★ MAHAQURCI ★
By the Applomb writer:Hamagee
Wattpad @Hama_gee
Page 19
A palour kuwa Abbaa,Ummee da kuma Uncle Umar neh zaune a kan kujera,while Rayyan da Sumayya a qasa suna sauraron fad'an da ake musu.Maganganu masu ratsa jiki suka dinga yi musu,daga bisani sukace Rayyan da Sumayya su tashi su tafi Allah yyi musu albarka,suka ansa sannan suka miqe,Rayyan ya fita Sumayya kuma d'aki ta koma. Sugrah ta gama waya kenan bata jimaba taji shigowar Sumayya,tashi tsaye tayi tana tambayarta "yah dae",Sumayya tace "yanzu zamu tafi wllh,nazo miki sallama neh",ta fad'a hakan neh kamar zatayi kuka,Sugrah tace "don't worry sis,everything shall come to an end insha Allah,just do as I told you earlier,everything will definately be alright",haka Sugrah tayi ta mata magana har Sumyn ta d'an samu nutsuwa da courage sannan Sugrah ta rakota waje. Saeda Sumayya tayi sallama dasu Ummee da Abbaa tukunna ta fita,inda Sugrah keh biye da ita tana mata maganganu masu dad'i,sae dariyarsu suke sha kai kace ba Sumy bace.Har mota Sugrah ta raka Sumayya inda tayi ta tsokanarsu wae ango yazo tafiya da amaryarshi,ita dae kar yyi mata gudu da yar'uwa dan tasan yanzu alla alla yake su isa,shi dae binta da dariyar yaqe kwae yakeyi har suka rabu,saeda suka fita daga gate d'in kafin Sugrah ta juya ta shiga gida cikeda missing nah Sumayya. A palour ta tararda su Ummee dan haka itama ta zauna suka cigaba da hirar tare har lokacin sallahn magrib kafinnan kowannen su ya tashi. •°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°• Bayan fitarsu Rayyan da Sumayya daga gidan,tafiya suke bbu me cewa wani ci kanka,tafiya kawae sukeyi.A haka har suka iso gidan,me gadi yah bud'e gate d'in suka shiga,Khairat da Khaleel na hango can cikin wani d'an field da aka gyara shi na wasan yaran,wasan su suke tayi. Da gudunsu suka qaraso wajen itayen nasu ganin motar Babansu neh,basu ma san harda maman ba,"oyoyo Daddy",inji Khaleel kenan,wani ihu Khairat tayi ganin Mommynsu ta fito daga motar "Mommmyyyyy!!",juyowa Khaleel yyi dan tabbatar da maganar da yaji a bakin yar'uwar shi,shima a guje yaje gunta yyi hugging nata cikin murna,can sama Sumayya ta d'aga Khaleel cikeda murna itama. Khausar nagani ta fito kamar daga bacci ta tashi,daga dukkanin alamu kuma hayaniyar da ake ceh ta d'aga ta.Wani tsalle ta daka itama da gudu tazo tayi hugging Sumayya tana murna,itama Sumyn murna takeyi,nan Rayyan ya tsaya suka cigaba da hidimar ganin yadda yaran suka sauya lokaci guda,lallae ya zamo dole ya ringa kwatanta kyautata ma Sumayya saboda yaran nan,dan yaga farin cikinsu kenan. Hotuna Rayyan ya shiga d'aukansu,yaran kuwa kamar zasu koma cikin maman,hakan ba qaramin dad'i yasa yaji ba. Rayyana ceh ta leqo ta windown palour tana leqen abunda yake faruwa,ganin familyn yasa ta cikin matsanancin damuwa qwarai,ashe dama akwae ranan da Rayyan zaeyi mata haka,shine zae dawo da matarshi koh fad'a mata baiyi ba,kuma ji yadda ya sake cikin iyalan shi suna having good moment,duk wayan'nan maganganun a zuci Rayyana keh yinsu. Wani irin b'acin raineh yazo mata,lallae ya zamo dole tayi wani abun cikin gaggawa,tama rasa yadda zatayi,can ta bar palourn ta koma d'aki dan ganinsu zai iya sa mata ciwon zuciya,Rayyana nada mugun kishi dan abunda yasa ma ta yadda ta auri Rayyan saboda ya tabbatar mata da cewa Sumayya bata gidan neh amma da bazata aureshi ba,(a raina nace,kishi yanzu kika fara jinshi,kuma nan gani nan bari d'umamen mayya 🙄🙄 ,Rayyan na Sumayya ceh ita kad'ae dukda cewa sunanku d'aya dashi amma Rayyan bai dace dake ba).. *Ina masoyan Sumayya* 🙌🏽 ,, *Ina kuma masoyan Rayyana*. 🙌🏽 *Ku cigaba bin Hamagee* 😍hghausanovelseries.blogspot.com
![](https://img.wattpad.com/cover/138596769-288-k251185.jpg)
أنت تقرأ
MAHAQURCI
أدب المراهقينTabbas mahaqurci mawadaci neh,babban abinda littafin nan yake nuni dashi kenan,bayan wannan sai biyayya wa iyaye. Duk hukuncin da iyayenka/ki suka zantar akan ka/ki koda kana ganin baiyi maka ba to kayi haquri kayi musu biyayya,yin hakan zai sa ka s...