★ MAHAQURCI ★
By the Applomb writer:Hamagee
Wattpad @Hama_gee
Page 18
Sumayya ceh tace "ba komai Abbaa nagode,kuma nasan baza kayi abunda zae cutarda ni ba,dan haka zanyi dukkanin abunda ka umarcen dayi dan nasan shine hanyar tsirana".Abbaa ya dubeta yace "yauwa Mamana,Allah yyi muku albarka",dukansu sukace "ameen",Ummee ma ta d'anyi musu nasihu kafinnan sukaje sukayi dinner tare. *************************** *Abunda ya faru shine*,, Uncle Umar yaje gidan Umma wato mahaifiyar Rayyan,a cikin tad'i take fad'a mishi cewa Sumayya na gida,shikuma hakan ya mugun bashi haushi,ace hakan ta faru amma koh sanar mishi Rayyan bazae yi ba,toh ya zamo dole ya dawo da ita koh yana so koh baya so.Saedae be nuna mata cewa yaji haushi har haka ba. Bayan ya bar gidan ya koma gidansa,kiran Rayyan yyi a waya yace dashi yyi maza yazo gidanshi yanzunnan,akwae maganar da yake sonyi dashi,batareda b'ata lokaci ba kuwa Rayyan yazo gidan,nan Uncle Umar ya soma yi mishi fad'a kan abunda yyi sannan yace dashi zaeje ya samu mahaifin Sumayya kuma dole ya dawo da ita,sannan idan ya sake ya sake jin wani abu me kamada wannan ya faru a tsakaninsu,toh zae fuskanci fushinsa. Rayyan yayi mishi alqawarin bazae qara ba kuma zaeyi yadda yace,shine dalilin zuwan Uncle Umar wajen Abbaa a office.Kuma yanzu a halinda ake ciki gobe tare zasu gidansu Sumayya su d'aukota. *Washegari*, Tunda safe Sumayya keh shirya kayanta Sugrah kuma tana kitchen tana breakfast dan yau Friday neh su Ummee zasu aiki,bayan ta kammala suka had'u kamar yadda suka saba sukayi breakfast d'insu,kafin Abbaa ya fita saeda yace ma Sumayya ta gama shirinta dan zuwa anjima bayan an sauko daga sallahr zuma'a Rayyan zaizo d'aukanta,tace mishi toh sannan tayi mishi adawo lfya. Bayan sun gama abincin rana sun gyara gidan,sae sukayi wanka dukansu dan har lokacin su Ummee basu dawo ba,sukayi sallah sannan suka zauna suna d'an hirarsu,sunayi suna qarasa gyara kayan Sumayya tare har suka gama.Can Ummee ta dawo,sallah ta shiga yi kafin Abbaa ya dawo suci abinci.Kafin ta fito kuwa ya dawo,inda suka had'u dukansu sukaci abincin. Around qarfe 3:00pm Rayyan da Uncle Umar suka zo,Sugrah ceh tayi musu iso tareda gaishe su sannan taje ta kira Abbaa da Ummee,suma gaisawar sukayi da suka fito sannan Abbaa yace ta kira mishi Sumayya,Sugrah ta juya taje kiranta.A zaune ta sameta a d'akin,ta fad'a mata cewa Abbaa yace tazo,Sumayya tace "ohk,d'an fitarmun da akwatin saeki bar hand bag d'in sae zamu tafi",Sugrah tace "ohk",tareda jaan akwatin,saeda Sumayya ta fita tukun na Sugrah ta fidda akwatin wajen motar. Bayan ta fitar saeta dawo cikin d'aki abunta sannan tacigaba da game d'inta.Tana cikin yi ta tunoda wani abun,numbern Taqiyya ta shiga nemowa,bayan ta samu saeta danna mata kira,inda take dad'a mata tuni kan abubuwanda zasu je dasu wajen screening d'in dan ran Monday zasu fara,Taqiyya tayi mata godiya tareda tambayarta Adda Sumy,Sugrah tace "gashi can yazo,wae tafiya zaeyi da ita,ni dae wllh bazan tab'a yarda dashi ba in bawae nagama ganin kamun ludayinsa bane dan kinsan namiji wanin munafuki neh,bazaki tab'a gane alqiblarshi ba saekin zauna dashi sosae.Amma nikam nace mata wllhi wannan karon kan ta gasa shi,karta yadda yaci mata kashi idan ba haka ba kuma zata koma y'ar kallo a gidanta dan wannan Rayyanar ba qaramar shegiya bace,mazajen wasu ma tana musu karuwancin nan balle kuma nata.Sannan daga dukkanin alamu Adda Sumy ta fahimcen dan she's ready to did all of this". Taqiyya taji dad'in maganar dan itama ba qaramin haushi halin Adda Sumy keh bata ba,bayan sun gama sae Sugrah tayi hanging.hghausanovelseries.blogspot.com
YOU ARE READING
MAHAQURCI
Teen FictionTabbas mahaqurci mawadaci neh,babban abinda littafin nan yake nuni dashi kenan,bayan wannan sai biyayya wa iyaye. Duk hukuncin da iyayenka/ki suka zantar akan ka/ki koda kana ganin baiyi maka ba to kayi haquri kayi musu biyayya,yin hakan zai sa ka s...