★ MAHAQURCI ★
By the Applomb writer:Hamagee
Wattpad @Hama_gee
Page 21
Rayyan yace "subhallah,haba Rayyana meyasa kke fad'in haka while deep in your heart kin san ba hakan bane",Rayyana tace "toh miye inba hakan ba?",Rayyan yace "shine nakeso ki nutsu ki saurari abunda zan fad'a miki,kinga in muka daure muka fahimci juna zamu bama marad'a kunya",Rayyana tace "ba wani maganar fahimta anan tunda ka shigo mun da wata a matsayin matarka cikin gidannan",Rayyan da kanshi ya mugun d'aukan charge yace "ohh my goodness,for Godsake ki zauna ki saurareni mana",Rayyana na mugun son Rayyan shiyasa ma bata son b'acin ranshi koh kad'an,amma ya zamo mata dole ta qwaci yan'cinta agun shi,a cewarta kenan. Da qyar ta yadda ta zauna tana sauraron shi,Rayyan ya fara dacewa "daga farko ina mai baki haquri kan abunda ya faru dukda cewa ba laifi nah bane",Rayyana bata mishi qala ba saema tab'e bakinta da tayi,Rayyan koh bai damu ba ya cigaba "sannan ina so kisa ma ranki cewa *komai rintsi* _ina tare dake_ kuma Sumayya doesn't mean anything to me,as for me,I'm having only one wife,only one!",Rayyana ta d'anji sanyi kad'an a ranta dan harda d'anyin murmushi,saedae batayi Rayyan ya gani ba. Ta fuske sannan tace "har yanzu baka gamsar dani cewa bakayi hakan da niyya ba",Rayyan yace "Uncle Umar neh ya kirani ranan har gidanshi ya zazzagen akan ban kyauta ba abunda nayi kuma yace lallae saena dawo da Sumayya cikin gidana",haka Rayyan ya karanto mata duk abunda ya faru daga ranan da Uncle Umar ya kirashi har zuwa yau daya dawo da Sumayya,Rayyana ta d'anyi ajiyar zuciya,ta tausaya ma Rayyan irin ansa shi yyi abu dole bada sonshi ba. Haka Rayyan ya cigaba da bata haquri harta haqura dan tana mugun sonshi,kuma babban abunda yyi mata dad'i kuma ya dad'a tabbatar mata da cewa bbu kowa cikin zuciyar Rayyan sae ita shine alqawarin da Rayyan yyi mata na cewa bazae na kula Sumayya ba kuma bazae na shiga d'akinta ba,abun yyi mugun yima Rayyana dad'i. Anan suka sha soyayyarsu kafin suka koma d'aki sukayi bacci. ************************* Bayan Sumayya tayi ma yaranta abinci sunci saeta musu wanka ta shirya su,basu jima ba sukayi bacci,itama baccin tayi,lokacin goma ma batayi ba. *Washegari...* Da wuri Sumayya ta farka daga bacci,bayan tayi sallahn asuba bata wani koma ba,addu'oi da karatun al'qurani ta yi tayi har gari ya gama wayewa,lokacin around 6:30am neh,tashin su ta shiga yi d'aya bayan d'aya tana musu wanka dan already ruwan heatern toilet d'in yyi zafi,so bata needing sake d'aura ruwan wanka. Bayan nan saeta barsu su shirya taje had'a musu breakfast,bayan sun gama ita da kanta ta raka su har islamiyar,yaran kuwa sae murna sukeyi,bayan ta kaisu saeta musu bye-bye kafinnan ta juyo bayan ta musu kashedin karsu zauna wasa idan an tashi,suka ce mata bazasuyi ba. Sumayya na shigowa gidan saega Rayyana ta fito daga d'akin Rayyan daga ita sae y'ar qaramar rigar bacci bbu koh d'an zani balle mayafi,Sumayya dae batace da ita qala ba ta wuce abunta,wani irin tsaki Rayyana ta buga amma kamar da iska tayi dan Sumayya shigewarta d'aki tayi kamar bata san tana existing ba,hakan yyi mugun b'ata ma Rayyana rai kuwa dan a rayuwarta ta tsani shariya,ta fiso duk abunda ta bid'a toh ta sameshi yadda takeso. Koda Sumayya ta koma side d'inta kuwa bacci ta koma,saeda rana ta tashi ta gyara ko'ina tayi ma yaran girki sannan tayi wanka,bata damuda yima Rayyan girki ba tunda har yanzu be had'asu yyi magana kan yadda zasuna tafiyar da abubuwan su ba,be kuma dameta ba,dan ita a yanzu a shirye take da ta qwacenma kanta y'anci a wurin Rayyan.hghausanovelseries.blogspot.com
ВЫ ЧИТАЕТЕ
MAHAQURCI
Подростковая литератураTabbas mahaqurci mawadaci neh,babban abinda littafin nan yake nuni dashi kenan,bayan wannan sai biyayya wa iyaye. Duk hukuncin da iyayenka/ki suka zantar akan ka/ki koda kana ganin baiyi maka ba to kayi haquri kayi musu biyayya,yin hakan zai sa ka s...