MARAICHI

1.3K 67 1
                                    

🌳🌳       ⚜        🌳🌳
🌳                              🌳
              👑👑
                 🌳
      MARAICHI❣
               NA
Zainab Naseer Sarki
     (Zeenaseer😘)

0⃣6⃣

Gaskiya dangane da matsalar haihuwa babu amma de kije likita nasan ganinki.
    Jikinta na rawa tabi bayan nurse din har office din likitan sannan ta yimata iso da tashiga ita kuma ta kuma.
     Har lokacin yaran na rungume ajikinta tana hawaye.
Sallama tayi tareda shiga kafor ta tura sannan ta nemi guri ta zauna tana goge fuskar ta.
    Kallan ta yayi tareda zare karamin glass din dake idan sa.
Hajiya saide kuyi hakuri dama Allah yayi yaro bazeshaki iskar duniya ba.
    Kanta kawai take iya gyadawa dan gaba daya tashiga damuwa jitake kamar danta tarasa.
     Yawwa sannan dama inasan sanar dake ko kuma ince inasan tambayarki.
Daman matar da kuka kawo tana da wata matsalane a kwakalwa ko iska dade wani Abu makamancin hakan.
    Kai ta gyadamai alamun Aa, tana kallan sa.
    Toh gaskiya hajiya matar da kuka kawo bata da lafiya ameen tanada matsala a kwakwalwarta dan daker muka samo kanta wajan haihuwar nan.
   Gaskiya doctor lafiyarta kalau kuma bata da matsalar kwakwalwa saide wajan nakudar nan tasmeta.amma ayi mata x-ray agani ko tasamu matsalar.
    Shikenan ba matsala tana dakin Hutu dan munyi mata allurar bacci kuma ina ganin sainan da 10hrs zata farka.
    Toh likita na gode Allah yasaka da alkhair
   Ameen babu komai Allah ya jikan yaro.
   Ameen thumma ameen tafada tareda mikewa tabar dakin.
    Dakin da maryam take ta nufa tana hawaye yaran sabe akafadarta.koda tashiga tareda sallama dakin shiru ita kadai kwance tana faman bacci sun canza mata kaya.
Zama tayi kusa da gadan tana kallanta.lokaci daya harta canza ta kara wani irin fari fuskar tayi fayau.
    Ahankali takai hannunta ta shafo gashin kanta Har zuwa fuskar ta.
Lokaci daya ta tuna dasu Shaheeda hankali ya kuma tashi batasan lokacin da saban kuka ya kuma kwace mataba.
     Wayata ta dauka tareda kiran gida ta sanar musu da abunda ya kuma faruwa.
   Hankalin kowa ya gama tashi dan suna kaunar maryam din itace Auta acikin gidan.nan suka sanar da Naja insha Allah gobe suna kan hanya.
    Nan ta kuma kiran dan Asabe ta sanar masa.shima hankalin shi ya tashi sosai nan danan yawo asibitin dan ya tausaya mata.

Bai wani dau lokaciba ya iso dan gaba daya baiji dadin hakanba.
    Dakin yabturo da sallama bayan sun gaisa da naja ta mika masa yaran.
   Kallan yaran yashigayi kamar yayi kuka dan yabtausaya mata.
Ahankali yace yanzu bara naje da yaran nan ayi masa sutura akaishi tunada kinga yanzu kamar dare ya fara.
   Shikenan ba damuwa nima bara naje gida dan zan dauko wasu an kaya tunda kaga kwana ya kamani.
    Tare suka fito daga asibitin kowannan su yayi cikin motar sa.

Tana zuwa gida daukar duk abunda zatayi tayi sannan ta fice daga gidan.

Shikuwa Dan Asabe gidan liman din layinsu yakai yaran aka mai wanka aka shirya shi sannan suka kaishi.
   Asibitin ya dawo shima ya zauna sai dare sannan ya dawo koda ya kuma gidan tunanin su Sapna yake ko sunci abinci koya zasuji.dan yasan Umma ba ruwan ta sai kuma ya tuna ai Hafsat nan.kuda yataso zaije ya dubasu sai yaga Har sun kulle gidan hakanan ya koma ya kwanta.Amma tabbas yana tausayama yarana.

👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑
Har gari ya fara haske amma Sapna bata koma baccin ba.
    Ahankali ta sauko daga saman gadan ta nufi toilet alwala toyo sannan tayi sallah.
Zama tayi kan abin sallah tareda fashewa da kuka sosai take kukan sannan ta fara fadin.
   Allah ka dawo mana da Maman mu kasa bata mutuba,Allah kasa mama bata mutuba ta dawo mu rinka zama tare.
    Ma..mahh! Shaheeda ta fada tareda mikewa ta zauna.
   Da sauri Sapna ta goge hawayen idanta tareda hawa kan gadan.
Ta kankameta tana hawayan.
    Ya Sapna ina mama?
Shaheeda kiyi bacci mana ko kinasan dodo ya kamaki.
    Girgiza kanta tayi tareda kara shigewa jikin sapnar tana Ajjiyar zuciya jin an amabaci dodo.
    Ahankali tace ya Sapna toh kar dodo ya cinye mama.
    Bazai ciye taba kiyi shiru in kika kara magana zaizo ya kamaki.
    Kara rufe ido tayi tareda kuma matsewa jikin Sapna.

