Page 29

975 56 0
                                    

           ★ MAHAQURCI ★

By the Applomb writer:Hamagee

     Wattpad @Hama_gee

Page 29
    Da sallama ta qarasa inda yake jingine a jikin mota,yana ganinta shima ya fara matsowa kusa,ya ansa sallamar.Bayan sun gaisa saiya fara mata introducing kanshi kamar haka "da farko dai sunana *Suraij Muhammad*,mu y'an asalin Maiduguri neh amma yah kawo mahaifinmu nan,so anan muka taso nida wana mu biyu iyayenmu keda,na biyu kuma ina meh baki haquri kan bibiyarki da nayi tayi tun sati biyu kenan yanzu da suka wuce,bazan b'oye miki ba wallahi kinmun neh inasonki,dukda be kamata nazo gareki daga farko ba, kamata yyi na nemi izini amma kar yin hakan ya janyo wani abun shiyasa nace barin tuntub'e ki tukunna,dan Allah ki bani dama Sugrah",mamaki neh ya bayyana qarara a fuskar Sugrah jin ya kira sunanta,ya lura da hakan amma bece komai akai ba,"yah kkayi shiru malama Sugrah?". Sugrah dae ta rasa na fad'i daga bisani tace dashi "naji kuma na gode amma kafinnan inaso kabani lokaci nayi tunani akai tukunna,daga baya zan sanarda kai hukuncin dana yanke",tayi hakan neh saboda tasan kafin lokacin Sagir d'inta yah dawo kuma ya turo tunda yana dawowa za'ayi musu baiko,Surayj kuwa be damuba dajin hakan,kwae cewa yyi "toh Allah yah kaimu",tace "ameen".Bayan sunyi exchanging contact sae sukayi sallama ta shiga gida shi kuma ya shiga motarshi ya tafi cikeda jin dad'in yadda Sugrah ta karb'e shi,dan koh be sameta matsayin mata ba yasan ta mishi halacci. *5days ltr....* Sugrah na kwance a d'akinta around 8:30pm bayan anyi sallahr isha'i,duk a gajiye take,wayarta ceh tayi ringing a karo na farko ta d'aga,Suraij neh dan haka ta d'aga tareda yin sallama ya ansa,gaisawa sukayi kamar yadda suka saba inya kirata saisu gaisa kafinnan yyi hanging up. Ana cikin haka wayarta ta sake ringing a karo na biyu,koda ta duba sae taga numbern Sagir ceh,cikeda zumud'i ta d'aga dan a tunaninta zaece mata sun sauqo daga jirgi neh dan lokacin da zasu tashi ma ya fad'a mata,tana d'agawa tayi sallama,sae kuma taji sab'anin muryarda take sauraron ji,nan akayi mata wata mummunar sanarwa wanda hakan yasaka ta cikin tashin hankali a take.Zuciyarta bugu ta shigayi tana fad'in "no! Noh!! It can be you Sagir,after all this time that we've suffered together just to witness this special day!".Abunda mutumin nan ya fad'a mata shine a lokacinda jirgin su Sagir yazo sauqa,direction d'inshi ya goce wanda hakan yyi sanadiyyar dungurawar jirgin,mummunan accident neh yah auku a wannan lokacin dan bbu wanda yyi rai a cikin mutanen jirgin kaff,bama su kad'ae ba waya'nda suke kusada wajen ma a lokacin saeda abun yah had'a dasu,wayarshi kuma a cikin gawarwakin aka tsinta harda ta wasu ma,ikon Allah yasa basu qoneba shine yah kunna wasu suka kunnu wasu kuma basu kunnu ba so shine ya kira layinta dan shine last numbern da yyi magana da ita. Bayan mutumin ya sanarda ita saeya katse kiran,Sugrah tafi awa a wajen tana kukanda bbu hawaye dan hawayen ma gagararta yyi,daga qarshe tayi tunanin kiran Mamanshi dan sanarda ita daman tanada numbern ta sukan gaisa time to time hakannan.Tana kira taji mamanma cikin tashin hankali take dan taga sanarwar a tv,shi kad'ae takedashi daman sae qanwarshi wato Siyama,yanzu ita kad'ai takeda a duniyarnan,Maman tace da Sugrah sae haquri yanzu ma airport d'in zasu da Abbansu dan d'aukar gawarshi,daga qarshe tayi hanging call d'in. Ranar Sugrah batayi bacci ba tsabagen kid'ima da tashin hankalin da take fusknta.Washegari da safe Sugrah ta sanarda iyayenta komai,sunji mamakin yadda yaran suka riqe alqawarin juna for all this while dan basu ma san suna tare har yau ba,sun tausaya ma ya'rtasu sosae dan haka suka shirya gaba d'ayansu sukaje gidansu Sagir d'in kafin a kaishi gidanshi na gaskiya,Sugrah tayi kuka bana wasa ba ganin gawar masoyinta a gabanta,nima kaina saeda nayi kuka.. Saena aka kai gawar Sagir kafin suka koma gida.Kullum tana zuwa gidan har akayi sadakar uku.Sumayya da Rayyan ma saeda sukaje musu ta'aziyya gidansu Sagir d'in.Allah sarki mutuwa kenan meh raba d'a da mahaifi,me raba masoyi da masoyi,Allah yah kyauta namu qarshen 🙏🏻 .. 3weeks Later.... Muje zuwa a last page...luv you all


     hghausanovelseries.blogspot.com

MAHAQURCIDove le storie prendono vita. Scoprilo ora