★ MAHAQURCI ★
By the Applomb writer:Hamagee
Wattpad @Hama_gee
Page 10
Har Sumayya tayi bacci Sugrah na nan tanata faman chatting.Ta kai past 12am tanayi,daga baya bacci yyi gabada ita. ★°★°★°★°★°★°★°★°★°★ Bayan tafiyarsu Sumayya,kukan yaran ya ishe Rayyan,ya rasa yadda zaiyi dasu barinma Khaleel d'an qarami dashi,shekarunsa uku kenan,sae Khairat dakeda shekaru biyar,sannan babbar wato Khausar me shekaru takwas yanzu.Yayi yayi dasu suyi shiru amma sunqi,garama Khausar dake ita tanada hankali,ita tayi ta lallashin qannen ma,Rayyan ya rasa yadda zaiyi dasu,saedae bbu yadda ya iya illa ya rarrashe su. Da qyar sukayi shiru,shida kanshi ya shiga kitchen ya dafa musu indomie da qwai ya kawo suka ci.Bayan sun gama saeya tattare wajen tass ya wanke kwanukan ya kifa,bayan nan saeya dawo palourn inda ya tararda su har sunyi bacci,d'aya bayan d'aya ya d'aukesu yaje ya kwantar a d'akinsu sannan ya dawo palour ya zauna yanata tunani. Damuwarshi a yanzu kwae ta yaran ceh,saboda irin kukan da sukeyi.More especially ma Khaleel da bai saba zama bbu mamanshi a kusa ba,saedae ya sama ranshi koma miye zasu daena dan yazamo dole su saba.A halinda ake ciki yanzu baya son sake zama da mamansu,because aure yakeson yi anyhow,yana cikin wannan tunanin ya d'aga wayarshi ya kira wata wacce yyi saving sunanta *Soulmate*,ba'a jima ba ta d'aga wayar,yace "hello soul",daga wajenta ta ansa da "hy lurvely",Rayyan na mugun son sunanda take kiranshi dashi wato 'lurvely',ba kad'an ba sunan na burgeshi,nan suka cigaba da hirarsu inda Rayyan ya sanarda ita duk abunda ya faru yau,wani abun takaicin shine maimakon ta bashi shawarar cewa abunda yyi be kyauta ba sae tace dashi "you've done a great job myn,you she's always a barrier in our relationship,so I think this is the right time to divorce her,from then I could only be yours and no one else's". Ba kad'an ba Rayyan yaji maganar nan har qwaqwalwar shi amma he couldn't help but to agrees with what she said.He sighted a heavy breath kafin yyi making up mind nashi,yace "all you've just said was true,and I have to do something anyhow,just trust me you'll soon be mine,because I'll not allowed that wrath that's called my wife to come between us again,I lurve you",murna kamar zai kashe Rayyana,sunanta kenan dama. Bayan sun gama wayar sae yyi hanging sannan ya d'an kwanta,bacci tuni yyi gaba dashi.Around 3:40pm ya tashi nanma kukan Khaleel neh ya tashe shi,yazo gurinshi yana ta kuka yana dukan jikinshi yana kiran 'Moomi',haka suke kiran mamansu dama. Tashi yyi da sauri,ya shiga rarrashin shi,saeda yyi shiru kafin nan ya tashi yaje yyi alwalawa ya tafi masallaci dan lokacin ake kiran sallahn la'asar.Bayan ya dawo ya d'ebi yaran sukaje wani shop,inda ya sae musu,icecream,biscuit,chokolate,da ire-irensu dae kafinnan suka dawo gida,kuma yace musu mamansu taje anguwa neh amma zata dawo dan d'azu sunyi waya tace mishi ta kusa dawowa,da haka ya samu yaran suka d'an sake har suna walwala kamar basu bane masu kuka d'azu ba. Da daddare yyi musu pudding suka sha kafin nan yasa sukayi bacci da wuri dan gobe Monday akai zuwa scul,kuma dukansu suna zuwa makarantar. Bayan ya kwantar da yaran kuwa ya jima beyi bacci ba dan saeda yasha hirarshi da Rayyana kafin nan yyi bacci. Cikin dare yaran suna bacci yaji kukan Khaleel,haka ya tashi yaje d'akin nasu dan duba meya sameshi,yana shiga ya kunna lamp d'in sannan ya isa gare shi. Wae ruwa zae sha,ya fad'a mishi cikin maganarsa da ba kowa ke ganewa sosae ba,nan Rayyan ya tashi ya dauko ruwa yazo ya bashi yasha sannan ya lallab'a shi yyi bacci,harya fita sae kuma ya dawo ya d'auke shi ya tafi dashi d'akin shi dan karya sake tashi ya damu sauran suna bacci..hghausanovelseries.blogspot.com
YOU ARE READING
MAHAQURCI
Teen FictionTabbas mahaqurci mawadaci neh,babban abinda littafin nan yake nuni dashi kenan,bayan wannan sai biyayya wa iyaye. Duk hukuncin da iyayenka/ki suka zantar akan ka/ki koda kana ganin baiyi maka ba to kayi haquri kayi musu biyayya,yin hakan zai sa ka s...