🌳🌳. ⚜. 🌳🌳
🌳. 🌳
👑👑
🌳🌳
🌳
MARAICHI❣
NA
Zainab Naseer Sarki
(Zeenaseer😘)0⃣2⃣
Da kuka ta shiga dakin nasu.
Mahaifiyar ta da suke kira Umma tana zauna tana kallo.tayi maza ta sanya wa kofar ido tana jiran shigowar yar tata da ke kuka.
Hafsat dake zaune tana Assignment tace Dallah malama waike yaushe zaki kirma saikina barema mutane baki kina kuka saikace ba mace ba.
Toh kekuma ina ruwanki in bazaki share mata kukan taba ki rabu da ita.
Wayyo Allah ummana Wallahi bazan yar daba sai de kome za'ae ayi amma Wallahi saina ci uwarta gobe amakaranta.
Menene uban waye ya tabaki.
Ba wannan muna fukar yarinyar bace taje ta hadamun karya gurin yaya dan Asabe ita da babanta Shikuma harda biye musu yayita yimin fada.
Kede Wallahi munafuka ce kullum saikin hada fada agidan nan banza me kama da biri.
Hafsat ta fada tana hararar safiyar.
Ummance cikin jin haushi ta nuna ta tareda fadin kece munafuka shakaran banza wanda batasan ciwan yar uwar taba.
In banda ke sokuwace maimakon ki tashi ki shigarma yar uwar taki saikina zaginta.
Amma Umma kanmi zakina biye mata bayan kisan shegiyar karya gareta.
Na biye matan.Wallahi Hafsat ki kiyayeni kinji na fada miki.
Cigaba da rubutunta tayi batare da ta kuma kula suba dan ita harga Allah haushin safiyar take ji.
Kinga rabu dasu Wallahi karki raga mata inbanda iskanci yarinya kamar aljana,simi simi dakai kamar muna fuka.
Ki kwantar da hankalin ki kishare hawayanki.
Kuma shima Dan Asaban yana munafunci cikin lamarinsa.
Uhmm Hafsat ta fada ahankali tare da fadin wata rana sai tabaki kunya inde kina biye mata.👑👑👑👑👑👑👑
Gidane ha dadde wanda yagaji da tsaruwa,kamar a kasar turai.Gina ya tsaru iya tsaruwa.
Cikin gidan na shiga dan gaba daya yr kwauye na kuma sabo da kale kale lol😜..
Ko ina ya tsaru cikin falon na shiga nan nabune baki saboda haduwar sa.
Wata mata nagani wanda bazata huce shekara 25 fara ce tas kuma tana da jiki ba laifi.zaune take tarkacan takardu a gabanta da alamu making take.
Salma! Salma!!
Tsaki taja tare da fadin ina zuwa.
Wai baza'a taba Barin mutun yayi abunda zaiyiba.
Anje pen din hannunta tayi sannan ta mike.
Cikin dakin shi ta nufa sannan ta tsaya tana kallan sa.
Kinga shiyasa kullum muke samun matsala dake,kwata kwata kin maida aikin ki yafi komai cikin gidan nan gaskiya bana jin ddi.
Haba dear! Kaima kasan gobene akesan hada result din yara tunda Hutu za'ae kuma in banyi recording din ba yanxu yaushe kake San nayi.
Kaide kawai baka San aikin nawane shiyasa.
Aww! Hakama zakice kinan duk hakuri da nake dake dake bakya gani gud kiyi yanda kk so.
Ta gefanta yabi ya fice dan gaba daya salman haushi take bashi.
Binshi tayi da gudu tareda tare kofar.
Ina kuma zaka?
Inda kika aikeni.
Amma ai kasan bakamin adalciba baka tashi fita sai kaga wkend ina gida.
Kibani guri na huce bana San abunda kike yi.
Wallahi Fahad babu inda zaka je.
Ahhho! Kina nufin sabo da ke sai naki zuwa gaida iyayena kenan ko?
Meyasa salma kin rainani bakyau ganin gimana nifa mijinkine kidena abunda kk.
Kabari da yamma kaje ka gaida su.
Tsayuwa ya gyara tareda fadin inna zauna agidan ki ka gayamin abunda zan miki?
Kaga fahad kowani ma aikaci yana bukatar Hutu duk wkend saboda haka katafi dakinka kayi kwanciyar ka.inyaso da yamma saika je ka gaida su din.
Mtewww ture ta yayi tareda ficewa daga gidan.
Motarshi ya shiga tare da mata key gidansu ya nufa.Koda ya isa me gadi ne ya bude masa gate din sannan ya park din motar shi.
Cikin falon ya shiga da sallama. Momi ya na zaune tana duba wani littafi fuskarta dauke da dan karamin glass a fuskarta.
Zama yayi kan kujera tareda gaida ta.
Littafin ta anje gefe daya tareda cere glass din sannan ta amsa gaisuwar tasa.
Ya gidan ya salma.
Wallahi duk lafiya qlau ina Aisha.
Inaga tana sama kirata mana a waya.
Nasan zancan gizo bazai huce na koki ba.
Wallahi kuwa momi kamar kinsan yinwa nakeji.tazo ta hadamun breakfast.
Ga wani can da nayima Abban ka yana sauri kadan yaci ya huce Kaduna.
