★ MAHAQURCI ★
By the Applomb writer:Hamagee
Wattpad @Hama_gee
Page 20
Rayyan yyi enjoying moment d'in sosae,ba dan komai ba kuma saedan yadda yaga yanayin yaranshi ya sauya,gabad'ayan su cikin farin ciki suke.Sumayya kuwa sae shan qanshi takeyi,bata wani mishi fara'a,dan yaran nema amma da bazata tsaya ba dan daga dukkan alamu nasihar Sugrah ta shigeta.Koh sun had'a ido dashi b'ata rai takeyi koma ta harareshi abunta,shiko mamakin sauyawarta kwae yakeyi. Bayan sun gama sae suka shiga cikin gidan dan lokacin magrib ya gabato,yaran na manne da ita dan gani suke kamar in suka motsa daga jikinta zata sake tafiya tabar su,barinma Khausar dake tafisu wayo,tare suka shiga d'akinta inda sukayi alwala dukansu sukayi sallahn tare,addu'oi sukayi sannan suka tashi,inda yaran ke zuba mata surutu,barinma Khairat dan tafi kowa surutu a cikinsu,itace take mata tad'in wae Daddyn su ya kawo wata mata mara kirki gidan,wae kullum bata basu abinci kuma bata kulasu,wae ranan ma ta duki Adda Khausar,ran Sumayya yyi mugun b'aci amma saeta danne tace dasu "kunga wacce Daddynku ya kawo auntyn kuce,so banason rashin kunya ya shiga tsakaninku,what I mean is that karku sake kuyi mata rashin kunya because she's your second Mum ohk!!","ohoh walle ba Mum inmu bace,ranan ma da bugee mana Adda Khaushe kuma bata bamu abunshi,bata kaimu shukul,Daddynmu keh kaimu",Khaleel neh yyi wannan maganar,Sumayya ta mugun jin mamaki ace yaro qarami yasan hakan,amma lallae daga dukkan alamu Rayyan ya d'ebo ruwan dafa kanshi dan tabbas Rayyana ba mutuniyar arziqi bace dan sunyi wa juna farin sani. Lallab'a yaran tayi sannan tace musu "koma miye karku rainata,idan ta dake kuma karkuce mata komai kunji?",sukace "toh Mommy",saedae a ran Sumayya tunanin yadda zatayi dealing da wannan issuen takeyi dan a gaskiya bazata bari Rayyana tasaka mata yara a gaba ba dan ita ba sanin zafinsu tayi ba. ••°°°°°°•••••••°°°°°°•••••••°°°°°°•• Rayyan kuwa side d'inshi ya shiga,inda yyi alwala ya tafi masallaci.Bayan ya dawo kuwa sae a lokacin ya tuno da Rayyana dan haka yyi maza ya shiga side d'inta inda ya tararda ita a zaune tana kallon tv,'wae Rayyana batada wani aikin yine inba kallo ba?yanzu haka nasan koh sallah batayi ba dan ba kowace sallah takeyi ba',Rayyan neh yyi maganar a zuciyar shi kafin ya qarasa cikin palourn. "Salamu alaikum",ya fad'i kafin ya shiga dan batama ji alamar an bud'e qofar ba,Rayyana tayi kamar bata jishi ba dan a cike take yau,ya qarasa tareda zuwa kan kujerar da take zaune ya zauna a kan hannun kujerar dan a one seater take zaune,yace "haba sweet bakiji sallama ta bane?",Rayyana da dama tazo har wuya tace "sallamarka ta banza,gara ma ka riqe abunka dan bama ni ya kamata ace kayi ba,ban tab'a zaton zakaci amanata ba Rayyan,tun yanzu ma kenan balle in mun dad'e". Rayyan yace "subhalla! Mena miki na cin amana sweet? Kema kinsan ina sonki kuma bazan tab'a yin abunda nasan it will come between us ba",a fusace Rayyana ta miqe tsaye tana fad'in "dama ku maza haka kuke,sae ku muzantawa mutum kuma kuzo kuna pretending as if you're innocent,dole kace baka san me ka mun ba tunda dawo da matarka ba laifi bane agunka saboda kana d'okint". Rayyan yama rasa ta inda zai fara yima Rayyana bayani dan yasan abune meh wuya ta fahimce shi,ya d'anyi gathering courage kafin ya fara cewa "kiyi haquri ki zauna dan mu fahimci juna,wallahi banyi hakan danna b'ata miki ba,bbu yadda na iya neh kwae",Rayyana ta qara quluwa,ce mishi tayi "ohk ka rasa yadda zakayi koh,idan baka dawo da ita cikin gidanka ba bakada walwala koh? Lallae namiji munafiki neh,duk abunda nake maka baka gani har sae kaje ka kawo matarka tukun,hummm!! Yanzu na gano ka,amma ka fad'i tsakaninka da Allah meye bana maka,meh ka nema ka rasa aguna?",kuka ta soma yi dan abun ya fara fin qarfinta.hghausanovelseries.blogspot.com
![](https://img.wattpad.com/cover/138596769-288-k251185.jpg)
YOU ARE READING
MAHAQURCI
Teen FictionTabbas mahaqurci mawadaci neh,babban abinda littafin nan yake nuni dashi kenan,bayan wannan sai biyayya wa iyaye. Duk hukuncin da iyayenka/ki suka zantar akan ka/ki koda kana ganin baiyi maka ba to kayi haquri kayi musu biyayya,yin hakan zai sa ka s...