Page 1

5K 181 1
                                    

               ★ MAHAQURCI ★

By the Applomb writer:Hamagee

     Wattpad @Hama_gee

Page 1
    "Sugrah! Sugrah!" Abban Sugrah neh ke kiranta,"naaaaam",ta ansa sannan ta fito,a palour ta ganshi zaune kan kujera yana danna remote d'in tv,qarasowa tayi da sallamarta,ya ansa sannan ta nemi gu ta zauna,"sannu da hutawa Abba gani",yace "yauwa Sugrah,nace kin san admission ya fito kuwa?",Sugrah dake ta raba ido tace "aa Abba",Abba yace "ohk,ya fito toh d'azu na gani a news saeki duba naki",Sugrah tace "toh Abba barin je in duba",Abba yace "yauwa,ga recharge card kisa saekiyi suscribing"Sugrah ta karb'i recharge card d'in sannan tace "nagode Abba",Abba yace "it's ohk",Sugrah ta tashi ta koma d'akinta duk jikinta rawa yake,hawaye neh ya soma zubo mata,tana cikin wannan yanayin wayanta ya soma ringing,ta share hawayen fuskarta tareda daedaeta muryarta kafin ta ansa wayan,"hello Taqiyya"sae akayi mata magana ta wayar ta ansa da "wllh ban duba ba amma yanxun nan zan duba",sae kuma tace "ohk"sannan tayi hanging call d'in,ta d'au recharge card d'in da Abba ya bata tasa sannan tayi sub ta duba,tana dubawa kuwa ta samu anyi releasing admission d'in kuma ta samu,wani baqin ciki neh ya cikata,ta kai 30mins tana cikin wannan yanayin kafin ta tashi ta fito palour inda ta tararda Abba da Ummee suna hira,tayi sallama suka ansa sannan ta qaraso ta nemi guri tazauna,ta dubi Ummee tace "sannu da hutawa Ummee",Ummee tace "yauwa Sugrah,Abbanku ya fad'a mun admission ya fito ko?",Sugrah ta qago murmushin qarya tayi sannan tace "eh harna duba ma yanxu haka nazo fad'a muku cewa na samu neh",Abba da Ummee suka ce "Alhmdllh"a tare sannan sukayi ta encouraging Sugrah kan maganar karatunta daga qarshe sukayi mata addu'a tareda fatan alkhairi kafin ta tashi ta bar wurin.. Tana komawa d'aki ta soma kuka tana tuna irin soyayyarsu da Sagir wanda yanxu kimanin shekara guda kenn da suka had'u,tana sonshi shima yana matuqar sonta dan haka suke sonyin aure nan bada jimawa ba gashi daga dukkanin alamu iyayenta bazasu barta tayi aure ba saeta gama karatun saboda sau tari Abban ta yana mata magana kan halinda y'ar uwarta ke ciki a halin yanzu,akwae yarta kafin ita me suna sumayya,Sumayya nada mugun ilimi ga son karatu amma iyayen basu barta taci gaba daga secondary school ba gashi a halin yanxu mijin data aura yaqi barinta ta cigaba da karatun bayan anyi dashi kan bayan auren zata cigaba kuma ya amince,sannan wulqancin yau da ban na gobe da ban,kullum ta tambaye shi abu sai yyi mata qorafi wae ta fiye yawan tambayan abu ance mata neman kud'in abu me sauqi neh,tun bata fad'a ma kowa harta kai yanxu iyayen sun gano halinda take ciki so sune masu tmakonta,wannan dalilin yasa Abban Sugrah kafewa kan sae Sugrah tayi karatu da tayi aure wae duu da duu Sugrahr nawa take dan yanxu neh ma take shirin cika 17yrs ya kama zata gama University harda serving at the age of 22 kenan,ita kuma Sugrah tun tana ss2 take da burin aure tana qare secondary school d'inta.. Tashi tayi ta shiga toilet dan yin alwala saboda kiran sallahr data ji na la'asar,bayan ta fito tazo ta gabatar da sallah sannan tayi addu'oi ta tashi,tana zune a kan gadonta wayanta ya soma ringing,koda ta duba sae tayi kmar bazata d'auka ba da ta ga me kiran,sae kuma ta d'aga,tayi sallma ya ansa sannan suka shiga gaisawa,Sagir ne me kiran..

     hghausanovelseries.blogspot.com

MAHAQURCIWhere stories live. Discover now