Page 22

879 61 0
                                    

           ★ MAHAQURCI ★

By the Applomb writer:Hamagee

     Wattpad @Hama_gee

Page 22
    Around 12:07pm su Khausar suka shigo gida,kai tsaye side d'insu suka shiga,suna shiga palourn maman suka samu tana zaune fitowarta kenan.Suka gaisheta sannan tayi musu sannu da dawowa,saeda sukayi wanka sannan sukayo alwala sukazo sukayi sallahn tare dan lokacin qarfe d'aya neh da y'an minutes,bayan sun idar Sumayya ta kawo musu abunci sukaci kafinnan sukayi bacci,dan baccin rana sana'ar su ceh dama,haka da la'asar tayi sukayi sallahn tare,haka magrib da isha,bayan sunyi dinner kuma sae suka kwanta dan gobe Sunday da islamia. Rayyan da Rayyana kuwa sabgarsu kawae sukeyi basu kula Sumayya da yaranta wanda hakan na faruwa neh saboda yadda Rayyana take so kenan,kuma idan Rayyan bai bita a hakan ba toh zasu samu matsala kuma baya son hakan.Abunda ke mun dad'i kuwa abun baya damun Sumy koh kad'an.Abunda keh gabanta a yanzu shine Jamb da take shirin rubutawa dan yanzu saura 8days su fara. 💦💦💦💦💦💦💦💦💦 Sugrah anata shirye-shiryen fara registration dan har sunyi screening,koda yaushe suna waya da Sumy dan jin yadda abun nasu yake,koda Sumy ta fad'a mata cewa ae baya kulata Sugrah batayi mamaki ba dan dama tasan za'a rina (wai an saci zanin mahaukaciya,yace a rina!! 😂). *************************** Ranan Monday da wuri Sumayya ta tashi ta shirya yara itama ta shirya akan zata kaisu makaranta saeta wuce exams d'inta daga nan,sun firo main palour kenan saega Rayyan ya fito,shima ya shirya daga gani office zashi dan har gudu gudu yake,tayi kamar bata ganshi ba da had'a kan yaran tace "muje kar muyi late koh!",sukace "toh Mummy",Khairat ceh tace "Daddy ina kwana!". Rayyan ya ansa da "lafita mamana,an tashi lfya?",yayi maganar cikeda fara'a,sauran yaran ma suka gaidashi ya answer,sunanta ya kira "uhm..uhhm,Sumayyah!",bata answer ba sae juyowan da tayi,wani abu yaji wanda be tab'a jiba a gameda ta ita na mai yawo a qwaqwalwa,ta mugun mishi kwarjini fiyeda yadda yake zato,batada niyyar cewa koma dan haka yace mata "muje nayi dropping naku koh",Sumayya da mamakin shi ya isheta saedae bata bari yaga alamu ba tace "let it be,zan sauqesu saina wuce",ta juya zata tafi yace "but why?",ganin yadda ta juyo kamar meh shirin hawa kanshi da duka yace "but anyway,ga keyn mota saeki kaisu ki wuce". Sumayya tace "We don't need it",ta juya tajaa yaranta suka tafi kafin ya qara mata wata maganar,suna fita suka sha wata kwana wanda ya fiddasu daga layin gidan,meh adaedaeta suka gani dake kan hanya neh,ta fad'a cewa ATBU zai kaisu,idan ta ajiye yara a school saeya dawo da ita Prof.Iya Abubakar dan nanne centern da aka bata. *************************** Bayan fitarsu tsayuwa kwae Rayyan yyi yana bin qofar da ido,duk jikinshi yyi sanyi.Ko a mafarki be tab'a zaton Sumayya nada zuciya haka ba,tunano abunda ya faru yyi tayi daga qarshe dae ya fita ya tafi office d'in,ya yanko kwana kenan saya ga shigarsu Sumayya napep d'in,kafin ya qaraso kuwa har sun tafi. Bayan ta ajiye yara ta dawo Prof.Iya,bayan sun fito around 9:30am saeta koma gida tana zaman jiran result nasu ya fito dan after 3hours dama zae fito,har wajen 12:50pm ba'a turo message d'inba dan haka tama cire maganan a ranta.Tashi tayi dan zuwa d'auko yara a scul dan 1:00pm su khausar suke tashi,Khaleel kuwa tun 12:00pm ake tashinsu,dama idan an tashe su primary school d'in yake zuwa shida wasu mates nashi sae su jira a tashi yayunsu kan azo d'aukarsu. Lokacinda Sumayya ta iso *Staff School*,wato makarantar su Khausar,qarfe d'aya harda minti biyar dan da qafa ta shigo kasancewar ba'a barin y'an acab'a shiga ATBU.A waje ta bar d'an adaidaitan ya jirata,tana isa taga su Khausar da Khairat zaune duk sunyi zugum a gindin wata bishiya,ta mayar koh saboda jiran ta da sukayi tayi neh ma.Tana qarasawa Khausar ta taso ta gudu ta rungumeta tana fad'in "Mummy sannu da zuwa! Kinzo kin d'auki Khaleel neh yau? Bamu ganshi ba?".Wani dumm Sumayya taji a zuciyarta.....


    hghausanovelseries.blogspot.com

MAHAQURCIWhere stories live. Discover now