★ MAHAQURCI ★
By the Applomb writer:Hamagee
Wattpad @Hama_gee
Page 3
Around 9am Sugrah ta tashi a bacci,toilet ta shiga tayi wanka tayi brush saeta fito tasa kaya,fitowa tayi ta nufa d'akin Ummee ta sameta a kwance,tayi sallama Ummee ta ansa sannan ta qarasa ta gaisheta,bayan sun gaisa sae Ummee tace mata taje tayi breakfast nata na kan dinng,Sugrah ta ansa da "toh,nagode"sannan ta miqe ta nufi palourn. Tana fitowa lokacin Abba ya fito zae tafi office,ta gaisheshi ya ansa sannan ya nufa d'akin Ummee yyi mata sallama dan su hakan na cikin tsarin gidansu duk wanda zae fita sai yyi sallama ma mutnen gidan,bayan sunyi sallaman ya fito zae tafi,Sugrah tayi mishi a dawo lfya,ya ansa kafin ya fita,tea d'inta ta had'a ta soma breakfast abunta. Bayan ta gama ta gyara palourn da ko'ina sannan ta fara shirin abincin rana,ba bun ta fad'a cewa zasuyi baqi ba tana tsoron bunda zae je ya dawo dan haka bata ma fara maganar ba,bayan ta kmmala abincin ta gyara kitchen d'in saeta koma d'akinta ta d'au wayanta ta som game,lokacin 12pm neh,dan haka ta shiga toilet tayi alwala kafin lokcin sallah ya qarasa,bayan kamar 10mins hka aka fara kiran sallah dan hka ta jira sae 12:00pm kafin nan tayi sallahr ta. Bayan ta idar da sallahn ta d'an kwanta,can around 2:00pm Abba ya dawo,Sugrah harta fara bacci ta tashi,taje tayi mishi sannu da dawowa,bayan Abba da Ummee sun fito sae suka zauna dukansu sukayi lunch d'in tare,gaskiya familyn su abun sha'awa neh komi nasu daban dana sauran gidaje,bayan sun kammala Sugrah ta kwashe plates d'in taje ta wankesu sannan ta gyara wajen ta koma d'aki ta d'an kwanta. Sagir neh ya kirata ya sanarda ita cewa da yamma su Babanshi zasu zo,tace "Allah ya kaimu",yace "ameen",bayan sun d'anyi tad'i sae yyi hanging up,a lokcin Sugrah ta samu ta d'anyi bacci. [2:24am, 12/14/2016] Hamagee馃尫: Around 4:00pm Abba ya dawo daga masallaci,be jima ba akayi mishi sallama wae yyi baqi,yace a shigo dasu,bayan sun shigo Abba ya fito suka gaisa dukda be ganesu ba saeya yima Ummee magana,Ummee ta fito suka gaisa sae ta kawo musu drinks da cups,sae bayan sunsha Abba yake tambayar daga ina dan be waye su ba. Sugrah ta idar da sallahn la'asar kenan taji hayaniya kamar anyi baqi,sarai tasan su Baban Sagir neh shiyasa bata ko yi attempting fita ba,tana ji megadi yyi ma Abba sallama har ya fito suka gaisa,cikinta neh ya soma qara data ji tambayar da Abba yyi musu.. A take Baban Sagir ya sanarda Abba dalilin zuwansu,na sunzo nemarwa dansu auren y'arsa,Abba yyi gyaran murya kafin yyi musu bayani cewa suyi haquri ba yanxu zae aurar da y'arsa ba tukun,sae nan da zuwa wani lokacin da ya tanadar mata.Bayani me gamsarwa yyi musu dan haka sun fahimce shi sosae kuma basu nuna damuwarsu ta qin amincewar su ba,bayan sun gama sae sukayi sallama ya raka su. Hawaye neh suka soma zuba daga idon Sugrah,taji tukkanin maganganun da sukayi,yanxu kam ta tabbatar da cewa Abbanta da gaske yake karatu yake so tayi ba aure ba dan haka ya zamo mata dole ta cire maganar aure a ranta,idan ta tuno da Sagir sae kukan da take ya qaru,can taji Abba ya dawo daga rakiyar da yyi musu yana kiranta "Sugrah! Sugrah!"da sauri ta share hawayen fuskanta sannan ta ansa "naaam Abba"hghausanovelseries.blogspot.com

VOCÊ ESTÁ LENDO
MAHAQURCI
Ficção AdolescenteTabbas mahaqurci mawadaci neh,babban abinda littafin nan yake nuni dashi kenan,bayan wannan sai biyayya wa iyaye. Duk hukuncin da iyayenka/ki suka zantar akan ka/ki koda kana ganin baiyi maka ba to kayi haquri kayi musu biyayya,yin hakan zai sa ka s...