Page 27

913 59 0
                                    

           ★ MAHAQURCI ★

By the Applomb writer:Hamagee

     Wattpad @Hama_gee

Page 27
    Wani irin farin ciki Rayyan yaji marar misaltuwa,nan yayi hugging nata so tight shima suna kukan tare.Sun jima sunayi daga bisani sukayi shiru sannan suka cigaba da maganganun su cikeda nuna kulawa da qauna,bayannan kitchen d'in suka koma tare sukayi komai,bayan sun gama girkin sunyi setting table sae Sumayya ta shiga wanka shi kuma ya tafi d'auko yara daga makaranta dan already qarfe d'aya tayi.Daga Sumayya har Rayyan duk yau cikin farin ciki suke. Bayan ya d'auko yaran sae suka dawo gida,lokacin Sumayya tayi wanka harta shirya,suka gaisheta ita kuma tayi musu sannu da dawowa,bayan sunyi sallah yaran kuma sun canza kayan jikin su sae sukayi lunch d'in tare,bayannan kuma sae sukayi wanka sukayi shirin islamia,bayan sunyi sallahn la'asar sae Rayyan ya kaisu ya dawo.Sabon amarci suka bud'e yau. ¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶ *After two weeks....* Yau ya kasance ranar Monday kuma yau Sumayya zata fara attending school,dan haka da wuri suka shirya Rayyan ya sauqesu dake duk makarantar d'aya ceh,saedae bayan sunje sae aka fad'a mata cewa *Gubi* zata wato d'ayan *University Campus* kenan.Haka Rayyan ya kai Sumayya har can dan a cewarshi matarshi bazata hau school bus koh motar haya ba tunda Allah ya hore mishi abun hawa. Haka bayan ta gama,shiya d'aukota,washegari ma haka.Haka rayuwarsu ta cigaba da kasancewa,kowa na faranta ran d'an uwanshi,kuma kowa yana iya bakin qoqarinshi wajen ganin baiyi wani abunda zai b'ata ma d'an uwanshi rai.Yaransu kuwa suna samun kulawa da tarbiyya yadda ya kamata,gasuda girmama juna dana gaba dasu,suna yawan ziyartar gidansu Sumayya yanzu,wataran kuma gidansu Rayyan,idan sunje kuma sae sun wuni baban yake zuwa ya d'auke su idan dare yyi irin bayan isha d'innan.A halin yanzu kuwa Sumayya ta fara koyon mota dan Rayyan yace idan ta gama iyawa a nashi saeya sai mata wata dan zuwa hidindimun ta na yau da kullum.. ★★★★★★★★★★★★★★★ *4years later...* Sugrah na gano cikin mota itada Sumayya,fitowarsu kenan daga ATBU daga gani gida zasu,kayan youth service keh jikin Sugrah,wato (NYSC),ta kammala degree d'inta yanzu sun fara serving,wata mota ceh keh ta binsu,Sugrah tace ma Sumayya "dan Allah adda Sumy muyi sauri,wllh mutumin d'azun nan keta binmu,kamar wani maye",saeta d'an jaa wani gajeren tsaki,Sumayya koh dariya tayi ta mata tace "kka sani koh shine mijinki? Ana gudun masoyineh",Sugrah tace "haba Adda Sumy,sekace baki san alqawarinmu da Sagir d'ina ba,karki manta saboda ni ya bar qasarnan yaje can danyin karatu koh zai samu muyi aure,yanzu next week d'innan ma fa insha Allahu zai dawo" Sumayya tace "hakane kam amma kin san ance matar mutum kabarinsa koh,so a cikinsu duk wanda Allah yasa shine mijinki bbu yadda zakiyi inba aurenshi ba,dan Allah bbu ruwanshi da wancen ya tafi wata qasar saboda aurenki,koda wata duniyar yaje kan qarewa in dae ba rabonshi bace keh toh ba zae aura ba".Sugrah tace "hakane,amma ae ya kamata mutum ya yi qoqarin sakawa wanda ya mishi alkhairi da alkhairi koh",Sumayya tace "sosae mah,keh dae Allah ya zab'a miki wanda yafi zama alkhairi acikinsu",Sugrah tace "ameen". A daedae lokacin suka iso gidan,Sumayya tace "dama kinzo mun wuce gidana neh kwae",Sugrah tace "eh toh! Amma mu shiga tukunna saena fad'a ma Ummee",Sumayya tace "toh muje",suka fito daga motar suka shiga,megadi na musu sannu da dawowa. Bayan sun gaisa sae Sugrah ta fad'a ma Ummee cewa zata gidan Sumayya gobe zata dawo,Ummee tace "Allah ya kaimu goben", sukace "ameen".Daga nan Sugrah ta d'au chargern ta kafin su tafi dan already akwae kayanta a gidan Sumayya,anytime tana zuwa tayi kwanaki.Bayan sunyi sallama ma Ummee sae suka wuce.


    hghausanovelseries.blogspot.com

MAHAQURCIWhere stories live. Discover now