Page 2

2.1K 103 0
                                    

             ★ MAHAQURCI ★

By the Applomb writer:Hamagee

     Wattpad @Hama_gee

Page 2
    Bayan sun gama gaisawa Sugrah take mishi maganan admission ya fito kuma ta samu,Sagir yyi mata murna sosae amma saedae ya fahimci kamar Sugrah bata jin dd'i dan haka ya tambayeta ko lfya,tace mishi "bbu komai",yace "anya kuwa naji gaba d'aya kin sauya neh", tace "bbu sauyawan da nayi kai dae kwae kaji yakan neh",yace "toh Allah yasa,kin san meh?",tace "ameen,saeka fad'a",yace "da a lissafina sae bayan aurenmu ki soma karatun nan amma yanxu dole saekin d'an fara,amma insha Allahu nan bada jimawa ba dan har na sanarda Babanmu izinin turowa kwae nake jira daga gareki",shiruu Sugrah tayi ta kasa cewa komai,koda yyi mata magana saeta fad'a mishi gaskiyar lamari saboda tunda wuri su san nayi,koda ta sanarda shi cewa Abba baya son tayi aure saeta kammala University yaji dad'i sosae amma sae yyi qoqarin bata qarfin gwiwa yace karta damu zae aiko iyayenshi qila idan yaga haka ko zae amince musu,ta yarda da batun shi dan har ta d'an ji sauqi a zuciyarta,a haka sukayi sallama.Ba kad'anba Sagir ya shiga tashin hankli dan a ganinshi kamar rabashi da wani b'ari na jikinshi ake shirin yi duk ya damu,daurewa kwae yakeyi,a haka ya sanarda mahaifinsa cewa yana so aje nemn masa auren Sugrah,bbu tantama kuwa mahaifin ya amince kan zuwa gobe insha Allahu zasu je.. Shi dae Sagir hankalin shi be wani kwanta ba dan yasan zaeyi wuya Abba ya amince tunda ya fad'a saedae kuma ya d'aukan ma kanshi alqawarin cewa biizinillah saeya mallaki Sugrahr shi,wannan kenan.. Ta wajen Sugrah kuwa hankalin ta ya d'an kwanta dan a ganinta Sagir ya kawo musu mafita yanxu,kuma tasa ma ranta in aka tambayeta cewa tana son Sagir zata ceh musu ehh.Wayar tace tayi ringing saeta d'aga,Sagir neh ya sanarda ita cewa yyi magana da Baban kuma yace dashi zuwa gobe zaizo,murna wajen Sugrah bbu magana,shi dae Sagir yasan kwae yarinta ke damun Sugrah amma inba haka ba yaushe zatayi tunanin wannan matsalar tazo qarshe,a haka sukayi sallama kowa da irin tunanin da yakeyi. Sugrah na murnar gobe zata huta da abunda ya jima yana damunta shikuma Sagir na tunanin gobe soyayyarsu zata zo qarshe.Bayan sallahn magrib Sugrah taje kitchen tayi musu dinner ta kawo palour kowa ya ci,bayan sun gama saeta kwashe shirgin ta kai kitchen ta wanke su ta kifa,tazo tayi masu Ummee saeda safe sannan ta nufa d'akinta dan bacci take ji,da tunanin gobe ta kwanta.Sagir ma bayan sunyi dinner ya kwanta bacci,shima tunanin goben yake tareda addu'ar mafi alkhairi.Wayan shi ya d'auko ya gwada kiran numbern Sugrah,ya kira wajen sau uku amma bata d'aga ba wanda hakan yana tabbatar mishi da tayi bacci kenan,dan haka ya haqura ya bar kiran yyi baccinsa shima... Washegari da asuba Sugrah ta tashi tayi alwala tayi sallah sannan ta koma bacci dan lokacin ana d'an tab'a sanyi,lokacin ta d'au wayarta dan ganin time sae taga missed calls d'in Sagir,koda ta duba time d'inda ya kira saeta ga tun jiyane dan haka kwae saeta ajiye wayar dan tasan koma ta kira shi yanzu kam yana masallaci dan har yanxu ba'a idar da sallahr ba a wasu masallatan,baccin tayi me dad'i...

     hghausanovelseries.blogspot.com

MAHAQURCIOù les histoires vivent. Découvrez maintenant