Page 5

1.3K 77 0
                                    

           ★ MAHAQURCI ★

By the Applomb writer:Hamagee

     Wattpad @Hama_gee

Page 5
    "Najin dad'in hukuncin daka yanke both am gonna miss u"inji Sugrah dake magana kamar me shirin yin kuka,Sagir yyi qarfin hali dan yyi cheering nata up yace "ohh really",yana dariya,tace "look at u,damn it",yace "I'm gonna miss u more myn",tace "yanzu wane uni zaka tafi kenan?",ya d'an nisa tukunna yace "wllh naga wani kwanan nan a net wae SKYLINE a U.S yake,I think can zani",tayi shiru kamar me tunani sannan tace "toh Allah ya bada sa'a",yace "ameen",daga bisani sukayi sallama sae yyi hanging up call d'in. Ta jima tana tunanin shi kafin bacci yyi gabada ita,shima baccin yyi daga baya. Ba ita ta tashi ba sae ana kiran sallahr magrib,tana tashi ta shiga toilet tayi alwala ta fito tazo tayi sallah,tana idarwa ta fita tayi kitchen,anan ta samu Ummee tana qoqarin d'aura dinner,nan tazo ta taimaka mata suka d'aura tuwon daman d'azu tayi miyarta ta ajiye,suna cikin zaman jiran ruwan tuwo ya tafasa sae Ummee tayi noticing kamar Sugrah na cikin damuwa dan haka tayi maza ta tambayeta damuwarta "me ke damunki neh Sugrah",Sugrah tayi maza tace "nih kuma Ummee,bbu komai",Ummee ta girgiza kai tace "Sugrah kenan,karki manta nice na haife ki kuma nasan farin cikinki da kuma rashin sa,dan haka u just have to tell me what's bothering you anyhow",Sugrah ta nisa kamar wacce ta dawo daga tunani saeta ceh "Ummee ni bbu abunda yake damuna kwae ina jin wani irine kuma kinga kaina ma yana mun ciyo",Ummee tace "it's ohk then,amma ina so ki kwantar da hankalinki ki nutsu waje guda ki samu kiyi karatun ki dan shine gatanki,karki ga koh bama sonki neh muka takura ki akan sae kinyi karatun nan,muna miki gata neh amma zuwa nan gaba zaki fahimta",Sugrah tace "bbu komai Ummee,na yarda cewa zab'inda kukayi mun shine zab'i mafi alkhairi a gareni kuma insha Allahu zaku samen me biyayya ga dukkan umarnin ku",Ummee taji dad'in maganganun Sugrah dan haka tace "Allah yyi miki albarka",Sugrah tace "ameen Ummee nah",nan suka cigaba da hirarsu har ruwan ya tafasa Sugrah tayi talge,bayan d'an wani lokaci ta tuqa tuwon ta kwashe,tare sukayi setting table d'in sannan Ummee ta kira Abba sukayi dinner tare cikin annashuwa,su Ummee sunji dad'in yadda suka ga Sugrah bata sa damuwa a ranta ba gashi tana shirye data bi dukkanin umarnin da suka bata. Bayan sun gama sae suka d'anyi hira suna kallon tv kafin suka je suka kwanta. Koda Sugrah taje d'aki bata wani yi bacci ba,chatting d'inta tasha dan bata jin bacci saboda baccin da tayi d'azu,around 12:30am ta samu tayi bacci. Washegari da yamma Taqiyya tazo gidansu Sugrah,Sugrah taji dad'in zuwanta matuqa,batada wata qawa data wuce ta dan Sugrah bame tara shirgin qawayen nan bane dama da ita kad'ae take mu'amala gashi sun zamo kaman y'an uwa dan komai nasu tare sukeyi,kuma kowannen baya b'oye ma d'an uwanshi wani abu.Bayan sun sha hirarsu sae Sugrah take mata tad'in abunda ya faru jiya na zuwan iyayen Sagir da kuma yadda akayi,har zuwa hukuncin da suka yanke ma kansu itada Sagir d'in,Taqiyya ta tausaya musu k'warae saedae tayi ta baki kan abunda suka yanke daedae neh kuma su cigaba da bin umarnin iyaye insha Allahu zasu samu dacewa.Sugrah tayi mata godiya ita kuma tace bbu komai,daga qarshe Taqiyya tace zata tafi gida dan lokacin magrib ya kusa,Sugrah ta rakata tayi sallama ma Ummee sannan tazo ta mata rakiya,bayan ta hau adaedaeta sae ta dawo gida ita kuma ta wuce gudansu..

    hghausanovelseries.blogspot.com

MAHAQURCIWhere stories live. Discover now