★ MAHAQURCI ★
By the Applomb writer:Hamagee
Wattpad @Hama_gee
Page 9
Da yamma lis dukansu suka je kitchen suka d'aura abincin dare,sunayi suna hira har suka gama sannan Sugrah da Ummee sukayi sallah.Bayan sallahr isha suka had'u dukansu suka cii abinci cikin annashuwa da jin dad'i. Bayan sun gama hira da daddare around 9:30 Sugrah da Sumayya suka koma d'aki,saura Ummee da Abba.Suma d'in 10:00pm suka shiga bacci. Bayan su Sugrah sunje barci, wayarta ceh tayi ringing daga ganin me kiran saeta d'aga cikeda d'oki,bayan sun gaisa sae me wayar keh fad'a mata wani abu,murna Sugrah ta shiga yi tace "gobe gobe my dear?",daga d'ayan hannun aka ansa mata,saeta ceh "toh Allah ya kiyaye ya kuma bada sa'a",nan suka d'an tab'a hirarsu kafin nan suka hanging. Sumayya ceh ta tambayi Sugrah "wannan kuma waye?"cikin wasa,Sugrah tace "sunanshi Sagir,mun had'u dashi for the past one year,ina sonshi shima na sona har muna sinyin aure,dama munyi niyyar ina gama secondary school d'ina fito,but unfortunately,Abba yaqi,wae saena qare first degree,yanzu daga nan zuwa good four years kafin nayi aure",ta d'anyi tagumi,Sumayya dake kallonta tunda ta fara maganar cikeda tausayawa tace "ayyrh kiyi haquri,duk wannan abun saboda nineh,da badan auren da nayi haka bane da Abba bazae tab'a cewa saekin yi karatu da kiyi aure ba dan Abba meson abunda d'anshi keh so neh,kuma..",da sauri Sugrah ta katseta sannan take cewa "haba adda Sumy,why do you have to blame yourself? By the way ninayi farin ciki da hukuncin da Abba ya yanke,kinga yanzu zamu qara shaquwa da Sagir sosae kuma shima ta dalilin hakan zae koma ya cigaba da karatun,sannan koba don haka bama,dole inbi umarnin shi da kuma duk wani abunda nake so saboda albarkar iyaye itace komai.Kinga yanzu koda auren nayi,ina iya rashin dacewa da rashin samun kwanciyar hankali saboda bijirewa iyaye danayi,yanxu look at what just happened to you,baki bijire musu amma ya jarabce ki da wannan mijin toh balle kuma ace kin bijire musu,da yaya zaki kasance? Shiyasa yanzu duk maza suke ban tsoro saboda abunda na gani yau ya zame mun ishara",Sumayya tace "hakane Sugrah,kuma naji dad'in rashin bijirewar da kikayi musu dan wallahi namiji ba d'an goyo bane,yanzu zakiga kuna soyayyar ku kamar zaku lashe juna amma fa idan anyi auren nan toh zance yasha bam-bam,kuma wllhi ki tambayi kowaye kiji,soyayyar waje daban take dana cikin gida ko kad'an ba d'aya bane ga kowa kuwa,duk kuwa irin soyayyar da sukeyi,so a rayuwar ka ya kamata karka bar baya da qura...." Sugrah ta nisa sannan tace "hakane adda Sumy,gaskiya maza basu kyautawa,amma let that aside,yanzu ki kwanta ki huta danni lokacin baccina beyi ba tukunna",Sumayya tayi dariya tace "au keh har wani lokacin bacci neh dake?",Sugrah da dariyar takeyi itama tace "iyi,kullum inna shigo d'akinnan sae wajen 12:00 nake bacci wani lokacin ma bansan lokacin da baccin ke d'aukana ba,saedae in tashi in samu wayar can gefe",Sumayya tace "lallae kuwa, nikam toh bana wasa da bacci dan haka barin kwanta",dukansu sukayi dariya sae Sumayya ta tashi ta shiga toilet tayi fitsari da alwala sannan ta fito tayi addu'arta ta shafa saeta kwanta kamar yadda ta saba yi kullum.Tunanin yaranta neh ya fad'o mata,bata san halinda suke ciki ba yanzu saedae tasan koma miye Rayyan bazae cutarda su ba tunda ya'ya'n shine,da qyar ta samu tayi bacci.hghausanovelseries.blogspot.com

ESTÁS LEYENDO
MAHAQURCI
Novela JuvenilTabbas mahaqurci mawadaci neh,babban abinda littafin nan yake nuni dashi kenan,bayan wannan sai biyayya wa iyaye. Duk hukuncin da iyayenka/ki suka zantar akan ka/ki koda kana ganin baiyi maka ba to kayi haquri kayi musu biyayya,yin hakan zai sa ka s...