★ MAHAQURCI ★
By the Applomb writer:Hamagee
Wattpad @Hama_gee
Page 26
Washegari da safe bayan Rayyan ya dawo daga masallaci kamar zae tashi Rayyana amma saeya fasa,d'akinshi ya wuce ya barta a gun.Ta kai 6:30am kafin ta tashi,ganinta a wajen yasa ta tuno da abunda ya faru jiya,tashi tayi ta shiga d'akinta,ta hau tattara kayanta tana share qwalla kamar mutuniyar kirki.Haka ta kwashi kayanta ta bar gidan cikeda nadamar abunda ya faru jiya. Sumayya kuwa tana tashi ta shirya yara bayan tayi sallah,tayi musu breakfast sukaci sannan Rayyan ya kaisu makarantar.Anan ta samu tayi y'an gyare gyarenta,inda ta saka turaren wuta bayan ta gama,gidan sae qamshi yake da d'iban ido,dama wannan main palourn ya jima baiga shara tunda aka kawo Rayyana be wuce sau uku tayi mishi sharar tsakani da Allah ba,yawanci saedae ta tsince dattin da hannunta shikenan,Sumayya kuwa batayi neh saboda bata ma zama a wajen,dan palourn na mazaunin kaman na me gida neh,so kuma kullum Rayyan na tare da Rayyana ko a palourn ko kuma a d'akinshi ko nata side d'in.Wannan kenan... Ta d'aura abincin rana kenan taji bud'e gate,alamar Rayyan ya dawo kenan,amma meh yah dawoda shi yanzu? Sumayya ceh tayi ma kanta tambayar da ita kanta batada amsarshi,tana jin shigowarshi. Side d'inta ya nufa shi kuma kai tsaye,yana shiga yaga bata palourn dan haka kai tsaye ya wuce d'akinta,Sumayya kuwa tana kitchen tana jinshi amma tayi kamar bata jiba.Koda ya shiga d'akin bata nan saeya leqa toilet,still be ganta ba. Fitowa yyi palourn,sae lokacin ya tuna be duba kitchen ba dan haka kai tsaye ya shiga qofar kitchen d'in.Yana shiga ya ganta tsaye a gaban sink tana wanke kayan miya tana zubawa cikin blender.Sunanta ya kira inda ta ansa batareda barin abunda takeyi koh juyowa ba,yasan bata da niyyar sauraronshi dan haka ya qarasa inda take wanke kayan miyan,ya rufe tap d'in tareda kashe cookern sannan yajaa hannunta yana fad'in "muje ki sauraren na small minutes please",batareda Sumy tace komai ba tabi shi hannunta cikin nashi har zuwa palour. Ya zaunarda ita shima ya zauna sannan ya dubeta yace "daga farko ina so inba ki haquri kan duk wani abunda ya faru a baya,bazance Rayyana bace ta janyo komai saboda nima da nawa kamishon,dan haka nake neman alfarma da ki yafe mun,mu bar duk wani abunda ya wuce ya zamanto tarihi,mu gina sabon rayuwa muda yaranmu koh dan samun farin cikinsu,wllh ina sonki Sumayya ki yarda dani",ya wani marairaice yana mata magana. Sumayya dae batace komai ba har yanzu saedae deep inside her mind tanada yaqinin abunda yake fad'in gaskiya neh,dan tana kallon tsantsan nadama daga idonshi,yaci gaba "koh baki ji bane wife? Dan Allah ki daena tunnin komai ki yarda da abunda nake fad'a miki wllhi nayi nadama kuma insha Allah makamancin hakan bazae sake faruwa ba kinji?",Sumayya ta dube shi sannan tace "naji,Allah yah yafe mana baki d'aya". Rayyan yace "ameen...but uptill now bakice dani komai ba,ko bazaki iya yafe mun bane?",Sumayya taji tausayin shi sosae ganin yadda yake bata haquri kamar qaramin yaro,kuma zancen gaskiya tasan cewa da gaske Rayyan yake bata haqurinnan dan ta gani a idonshi,ya katse mata tunanin da saukowa qasa ya tsuguna akan gwiwanshi yana fad'in "will you please forgive my sins,na tuba",Sumayya ma qasan ta koma tana fad'in "it's ohk please,my husband doesn't has to do all of this just to sake for my forgiveness,na yafe maka Rayyan har a bada...I love you much".Hugging nashi tayi tana kuka..hghausanovelseries.blogspot.com

VOUS LISEZ
MAHAQURCI
Roman pour AdolescentsTabbas mahaqurci mawadaci neh,babban abinda littafin nan yake nuni dashi kenan,bayan wannan sai biyayya wa iyaye. Duk hukuncin da iyayenka/ki suka zantar akan ka/ki koda kana ganin baiyi maka ba to kayi haquri kayi musu biyayya,yin hakan zai sa ka s...