★ MAHAQURCI ★
By the Applomb writer:Hamagee
Wattpad @Hama_gee
Page 8
Bayan Sugrah ta idda addu'anta saeta miqe ta cire himar d'in kanta ta nad'e sannan ta bi tsawon gado,bata jimaba itama tayi baccin.. Ummee na fitowa Abba ya shigo da sallamarshi ta ansa,kai tsaye dining area suka nufa inda Ummee tayi serving nashi before ta zuba nata.Bayan sun gama cin abincin sae Ummee ta tattare plates d'in da sauran kwanukan ta kai kitchen ta ajiye sannan ta dawo wajen Abba wanda harya koma palourn ya zauna.Ta d'au cup ta zubo mishi champayne ta kai mishi palourn,tana zuwa ta miqa mishi,saeda yyi mata murmushi sannan ya karb'a a ranshi yana jin dad'in irin nuna kulawa da Ummee keyi mishi tun suna saurayi da budurwa gashi har yanzu salon be canza ba,gaskiya Ummee matace wacce kowanne namiji zaeso ya mallaka.Bayan ta miqa mishi saeta nemi guri ta zauna,saeda ta jira yad'an sha kafinnan tace "Abban Sumayya!",Abba yace "naam Ummeen Sumayya",cikeda nuna kulawa a lokacin ya ajiye cup d'in hannunshi ya dawo da full concentration nashi gurinta,Ummee tace "d'azu bayan Sugrah taje gidan Sumayya suka zo mun da zance mara dad'inji",a qule Abba yace "meya faru?",nanada nan Ummee ta zayyano mishi duk abunda Sugrah tazo ta fad'a mata. Ae kuwa nanda nan ranshi ya b'aci yace "lallae Rayyan ya wuce iyaka kuma wllhi saena gwada mishi shayi ruwa neh sannan daga yau bashi bbu y'ata,ae ba wae bamu sonta ko kuma mungaji da ita bane da muka d'auketa muka damqa mishi,maciyi amana kwae",Ummee ko haquri tayi ta bashi dan tasan yadda ranshi ya b'acin nan komai zae iya aewatarwa.Yace taje ta kira mishi su dukansu,Ummee ta tashi taje d'akin Sugrah dan kirawosu,inda ta tarardasu duka suna bacci.Nan ta tashe su tace Abbansu na kiransu kafinnan ta fice ta koma palourn. Sumayya ceh ta fara miqewa ta shiga toilet ta wanko fuskarta sannan ta fita Sugrah ma ta shiga ta had'o da alwala dan la'asar ta danno kai.Bayan sun gama a tare suka fita zuwa palourn. Ummee kuwa bayan ta fita palour ta koma ta sanarda Abba cewa suna bacci amma ta tashesu suna zuwa,Abban yace ae da ta barsu ma tunda bacci suke. Da sallama suka shiga palourn bayan an ansa,suka nemi guri suka zuna inda Sumayya ta gaida Abba,ya ansa tareda tambayarta abunda ya faru,nan ta zayyano mishi komai harda na baya,Abba ya jinjina kai yace "lallae wannan yaro yyi amfani da haqurin ki da kuma biyayya neh yyi miki hakan,amma karki damu insha Allah zan qwatan miki yan'cin ki,zan bashi nanda 3days idan har bezo ko ya aiko ba toh lallae hukunda na yanke zan aiwatar wanda ni kad'ae na barma kaina sani",bayan ya gama yace dasu su tashi suje,sun tashi zasu tafi sae Ummee tace "kuzo kuci abincin ku mana",Sugrah tace "nikam saenayi la'asar Ummee",Sumayya ma tace "sae munyi sallahr zamuzo muci",Ummee tace "toh shikenan",suka koma d'akin. Abba da Ummee sun jima suna tattaunawa kan batun har aka kira sallahr la'asar kafinnan suka tashi,Abba yyi alwala ya tafi masallaci,Ummee kuma tayi alwala tayi sallahn ta. Haka nan Sugrah ma tayi sallahr la'asar kafinnan suka fito suka ci abincin,bayan sun gama sae Sugrah ta tattare komai ta gyara gurin sannan suka koma palourn Ummee inda suka tararda ita zaune tana kallon tv,da sallama suka shiga bayan ta ansa,tare sukayi ta kallonsu har Sumayya ta d'an ji sanyi a ranta.Bayan Abba ya dawo kuwa d'akinshi ya shiga.hghausanovelseries.blogspot.com
YOU ARE READING
MAHAQURCI
Teen FictionTabbas mahaqurci mawadaci neh,babban abinda littafin nan yake nuni dashi kenan,bayan wannan sai biyayya wa iyaye. Duk hukuncin da iyayenka/ki suka zantar akan ka/ki koda kana ganin baiyi maka ba to kayi haquri kayi musu biyayya,yin hakan zai sa ka s...