Tsawan lokaci suna manne da juna.
So take taje tayi wanka ta shirya dan tafiya makaranta.
    Shaheeda! Ta ambaci sunan Ahankali
  Uhmm! Tace.
Bakiyi baccin bah?
   Ya Sapna ni natashi bana jin bacci.
  Toh taso muje muyi shower kinji.
    Toh ai dodo zai kama mu.
   Taso bayanan ai na koreshi.
   Kamo hannunta tayi tareda saukowa daga kan gadan.
   Ya Sapna ina mamana take?
    Bara muyi wanka saina kaiki wajanta ko yn kirki.
   Kai ta daga tana dariya.

Toilet din suka shiga dayake ko ina da hasken huta.
   Kayanta ta cire sannan ta cirema Shaheeda nata.
    Shower ta kunna nan Shaheeda ta fara tsalle cikin ruwa tana dariya.
   Itama biye mata tayi sunata wasa da dariya Har tayi wankanta ta gama sannan yima Shaheeda.
    Towel ta daura sannan ta daurama Shaheeda nata da mama ke mata amfani dashi.
    Nanma da wasa da dariya tayi mata shafa sannan ta sanya mata kaya.
    Itama shiryawa tayi cikin uniform dinta tsaf ta fito.
    Tana cikin saka sos dinta Shaheeda ta kuma fitowa daga daki fuskarta kamar zatayi kuka tana kiran mama dan ta fara gajiya da rashin ganinta.
    Da sauri ta taso tana kiyi shiru muje in kaiki.
   Amma ina hakurinta ya kare dan tsalleta fara tana kuka.kamar Sapna tayi hauka haka ta koma,dan tasan tabbas ta kama wannan kukan nata kafin tayi shiru sai anyi da gaske.
     Kumawa tayi ta zauna ta barta tanata kukan Har tagama shiryawa.
     

Wayarshi ya dauko tare da kiran Hafsat bata jima tana ringing ba ta dauka tare da gaidashi.
     Yauwa taho ki bude gidan mana lokaci yana kurewa kuma dayara daza'a kai mkrnta.
   Tam.tace tareda kashe wayar ta fito ta bude mai gidan sannan ya shigo.
     Inasu Sapna ya tambayeta?
    Suna dakin su.
Kina nufin su kadai suka kwana.
    Habade yaya bade su kadaiba dakin Umma suka kwana dazu na mai dasu daki.
    Ohk kin kyauta Amma Aida kin shiryata kinsan yau akwai mkrnt.
    A zuciyarta tace ai ta isa shiryawa insha Allah tama shirya.
    Yana tun karar dakin nasu yaji kukan Shaheeda, da sauri ya karasa.
    zaune ya ganta tanata faman kuka itama Sapna tana gefe tana hawayen.
    DA sauri ya karasa wajanta tareda daukarta yana fadin lafiya yr kirki.
    Cikin kukan tace mama!
    Itama Sapna da sauri ta taso tana kukan tareda shigewa jikinsa tana fadin yaya dan Allah ka kaimu wajan mamanmu dan Allah yaya.
     Ya isa Sapna yanzu kuzo muje kuyi breakfast sai kitafi makaranta insha Allah nizanje na dauko ki daganan zan kaiki wajan Maman taki.
    Baba komai kinji muje.
Sannan ya fito dasu daga dakin.dakinsu Safiya ya shiga.
Umma na zaune kan kujera a falo.
    Zama yayi sannan ya gaidata bayabo ba fallasa ta amsa.
    Itama Sapna gaisheta tayi Amma bata amsa tataba.
     Kaji maryam bata da lafiya tana asibiti ko?
   Eh jiya ai inacan shiyasa ban shigo da dareba.
    Tasamu karuwa namiji Amma barai yazo.
    Fal taji farin ciki cikin zuciyarta Amma saita nuna bataji dadiba.
    Allah ya jikansa tafada duksuka amsa da ameen.
    Yabjinkin nata Itakuma.
    Toh dasauki za'a ace Amma harna taho bata farkaba.
    Allah sauwake de,ameen nan ma suka fada.
    Safiya dake zaune tana karyawa tunda suka shigo batayi maganaba ya juya ya tambayeta tareda fadin ke dama baki iya gaisuwaba.
      Ayyah kasan itama jiya da zazzabi ta kwana da nacema yau bazata makarantaba amma tunda exam suke nace taje.
    Hmmm! Murmushi Hafsat tayi dan tasan kawai Umma tayi hakanne dankar yaya yayi mata fadane.
    Allah ya sauwake yace.
Ammm Hafsat haduma yarannan breakfast pls.
    Toh tace nan ta shiga hada musu Umma kuwa sai hararar ta take itakuwa tayi kamar bata fantaba dama so take ta basu tana tsoran fada.
    Nan ta hado musu ta anje suka zauna su naci.kamaryasani yaji ltashi yatafi Har suka gama sannan yace toh kutaso na kaiku makarantar.

😘😘😘😘😘😘😘😘😘😘
01 Amal fansclub💅🏻🌷

Written by Zeenaseer😘

MARAICHIWhere stories live. Discover now