★ MAHAQURCI ★
By the Applomb writer:Hamagee
Wattpad @Hama_gee
Page 11
Bayan ya kwantar dashi sae shima ya kwanta a gefen shi,a haka bacci yyi gaba dashi.. ************************** Washegari da asuba around 5:30 Sumayya ta tashi tayi wanka,tayi brush tareda d'auro alwala sannan ta fito ta tashi Sugrah,bayan ta tasheta saeta zo tayi sallah,Sugrah ma bayan ta fito sallahn tayi.Bayan sun idar sae suka koma bacci. Saeda gari ya waye kafinnan Sugrah ta tashi ta je kitchen ta d'aura breakfast,doya da qwai ta soya musu sannan ta dafa ruwan tea ta zuba a flask,ta je ta jera komai kan table abun sha'awa kai kace ma itace matar gidan,dan bbu aikinda Sugrah bata iyashi ba indai a cikin gida ne,wannan shine tarbiyyan Ummee,bbu wata me aiki a cewarta suma matane kuma zasu iyayin abunda me aikin ma bazatayi ba. Around 7:00am ta gama komai,lokacin kuma Abba ya fito already yyi shirin tafiya office,nan ta gaishe shi ya ansa cikeda nuna kulawa,tace mishi "breakfast is ready Abba",yace "yauwa mamana,call the rest so we can both have it together koh",tace "sure",sannan ta nufa d'akin Ummee inda ta tararda ita a kan gado amma ba bacci takeyi ba,wayace a hannunta tana latsawa,ta shiga da sallamarta Ummee ta ansa,bayan sun gaisa saeta ce mata tazo suyi breakfast,Ummee tace "harkin gama?",Sugrah tace "eh",sae Ummee tace "toh muje",Sugrah ta miqe Ummee na biyeda ita suka fito palourn,inda Ummee ta qarasa wajen dining itakuma Sugrah ta nufa d'akinsu. Ta tashi Sumayya tazo suyi breakfast,Sumayya tace taje tana zuwa,Sugrah tace "ohk" sannan ta fita.Palour ta koma inda Ummee ta tambayeta ina Sumayyan,Sugrah tace mata "tace tana zuwa",Ummee tace "toh",Sugrah tayi serving plate d'in kowa harda na Sumayya,ta had'a ma kowa tea,Abba baya shan sugar so ta sa mishi zuma dama dashi yake shan tea. Bayan fitan Sugrah Sumayya ta tashi ta shiga toilet ta kurkure baki sannan ta fito ta d'au d'ankwalinta ta d'an yafa shi a jikinta kafinnan ta fita. Ta shigo palourn da sallama,kowa ya ansa sannan tazo ta gaidasu Ummee da Abba sannan tayi joining nasu sukayi breakfast,bayan sun gama Abba ya tafi office hakama Ummee dake yau tana da lecturing,dama ita lecturer ceh a nan Federal Polytechnic Bauchi.Ta shirya ta tafi around 8:00am. °°°°°°°°°°°°°•••••••°°°°°°°°°°°°°° Da asuba yau Rayyan ya tashi,bayan yyi sallahn asuba be koma ba,yayi ma khaleel wanka ya shirya shi,saiya tashi Khausar da Khairat suyi wanka dama su sukeyi wa kansu wani lokacinma Khausar na iya yiwa Khaleel d'in,idan irin aiki yyi wa maman yawan nan. Tea da bread sukayi breakfast dashi bayan sun gama shirya sannan ya kaisu scul shima ya wuce office,bayan an tashi su Khaleel dake a nursery one yake, sae yaje ya d'aukoshi ya dawo dashi office gurinshi sannan yaci gaba da aikinshi bayan ya saya mishi abunda zae ci. Around 1:10pm ya tashi a office dan lokacin tashin su Khausar yyi dake su a primary suke,Khausar ita a primary four take while Khairat a primary one,bayan ya d'auke su saeya kaisu gidansu,wato gidan Grandparents nasu. Haj. tayi murnar ganinsu sosae,dan haka tayi musu tarba sosae,anan suka ci abincin rana sukayi sallahn azahar,koda hajiya ta tambayi ina Sumayya sae Rayyan ya fad'a mata qarya da gaskiya,wae daga kwae ya magana kan zuwa gaisheta saeta zazzage shi taci mishi mutunci,wae qanwarta ma taci mutuncin shi taja ta suka tafi,Hajiya tace "wa'iya zubillah,yanzu saboda zuwa gaisheni matarka taci mutuncin ka,amma nayi mamaki sosae saboda batayi kamada mara mutunci ba",Rayyan yace "ai ni kad'ae nasan irin zamanda mukeyi da ita dan bana fad'a miki neh kwae",Hajiya tace "toh Allah ya sauwaqe,amma kaje bikonta ina? Koh kuma nayi ma kawunka magana",Rayyan ya d'an sosa qeya sannan yace "ai ki barta kwae hajiya ba yanzu ba,saeta horu tukunna",hajiya tace "toh Allah shi kyauta,amma banji dad'in hakan ba Allah". Bayan sun gama tattaunawa sae su Rayyan d'in suka tafi gida,inda Hajiya tayita shan mamakin Sumayya..hghausanovelseries.blogspot.com

JE LEEST
MAHAQURCI
TienerfictieTabbas mahaqurci mawadaci neh,babban abinda littafin nan yake nuni dashi kenan,bayan wannan sai biyayya wa iyaye. Duk hukuncin da iyayenka/ki suka zantar akan ka/ki koda kana ganin baiyi maka ba to kayi haquri kayi musu biyayya,yin hakan zai sa ka s...