi mata allura kuma zata jima bata farkaba.
Kuma da ita nakesan mu tafi danba irin wannan asibitin ne ya dace da itaba.sunce sai de akaita na mahaukata zasu iya ganu matsalar.
Shikenan Allah ya bata lafiya yanzu sai musan abinyi dan bazamu zauna hakanan ba dole yau zamu koma.
Babu damuwa hajiya yanzu munyi waya da Baba yace shima gobe zai dawo insha Allah.
Itade Hafsat na zaune hannunta dauke da Shaheeda tana faman banci.
Sai lokacin hajiya ta kula dasu.
Sannan Hafsat ta gaidata.
Amsawa tayi da murmushi a fuskarta sannan tace Fatima ce hannu ki.
Eh itace bacci takeyi.
Allah sarki ya en gidan ina Sapna.
Duk suna lafiya Sapna suna makaranta.
Sallamar dan Asabe dasu Sapna ne ya katse su.
Da sauri ta karasa tareda fadawa jikin hajiya sannan tace hajiya ina Maman mu yaya yace bbynmu ya mutu jiya.
Tana nan bacci takeyi eh sai kiyi masa addu'a.
Itama Maman naku da ita zamu tafi dan akuma yimata magani.
Amma hajiya damu za'a tafi ko shiru tayi batace komai ba dan batasan barin yn jikokin nata nan garin.
Gaisawa sukayi da dan Asabe sannan suka yimasa jaje.
Ita kuwa safiya tunda ta gaida su hajiya komawa tayi ta zauna kusa da Hafsat.
Toh yanzu de dan Asabe zamu tafi da maryam sai kuma yanda hali yayi ya kake gani game dabyaran.
Toh hajiya babu damuwa amma yaran abansu mana anan tunda karatu suke kuma ga yn uwansu kuma ga Anty Naja.kuma za'a na kawo muku su insha Allah.
Shikenan ba damuwa Allah yayi maka albarka yabar zumunci.
Ameen thumma ameen yace sannan suka mike aka shiga dan fito da maryam din saboda hucewa zasuyi.
Toh Sapna taho mu huce gida ko Hafsat Ku taso muje hajiya Allah ya kiyaye ya kara lafiya kuma muma insha Allah zamuzo.ya fada hannunsa rike dana Sapna tana janta su tafi.
Lokacinne aka fito da ita ana turata za'a kaita mota.
Ahankali ta zame hannunta daga na dan Asabe ta rugo zuwa gadan da za'a fita da Maman tasu.kowa na wajan ita yake kallo kowa na tausayinta.
Tana isa wajan gadan tana hawaye ta kamo hannun Maman nata tasanya anata tareda kwanciya kan kirjinta tana kuka.
Kuwa ta bashi tasauyi dan wasu Har kwalla.
Ahankali tace mama kullum zan dinga yimiki addu'a innayi sallah zaki samu lafiya kuma ki dawo wajanmu muna kwana tare.
Kamar Maman tasu tanajin abunda take fada itama hawaye ya zubo ta jefan idanunta duk da arufe suke.
Hannu ta sanya ta goge mata hawayan nata.
Turata sukaci gaba dayi tana bin keken tana kuka.
Naja fita tayi daga asibitin saboda bazata iya gani ba.haka suma su Hafsat kuka suke Har safiyar.
Da sauri dan Asabe ya dauketa tare da fita da ita daga cikin asibitin.
Tanata mika hannu tana kuka.
Wayyo Allah Maman mu karku tafi da ita Ku kawo mana ita zamuyi mata addu'a ta samu lafiya yaya karka rabani da mamana dan Allah Ku kawo mana ita kar Shaheeda tayi kuka.
Shima duk dauriyarsa saida hawayen suka zubo masa amma sauri yayi ya goge.
Hanya suka raba su sukayi hanyar da za'a sakata cikin suma sukayi tasu hanyar. Cikin mota ta sanyata tareda rufeta.
Sai lekowa take ta Glass tana bubbugawa tana kuka sai faman hawaye take agaban idanta motar ta tashi suka tafi.
Shima dan Asabe motar yaja sukabar harabar asibitin.
Kasama kukan tayi saide ta jingina kanta da jikin kujera tana kallan gabanta hawaye na zuba.
Haka suma Hafsat da Safiya sai faman goge hawayen suke.
Shima shiru yayi yaci gaba da driving din bai kuma juyowa ya kalle suba.
Bude idan nunta tayi tareda kallan su hafsa.sannan ta dubi gaba taga dan Asabe.
Sauka tayi daga kan cinyar hafsa ta tsallako gaba ta fada jikin Sapna tareda fadin gurin mama zamu ta kuma shigewa jikinta.
Rungume ta tayi ta kuma fashewa da wani kukan.da sauri ta dago tare da fadin ya Sapna waya dukeki.
Bakowa cikina yake min ciwo kinji.
Hannunta tasa tana goge mata tareda cewa kiyi cilu mama zata baki magani ko?
Girgizamata kai tayi alamun eh ta kuma rungume ta.
Shiru tayi ajikinta Har suka isa gida.
Da sallama suka shiga banda dan Asabe daya koma.
Jikin kowa yayi sanya ahaka suka shiga gidan hannun Shaheeda cikin na Sapna.
Safiya dakin mamansu ta nufa itakuma rabe rabe ta tsaya yi,Shaheeda ce ke janyo hannunta tana fadin ya muje daki mu ga mama.
Dakinsu suka nufa.
Mama! Mama!! Ya Sapna bata da lafiya kibata magani tana kuka.
Kinga Shaheeda ki dena kiran mama batanan dodone ya cinye ta bazaki kara ganintaba in kuma kikayi kuka zai cin yini dake kuma.
