★ MAHAQURCI ★
By the Applomb writer:Hamagee
Wattpad @Hama_gee
Page 15
Kasa magana Rayyan yyi tsabagen yadda jikin shi yyi sanyi,amma a ranshi yana mamakin irin wannan abun,haqura yyi ya barta dan yyi yyi da ita taqi ta biye mishi.Hakan yasa ya fara shakku a kan sonda Rayyana take mishi koh na qarya neh dama.Amma daga baya saeya bata uzirin maybe gajiyar bikin ceh tasata yin hakan,shiyasa kwae ya rabuda ita yyi baccinsa. Rayyana kuwa kasa baccin tayi tana tunanin shi,da har zata koma kusada shi ta nuna mishi irin sonda take mishi amma kash,maganar qawarta Zulaiha ta tuno,na cewa karta yadda Rayyan ya kusanceta dan tabbas zae gane she isn't a virgin. Wannan dalilin yasa bata son Rayyan ya kusance ta har sae ta gama maganin da takeyi,wanda take ganin yin hakan zae iya dawo mata da martabarta ta y'a mace agun mijinta duk lokacin da ya kwanta da ita..(tirqashi,Allah yah kyauta). Da qyar ta samu tayi bacci saboda irin tunanin shi da take. Washegari da asuba Rayyan ya tashi yyi alwala sannan yazo ya tashi Rayyana kafin nan ya wuce masallaci.Bayan ya dawo saeya wuce d'akin yara ya tashe su dan yau akwae makarantar islamiya kuma already 6:30 neh yanzu,saeda ya tabbatar Khausar ta tashi kafin ya bar d'akin. Koda Rayyan ya shiga d'akin,a kwance ya tadda Rayyana inda ya barta,ya sake tashinta a karo na biyu amma ina,bata da niyyar tashi.Daya gaji da tashin nata sai ya barta tunda ita ba qaramar yarinya bace.. Fita yyi daga d'akin ya nufa na yara dan yasan Rayyana ba tashi zatayi yanzu ba,ko ta tashi mah ba shirya su zatayi ba daga dukkan alamu.Yana shiga ya samu Khausar na kan shirya Khaleel,fita yyi yaje ya had'o musu tea sannan ya kawo sukayi breakfast sannan ya kaisu makarantar dukda cewa bata da nisa. Bayan ya dawo around 8:05am sae a lokacin Rayyana ta tashi,batama yi sallahn ba tukun.Kallo kwai Rayyan ya bitada shi bece mata komai ba. Haka rayuwa ta cigaba da kasance ma Rayyan,kullum baida nutsuwa a cikin gidan shi,saidai har yau yaqi amincewa kan Rayyana bata son shi. Yau ya kasance ranar Juma'a,so da wuri Rayyan ya baro office,saeda ya d'auko yara daga makaranta sannan suka dawo.Indomie ya dafa musu sannan ya kawo suka ci tare dan yasan Rayyana batayi girki dasu ba,dama kuma ta fad'a mishi cewa bazata yi rainon kowane d'a ba.Bayan sun gama can sae bacci yyi gaba dasu,d'aya bayan d'aya ya d'aukesu ya kai d'aki ya kwantar sannan ya wuce d'akinshi dan shima baccin ya fara ji. ……………………………………………… Rayyana na gano zaune a gefen gadonta tana qoqarin sa wani d'ankunne,ta fito daga wanka kenan take shiryawa,ta sama ranta yau matsalarta da Rayyan zata qare har abada dan yau ta gama duk maganin da takeyi,kuma a yanzu jinta take kamar budurwa.Bayan ta gama shafe-shafen tasa room slippers nata sannan ta d'au wayarta sae d'akin Rayyan dan tajii shigowar shi dazu. Rayyan harya fara bacci yaji an bud'e qofar shi,bace komai ba kuma be juyo dan ganin meh bud'ewan ba dan yasan ba kowa bane illa Rayyana,ya d'au niyyar bazae sake wata mu'amula da ita ba har sae ta kawo kanta da kanta. Tana shigowa ta maida qofar ta rufe sannan tazo a hankali ta hau kan gadon kamar meh shirin kama fara,ita duk a zatonta Rayyan bacci yake yi,a bayan shi ta kwanta tana mishi rad'a a kunne.hghausanovelseries.blogspot.com
YOU ARE READING
MAHAQURCI
Teen FictionTabbas mahaqurci mawadaci neh,babban abinda littafin nan yake nuni dashi kenan,bayan wannan sai biyayya wa iyaye. Duk hukuncin da iyayenka/ki suka zantar akan ka/ki koda kana ganin baiyi maka ba to kayi haquri kayi musu biyayya,yin hakan zai sa ka s...