★ MAHAQURCI ★
By the Applomb writer:Hamagee
Wattpad @Hama_gee
Page 13
News castern na kaiwa nan sae aka nuno pre-wedding pic na Rayyan da Rayya,salati kowannen su ya shiga yi.Sumayya kuwa tana tashi tsaye ta fad'i a gun sumammiya. Sugrah ceh ta fara ganin halinda Sumy keh ciki dan haka tayi saurin miqewa ta isa gareta tana salati,nan take hankulan iyayen yah dawo wajen,a birkice Ummee ta miqe ta nufe su,haka ma Abbaa. "Sumayya! Sumayyaa!! Sumayyaaa!!!",Ummee ceh ta shiga qiran sunan Sumy tana jijjigata,duk ta birkice.Sugrah koh banda kuka da addu'a bbu abunda take aiwatarwa.. Abbaa koh tuni ya tashi yaje ya nemi wayarshi,qira ya rangad'awa Dr.Saleh Modibbo,he's their Family Doctor.Nan da nan ya sanarda shi cewa Sumayya tana sume yanzu haka,dan haka ya bar duk abunda yake yazo yyi checking lafiyarta.Dr.Saleh yace insha Allah yana zuwa yanzu. Nan Abba ya dawo inda Sumayya take yace su maidata d'akinsu.Haka Ummee da Sugrah suka d'auketa suka mayar d'akin suka kwantar da ita kan gado,Abbaa yasa Sugrah ta kawo mishi ruwan sanyi.. Ya yayyafa ma Sumayya ruwannan ya kai sau biyar,amma shiru kuke ji.Hakan ba kuwa qaramin d'aga musu hankali yyi ba,Sugrah da Ummee koh sae aikin kuka sukeyi.. Bayan kamar minti shida da yin hakan,sae sukaji bud'e gate,da sauri Abbaa ya fita dan yasan Dr.Saleh neh ya iso. Yana fita kuwa sukaci karo dashi yana shirin shigowa da sauri saurin shi,Abbaa ya qaraso dashi cikin gidan har zuwa d'akinda Sumayya keh kwance sumammiya. Nan da nan Dr.Saleh ya shiga mata duban gaggawa,su Abbaa kuwa zama sukayi a gefe suna kallon abunda keh faruwa,sae addu'ar da sukeyi. Ba'a jimaba Sumayya ta farfad'o tana kiran "Rayyan! Rayyan! Meyasa ka zab'i kamun haka please",Ummee ceh tazo inda take kwance ta riqe hannunta tana lallashinta,Sumayya ta dubeta tace "Ummee ki tambaye shi dan Allah,menayi mishi ya zab'i yamun hukunci ta wannan hanyar? Bayan kuma yasan bazan iya rayuwa bashi ba",tana maganar neh kamar wacce ta fara kwancewa,dan ko kad'an sunsan halin Sumayya da kunya da zurfin ciki,bazata tab'a bayyana damuwarta ba barinma irin wannan balle harta fad'a. Ummee ceh tayi ta lallaminta,daga bisani Dr.Saleh yyi mata allura ta samu bacci,sannan yace kar wani ya dameta dan tana buqatar hutu yanzu,sae kuma ya bada wasu magunguna akan idan ta tashi saeta fara shansu amma kar a tasheta saeta tashi da kanta. Bayan ya gama ya tattara shirginsa yyi gaba.. Kowa jimamin wannan abun yakeyi,duk sun zazzauna a palour.Lokaci lokaci Sugrah keh zuwa dubata. Ga dare ya farayi amma bbu me jin bacci a cikinsu.. Around 1:15am ta farka saedae wannan karon bbu abunda take cewa,Sugrah ceh taje ta sanarda su ummee,da hanzari suka shigo d'akin,kowannen su nayima Sumayya sannu,da kai take ansawa. Sugrah ceh ta d'auko ruwa da magungunan da Dr.Saleh ya ce a ringa bata,tazo ta bata tasha.Sae wajen qarfe 2:30 sukayi bacci ranan,kowa yana jimamin abunda ya faru ranan. Sumayya kuwa tunda ta kwanta take bacci bata tashi ba. Around 5:15am Abbaa ya tashi a bacci,yayi alwala sannan yazo ya tashi Ummee saeya tafi masallaci.Ummee ta tashi tayi alwala kafinnan taje d'akinsu Sugrah ta tasheta sannan tace idan dayi alwalan ta tashi Sumayya sannan saeta bar d'akin..hghausanovelseries.blogspot.com

VOCÊ ESTÁ LENDO
MAHAQURCI
Ficção AdolescenteTabbas mahaqurci mawadaci neh,babban abinda littafin nan yake nuni dashi kenan,bayan wannan sai biyayya wa iyaye. Duk hukuncin da iyayenka/ki suka zantar akan ka/ki koda kana ganin baiyi maka ba to kayi haquri kayi musu biyayya,yin hakan zai sa ka s...