Da sauri ta fada jikin Sapna tareda fadin bazan yiba yayi Sapna cikin muryar kuka harda hawaye amma ahankali takeyi dankar dodon yaji kukanta.
Muma saimun zaneshi tunda ya cinye mana Maman muko.
Eh ta gyada mata kai ta rungume ta.👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑
Wayr tace take faman ringing da sauri ta dauka tareda karawa akunnuwanta.
Hello Mom!
Salma ya kk DA fatan kin sanar da mi jinki maganar tafiyar nan.
Shiru tayi kafin tace mom na gaya masa Amma yace saide nayi 2dys inba hakaba bazani ba.
Lallai salma baki da hankali yanzu Har zaki tsaya namiji yana gindaya miki sharadi toh Wallahi kima janza shawarar.
Dan ana canza miji amma ba'a janza in uwa.kisan yanda zakuyi Ku dai daita jibi in Allah ya kaimu zamu huce kuma dukanmu zamu tafi atare.
Toh mom insha Allah zansan yanda za'a yauwa kinga su Hasina suda suke nesa harsun karaso saike yr ddi miji nade gaya miki sai anjima ta katse wayarta.
Yanzu ya kenan zatayi gaskiya tana kaunar Fahad Amma kuma ya zatayi.
Ko dayake ai shima yana kaunata dolema yaso abunda nakeso zan yarda kwana biyun zanyi Amma na tafi sati zanyi.
Murmushi tayi sannan ta koma kitchen din dan cigaba da girkinta.Bayan kiran sallah magrib Fahad ya shigo gidan yaga an gyara ko ina sai faman kanshi yake.
Murmushi shima yayi yashige dakinsa dan yin shower.
Bayan ya gamane ya sanya kayansa ya fito falo ya dawo ya zauna.
Itama fitowa tayi tayi kyau sosai cikin wasu English wears.
Karasowa wajansa tayi tareda fadawa jikinsa.
Promote din hannun sa ya anje tareda fadin kinyi kyau sosai ya shafa fuskar ta.
Kaima ai kayi kyau shine ka dawo ko ka nemeni ta fada cikin muryar shagwaba.
Kiyi hakuri bby na dawo agajiye ne shiyasa nadan watsa ruwa.but I miss u ya fada tareda yimata peck a hncinta.
Miss u too! Kataso muje nayi maka dinner me ddi.
Dagaske kice yau zan cika tumbina.
Mikewa sukayi suka nufi dinning en suna dariya.
Nan ta zuba masa hadaddan tuwan shinkafa miyar ganye tasha kifi da nama sai kanshi take.
Nan ta zuba masa yanaci suna hira.👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑
Jikinta ta dauraye da yake yau ma islamiyyah.uniform dinta ta cire ta wanke kayanta ta shanya.
Hafsat ce ta shigo dakin hannun ta dauke da abinci.
Sapna kuzo Ku zauna kuci abinci.
To yaya.nan suka zauna suna cin abincin su tanata yimusu wasa da dariya Har suka cinye.
Sannan ta gyara gurin ta dauke kwanan tace Ku zauna anan ina zuwa.
Dakinsu ta nufa ta dauko kayanta da duk wani Abu da zata bukata ta mai dashi dakinsu Sapna.
Dan dan asabene ya sanyata tayi hakan.
Umma kamar zata mutu dan jin haushin hakan amma saita dake dan ita kadai tasan abunda zata kullah.
Sapna ce ta tayata suka shirya kayan nata da komai suna raha dan hafsa tana sansu sosai.
Wayar tace tayi kara,
Sapna mikomin kinji
Mikewa tayi tareda fadin toh mika mata tayi sannan ta daga.
Hello Nana ya kike ya gidan ya su Anty Ummi.
Wallahi suna nan lafiya qlau ya karatu.
Alhmdullh exam ma zamu fara insha Allah.
Toh Allah yabamu sa'a ya jikin Anty Maryam.
Kede bari da sauki de za'a ce dazuma suka tafi bauchi da ita.
Allah Sarki haka yaya yace Wallahi abun tausayi.
Ni gani nayi kamar irin Ciwan mamanku ko?
Shima yayan haka yace dazu da suna waya da Anty Ummi.
Komade menene Allah yabata lafiya.
Ameen thumma ameen.
Inasu Umma duk suna lafiya de ko dasu Shaheeda.
Wallahi lafiya qlau kingama su Shaheeda nan yanzu nadawo dakinsu dan muna kwana tare.
Gaskiya kin kyauta banisu mu gaisa.
Mikawa Sapna wayar tayi tareda fadin nanace Ku gaisa.
Hello ya Nana inayini.
Lfylau Sapna ya skul.
Lafiya qlau ina su Anty Ummi.
Duk suna gaisheku suma ina yr kirki.
Gatacan tana wasa Shaheeda kizo ga ya Nana.
Da saurita rugu tareda da fadin ya Nana ina yn tsanana da kikace zaki ciyamin
Dariya tayi tareda fadin zan taho miki da ita kinji ko?Amma banda rigima kinji.
Ai ya Sapna bana ligimako!
Yh yanzu bata rigima ta girma.
Toh sai anjima Ku rinka karatu sosai kunji .
Toh tafada tareda mikawa hafsa wayar sannan sukayi sallama da Nana..
Muje zuwa😢😘😘😘😘😘😘😘😘😘😘
01 Amal fansclub 💅🏻🌷Written by Zeenaseer😘
YOU ARE READING
MARAICHI
Non-FictionLabarine na yara gudu biyu,wanda zusu taso cikin rashin kulawa da gata na iyayansu,sakamakon matar mahaifinsu. Labarine me fada karwa,nisha dan tarwa yana dauke da tausayi, soyayya da kuma karamci...