Page 17

861 56 0
                                    

           ★ MAHAQURCI ★

By the Applomb writer:Hamagee

     Wattpad @Hama_gee

Page 17
    Ummee ta fito daga wanka kenan lokacin da Sugrah ta shiga,ta fad'a mata cewa Abbansu na kiranta,Ummee tace "lfya dae koh,naga be shigoba kuma yana kirana",Sugrah tace "nima dae ban sani ba kam amma kamar akwae abunda ya faru",Ummee tace "toh Allah ya tabbatar da alkhairi",Sugrah tace "ameen",sannan ta fita ta koma palourn,tana shiga ta nemi guri ta zauna sannan ta fad'a ma Abbaa cewa Ummeen tana zuwa,Abbaa yace "ohk",duk tasu zaman jiran Ummee suke. Kowa da tunaninda yakeyi,Abbaa yana jiran fitowar Ummee samun ya fad'a musu abunda yake shirin fad'a,Sugrah da Sumayya kuma na tunanin dalilinda yasa Abba ya tara su a wajen.Kome zaice musu?? Ohoooo fah Bayan kamar 5mins da fitowar Sugrah,Ummee ta fito sanye da himar alamun bata gama shiryawa ba,ta nemi gu ta zauna tareda yima Abbaa sannu da dawowa,Abbaa ya ansa tareda cewa "kema sannu da gida",Ummee ta d'anyi dariya sannan tace "yauwa".Abbaa neh ya fara magana "ba wani abu bane dalilin da yasa na tara ku a nan illa in shaida muku cewa gobe insha Allahu Rayyan na zuwa zae tafi da Sumayya,so ki shirya kayanki",kamar an zaburi Ummee tace "haba Abban Sumayya,kai da bakinka kke fad'in wannan maganar?",Abbaa yace "kin san dae ba zanso abunda zae cutarda yarannan bako?",Ummee ta d'aga kai kwae ba tareda tace wani abu ba. Abbaa yace "toh karki damu kanki,anjima zamuyi maganar.Yanzu muje muci abinci tukun",Ummee tace "toh shikenan",amma a ranta bataji dad'i ba,dan a ganinta be kamata ace Sumayya ta koma gidan Rayyan ba koma miye ya faru.Tashi sukayi dukansu jiki bbu qarfi suka nufi wajen cin abincin. Bayan sun kammala sae suka koma d'aki,hankalin Sumayya duk yabi ya tashi,a kanme Abbaa zaice ta koma bayan yasan duk wahalarda take sha sannan kuma karatun da take shirin cigaba dayi fah.Sugrah tayi ta bata baki kan tayi haquri bata san meh Abbaa yah hango mata ba.Har saeda Sumayya ta d'an samu sauqi kafin Sugrah ta qyaleta,bacci sukayi dukansu. Da daddare ana zaune a palour Abbaa yyi gyaran murya sannan yace "Sumayya!",Sumayya ta d'ago ta kalleshi sannan tace "naam Abbaa",Abbaa yaci gaba "nasan zakiyi ta tunanin dalilinda yasa nace ki koma gidan mijinki,toh ina son kisan cewa banyi hakan dan wani abu ba illa da hangen yadda rayuwarki zata kasance nan gaba.D'azu qanin Baban shi yazo ya sameni a office,yake cemun wae Rayyan neh ya same shi ya roqeshi kan yazo ya samen ya bani haquri ki koma dan bazae iya zuwa da kanshi ba saboda nauyin bunda yyi,maganganu yyi ta mun masu ma'ana wanda shiyasa na amince da uzirinsa ma,daga nan nace ya kira shi Rayyan d'in yace mishi yazo ya samemu". Sumayya ceh ta d'anyi tari,wanda hakan yasa Abbaa dakatawa kad'an tareda yi mata sannu kafinnan ya cigaba "bayan ya kirashi be jimba ya iso,bayan mun gaisa sae yake dad'a ban haquri kan abunda ya faru sannan ni kuma nace mishi na amince zaki koma amma bisa wasu sharud'ai,yace mun ya amince.Nan na gidaya mishi sharud'ai guda biyu tak amma duk ciki bbu wanda zan ragar mishi idan ya sab'a yin su,yace ya yarda.Na farko nace zakiyi Waec da Jamb this year tunda har kinyi registering,kuma immediately admission na fitowa in kka samu zaki koma scul,sannan na biyu idan na sake jin yyi miki wani muzanci toh lallae zai fuskanci fushina,sannan kuma kema ban yadda ki bijire umarnin mijinki ba,infact idan yazo gobe dole mu had'aku duka muyi muku nasiha".

    hghausanovelseries.blogspot.com

MAHAQURCIWhere stories live. Discover now