★ MAHAQURCI ★
By the Applomb writer:Hamagee
Wattpad @Hama_gee
Page 23
Khairat ma rungumarta tayi tana fad'in "oyoyo Mummy",Sumayya tace "sannunku,ban gane nazo na d'auki Khaleel ba! When?",yaran suka d'ago daga jikinta,Khausar ceh tace "toh bezo ba yau,kuma dana tambayi su Ihsan sunce yau basu ganshi ba tunda aka tashi,wae su kad'ae suka zo","Subhanallah!! Ina ya shiga toh?",Sumayya ceh ta fad'a cikeda da damuwa,tama rasa yadda zatayi yanzu.Qarshe cewa tayi suje Women Societyn su duba shi (nursery kenan). Bayan sunje makarantar,neman shi sukayi tayi amma inaa,bbu shi ba alamarshi,duk Sumayya ta birkice,ba ita ba hatta yaran sun damu dan Khairat kam kuka ta soma yi.Gashi sunyi tambaya kowa yace be ganshi ba,infact yara kanma an gama d'ibarsu,bbu kowa yanzu. Can wani idean ya fad'o ma Sumayya,tace kodae yabi su Zarah neh? (Maqwabtan sune,gidansu nata bayan nasu).Tattara kan yaran tayi suka fita gate inda suka samu meh napep d'inda keh jiranta harya gaji ya tafi dan yanzu biyu ma ta wuce saboda an tashi y'an International ma,gasu sunata wucewa. Su *Mashkurah,Warji,Aisha Bkc,Sumayyah,Ummi megari,Maimuna VC,Hamagee,Hauwa Abdullahi,Fatima AA,Fareeda manu soro,Rahma yankari,Hajara y'ar mitsila,Aisha Kabeer Garba,Maryam Ahmad,Maryam Saeed,Hauwa A Ahmad da sauran members na A and B class* na hango sunata shan surutu a hanya,barinma Warji da Hamagee sae faman tsokana sukeyi kamar yadda suka saba.Yadda both A,B and C class members suka had'u ya ban sha'awa."Easha bebe kuyi mana sauri mana",inji Sumayya dake ta fantamawa,sunzo screening neh a makarantar,na qare musu kallo nace "kaji *University gurls* set of 2021 insha Allahu rabbi,saedae har yau basu bar halin nan nasu ba wanda yake matuqar burgeni,yasa nake jin dama ace muna tare kaman daa,kamar mu koma aji shida mu cigaba da rayuwarmu yadda mukeyi",I miss dem wollah 😞😞..# I heart them all 😍❤🙌🏽.. °•° ************★************ °•° Wani napep d'in Sumy ta sake tsarewa inda suka shiga ba tareda wani tsayawa yin wani cikini ba.Suna isa sukaje gidan su yarinyar inda suka tambaya akace be bisu ba,godiya tayi sannan suka dawo gida da niyyar yin sallah da kuma bama yara abinci kafinnan tasan nayi. *Abunda ya faru shine* Around 11:30am hakannan,Rayyan ya shiga ATBU,gidan wani abokin shi yaje suka tattauna kan wasu issues nasu,bayan sun gama kuma lokacin tashinsu Khaleel ya kusa,shine ya bi ya jira sanda aka tashe su saeya d'auko shi,ya biya dashi Jifatu store suka sayi icecream da popcorn tareda wasu chocolates sannan suka dawo office d'inshi,around 2:00pm dot ya tashi sannan suka koma gida. Ko kad'an Rayyan beyi tunanin sanarda Sumayya cewa ya d'auko Khaleel ba.Yanxu har qarfe uku saura amma shiru Sumayya bata dawo ba wanda hakan yasa ya fara tunanin koh tana neman Khaleel neh,waya ya d'aga zae kirata amma shiru wayan nata ringing ba'a d'aga ba. Dai-dai lokacin su Sumayya suka shigo wujiga-wujiga,duk a rud'e take.Khaleel neh yazo da gudu yana fad'in "oyoyo Mummy nah",yah rungumeta qam,itama rungumar shin tayi,yace "Daddy neh yaa daukoni ya sai mun chakulet kinga",yah nuna mata chocolates d'in hannunshi.Wani ajiyar zuciya Sumayya tayi tareda godewa Allah a zuciyarta,tace "that's good of you my child,amma mun damu dayawa da bamu ganka ba,but everything is now normal,muje koh",ta riqe hannunshi suka shiga..hghausanovelseries.blogspot.com

KAMU SEDANG MEMBACA
MAHAQURCI
Fiksi RemajaTabbas mahaqurci mawadaci neh,babban abinda littafin nan yake nuni dashi kenan,bayan wannan sai biyayya wa iyaye. Duk hukuncin da iyayenka/ki suka zantar akan ka/ki koda kana ganin baiyi maka ba to kayi haquri kayi musu biyayya,yin hakan zai sa ka s...