Yawwa momina Allah ya barmin ke.
Ameen Allah fahad kana bani mamaki namiji kamar ka bazai iya da gidan saba da anyi magana kace aiki yayi mata yawa ko da kasar take rike at list zata warema mijinta tym dinsa.
Ba abunta ta iya sai shegen kishin baza.
Momi Ade mana hakuri za'a gyara insha Allah.
Kaini bani guri Dallah.
Mikewa yana dariya ya nufi dinning. Zama yayi yaci abincin ya koshi sannan ya mike ya dawo falon.
Har yanzu momi tana nan bata tashiba.
Zama yayi suka dan taba hira kafin yamata sallama ya tafi.👑👑👑👑👑👑👑
Kwashe gari tunda safe mama ta tashi tayima su Sapna wanka sannan itama tayi.
Shiryawa Sapna tayi cikin kayan makaranta ta masu kyau.
Sannan tayi breakfast sannan me daukar su iya iso suka tafi makaranta.Koda suka iso dama ajinsu daya sapna da safiya.
Primary 5 yellow.
Dama ita Sapna ko a makaranta frnd dinta daya ce Husnah.
Suna zaune suna karatu kafin su fara exam din.
Gashinta taji anja mata tabaya.
Ouch! Ta fada tareda juyowa.
Safiya tagani tsaye itada kawayanta su uku akanta.
Haba safiya meye hakan zaki jamin gashi ki sakeni mana.
Dallah malama ki saketa mana ke ko kunya bakyaji gidanku daya amma kina mata Abu kamar ba yar uwarki ba.
Kinga dakata Husnah bansa dakeba da yr gidanmu nake.
Mikewa sapna tayi tareda matsawa kusa da Husnah sannan ta kalli safiyar tace ni inajin maganar yayana dan ya hanamu fada sabo da haka kije kiyi tayi.
Sannan ta kama hannun Husnah sukabar wajan.
Dada binta tayi ta janyota wannan karin saida ta fadi ta ji ciwo a kafarta.
Aikuwa Husnah da saurin hannu ta kwada mata mari.
Nan fa dambe ya kaceme aka dinga fada da ker aka rabasu.
Itade Sapna na gefe kafarta sai faman jini take.
Nan Auntynsu ta kirayesu dukansu sannan tayi musu hukunci ita kuma Sapna aka wanke mata ciwon nata.
Haka sukayi exam din Har aka tashesu.
Ko da driver yaxo daukar su dama Sapna ce me shiga gaba dan ita safiya cewa take bazata zauna kusa da itaba.
Haka suka dawo gida babu wance yayima wata magana .Da sallama ta shiga dakinsu.jikin mama ta fada tana kuka.
Lafiya Sapna yau kuma da kuka aka dawo.
Shaheeda ce itama da idanunta suka ciko da kwalla tace ya sapna waye ya dakeki.
Cikin kuka tace kalli mama ciwan da safiya taji mini a makaranta.
Garin yaya kuma ba yynku yace kar kukara fadaba.
Wallahi bani na jataba kuma banyi fada da itaba.tureni tayi na fadi.
Wannan wani irin bala'i ne.
Mikewa tayi da katan cikinta ta kama hannun Sapna shaheeda na biye da ita suka nufi dakin su safiyar.
Itama tana can ta hada karyarta kuma uwar tata ta yarda tana taa faman fada.
Sallamar da akayice ta tsaidata.
Mikewa zaune tayi tareda fadin lafiya maryam zaki shigo min daki.
Hmmmm Hauwa kenan mezaikaini shigowa dakinki inba kurunin da kuka yiba.
Ke safiya meyasa bakida mutunci
Sapna ba kanwar ki bace amma kika takura mata.yanxu ko wani kika ga yana kokarin dukanta bakya tare mataba.
Kinga maryam ya isheki haka,ya zaki shigo Har cikin dakin su kina mata fada kamar ke kika haifeta.
Dole na mata fada kalli kalli abunda tayi mata.ta fada tareda bude mata ciwon da tajima Sapna.
Bada sukayi kuma aka cuceta kinga kuwa aiba maganar kawo kara.
Hafsace ta shigo dakin da sallama tana murmushi tareda daukar Shaheeda.
Aunty dan Allah kuyi hakuri nasan duk akan safiyane.
Wallahi Hafsat ni kaina rashin jituwar yaran nan yana damuna amma Sam ummanku takasa fahimta Allah ya kauta.
Dama dole na kasa fahimta,Sapna bata da kunya.
Ke kuma Hafsat zaki gane kiranki sakaran banza.
Har daki Hafsat ta raka su Sapna sannan ta dawo.
Tana shigowa dakin Umma ta kwada mata mari.
Banza mahaukaciya idan na kara ganinkin taka dakin matar can Wallahi saina bata miki rai.
Amma Umma d.....
Zaki min shiru kosaina kara kwada miki wanda yafi wannan..😘😘😘😘😘😘😘
01 Amal fansclub💅🏻🌷Written by Zeenaseer😘
YOU ARE READING
MARAICHI
Non-FictionLabarine na yara gudu biyu,wanda zusu taso cikin rashin kulawa da gata na iyayansu,sakamakon matar mahaifinsu. Labarine me fada karwa,nisha dan tarwa yana dauke da tausayi, soyayya da kuma karamci...