★ MAHAQURCI ★
By the Applomb writer:Hamagee
Wattpad @Hama_gee
Page 24
Duk abunnan a idon Rayyan aka yi shi,bece komai ba itama batace qala ba tayi wucewarta da yaran.Bayan sun wuce sae Rayyan ya tashi ya koma d'akinshi. Around qarfe 8 na dare Sumayya na zaune da yara a palour,sun gama cin tuwo kenan sae wayarta tayi qara alamun shigowar saqo (message),tana dubawa taga Jamb neh sun turo mata scores nata,unexpectedly taga 266 tayi scoring,wani irin farin ciki taji a take tayi sujjada tayi ma Allah godiya,su Khausar neh suka shiga tambayarta abunda ya faru,nan ta basu labari,kamar sunsan meh ake nufi da Jamb d'in suka fara murna suma.Ranan Sumayya tayi kwanan farin ciki,koda ta sanar a gida ma sunyi mata murna sosae tareda fatan alkhairi. ************************** *Months later*.... Sugrah na hango reqeda side bag nata tana ta tafiya,da alamu a gajiye take,tana cikin tafiya ta had'u da wasu yan'mata sae rawar kai sukeyi,nan suka gaisa alaman sunsan juna,course mates nata neh su d'in,d'aya daga cikin yan'matan tace "yanzu gida zaki?",Sugrah ta d'aga mata kai alamun eh dan maganarma wuya take mata,yarinyar ta cigaba "kina qoqartawa gaskiya,idan ance ki dawo hostel saeki maida mutane y'an iska gashi yanzu ae kina fama,kinga da a hostel kke kuwa da ba haka ba,da kina gama lecturen ki zaki je ki huta",Sugrah tace "ae wllh nima kaina na gani yanzu,ina ma da shirin dawowa insha Allah zuwa next semester kafinnan muna year 2",wata daga cikinsu tace "wllh daya fi miki kinga Taqiyya ma a school take",nan sukayi ta hira daga bisani sukayi sallama suka rabu.Su sukayi hostel ita tayi gida. ……………………………… Sumayya kuwa har sunyi waec da neco suma taci yadda ake so,zaman jiran admission takeyi,ta cika medicine anan ATBU dan sunce zasu fara this year,rayuwarta takeyi cikeda jin dad'i,bbu ruwanta da shiga shirgin su Rayyan dukda yanzu ya fara dawowa daga rakiyar Rayyana dan yanxu kullum cikin fad'a suke da ita.Yara kuwa tayi tayi harta gaji kan ya ya bari zatana kaisu da d'aukosu amma fir Rayyan yaqi,yanzu shiya ke kaisu ya d'aukosu,duk wata hanyar da Rayyan yasan zaisa suma close to eachother yana binta while Sumayya kuma tana b'ullewa hanyar. A kwana a tashi bbu wuya,Sumayya ta samu admission hartayi registration a makaranta,yanzu saura 2weeks su koma.Sugrah kuwa aji biyu zata koma yanzu,maganar komawa hostel kuwa har an sama mata d'aki me kyau,dan ita kad'ae ceh a d'akin,gashi an gyara mata shi kamar wani d'akin gida bana makaranta ba. Rayyana ceh zaune ta had'a uban tagumi,duk damuwa ta isheta,tarasa yadda zatayi dan yanzu Rayyan ya dawo daga rakiyarta,baya wani biye mata.Yana nuna mata cewa yaranshi sunfi mishi ita,dan sau tari idan tayi musu wani abun a gabanshi yana tsayar mata,wannan yana mugun damunta. *************** Sumy na zaune a main palour tana kallon wani indian film,lokacin yara sunyi bacci duka dan da daddare neh,Rayyana ta fito d'akinta zata d'akin Rayyan,kamar wacce akayi wa magana,tayi cak ta tsaya,juyowa tayi tana fad'in "keh kuma meh kke jira baki bar palourn nan ba har yanzu?",Sumy bata koh d'aga ido ta kalleta ba balle ta tofa wani abun.A ranta tana mamakin yadda Rayyana take da neman magana. "Magana nakeyi kinmun shiru",Rayyana ta fad'a a tsawace,hakan ya mugun b'ata wa Sumayya rai amma ta danne,maimakon Rayyana ta tafi amma saeta tsaya tana neman wani abun fad'an dan yanzu abu qalilan take jira ya had'asu dan ta gaji da ganinta a gidan,a ganinta Rayyan zae iya rabuwa da Sumayya saboda ita,shiyasa take ta neman ta da magana dan neman sanadi.hghausanovelseries.blogspot.com
![](https://img.wattpad.com/cover/138596769-288-k251185.jpg)
YOU ARE READING
MAHAQURCI
Teen FictionTabbas mahaqurci mawadaci neh,babban abinda littafin nan yake nuni dashi kenan,bayan wannan sai biyayya wa iyaye. Duk hukuncin da iyayenka/ki suka zantar akan ka/ki koda kana ganin baiyi maka ba to kayi haquri kayi musu biyayya,yin hakan zai sa ka s...