★ MAHAQURCI ★
By the Applomb writer:Hamagee
Wattpad @Hama_gee
Page 14
Sallah ta koma tayi tareda yin addu'oi,ta jima a zaune kafin ta tashi taje d'aura breakfast dan lokacinma Abbaa ya dawo harya kwanta kuma sai safiya ta farayi yake dawowa.. Bayan fitar Ummee Sugrah ta tashi tayi alwala tazo ta tada Sumayya kafinnan tayi sallahn,Sumayya ma tashi tayi jiki bbu qwari taje tayo alwala tazo tayi sallah.Bayan Sugrah ta idar saeta koma gado hakama Sumayya.Sai can around 6:30am Sugrah ta tashi taje kitchen,anan ta taradda Ummee,bayan sun gaisa saeta soma tayata da aikin da takeyi. Bayan sun kammala komai sae Sugrah ta d'an share palourn tayi dusting tareda yin mopping ko'ina kafin suka kai abincin palourn.Nan ta gyara kitchen d'inma tass tayi mopping,tabi ta wanke kwanukan da aka b'ata sannan ta dawo d'akinsu ta kira Sumayya suzo suyi breakfast,da Sumy taqi zuwane amma sae Sugrah ta matsa mata,so haqura tayi ta fito.Bayan Sumy ta fita sae Sugrah ta gyara kan gado ta karkad'e sannan ta share d'akin tass kafinnan ta shiga tayi brush,tana fitowa ta nufa palour. Bayan Sumayya ta fito,kwanciya tayi a palourn tana jiran fitowarsu dan lokacin su Ummee ma basu fito ba tukun.Sae bayan d'an wani lokaci suka fito dukansu.. Sugrah na fitowa ta samu su Abbaa ma sun fito kenan dan taji lokacin suke gaisawa da Sumayya.Qarasawa tayi itama ta gaida Abbaa sannan suka zauna dukansu a qasa a palourn sannan suka fara yin breakfast. Bayan sun kammala sae Sugrah ta kwashe komai ta kaisu kitchen sannan ta dawo,nan sukayi ta tattaunawa kamar yadda suka saba kowane Saturday da Sunday a wajen sukeyi breakfast sannan idan sun gama sae su shiga tad'i dan sauran ranakun iyayen na fita aiki so basu samun lokacin zamada yaran saedae da daddare.. Bayan sun jima suna yi sae Abbaa yace dasu bari yaje ya shirya dan ya samu halarta d'aurin auren y'ar abokin shi wato d'aurin auren Rayyana da Rayyan (twins,injisu da fad'a),saboda mahaifinta ya gayyace shi so bazae qi zuwa ba.Su ummee kuwa basu tashi daga wajen ba sae lokacin d'aura abincin rana. *Bayan d'aurin auren Rayyan*,, ************************** Bayan y'an biki sun watse saura ango da amaryarsa,sallah suka tashi sukayyi tareda yin addu'a,bayannan Rayyana tace ita bacci takeji lokacinda yace suci naman kazar daya kawo.Rayyan yyi yyi da ita amma firr Rayyana taqi wae ta qoshi.Haka ya haqura ya barta bada son ranshi ba,Rayyana kuwa bbu koh kunyar nan irinta first night da amare keh ji,ta shiga toilet ta watsa ruwa kai kace gidan ubanta take,bayan ta fito da towel a qirjinta tazo gaban mirror tayi shafe-shafen ta sannan tazo ta nemi wata y'ar rigar bacci qarama tasanya saeta zo ta kwanta can qarshen gado,tajaa mayafi kuwa ta luhu. Duk wannan shed'anancin a idon Rayyan tayi shi,shi kuwa bbu abunda yace banda idon daya zuba mata.Mamaki neh ya isheshi,daga qarshe dai ya tashi shima ya shiga toilet d'in yyi wanka ya fito,shima night wear d'in shima ya sanya sannan yabi ya kashe wutar d'akin,gefen Rayyana yazo ya kwanta yana qoqarin gyara kwanciyar shi. Da sauri Rayyana ta tashi da tsiwarta take magana "haba Rayyan bazaka bari mutum ya d'an samu hutu ba,ka duba dae gajiyar bikin nan da mutum yasha,amma bazaka barni na huta ba? Nikam toh gaskiya bazan lamunta shekace dama jira kke a kawo maka ni,ass hole!!",tajaa tsaki bayan ta qare maganar...
hghausanovelseries.blogspot.com
YOU ARE READING
MAHAQURCI
Teen FictionTabbas mahaqurci mawadaci neh,babban abinda littafin nan yake nuni dashi kenan,bayan wannan sai biyayya wa iyaye. Duk hukuncin da iyayenka/ki suka zantar akan ka/ki koda kana ganin baiyi maka ba to kayi haquri kayi musu biyayya,yin hakan zai sa ka s...