Page 25

965 65 0
                                    

           ★ MAHAQURCI ★

By the Applomb writer:Hamagee

     Wattpad @Hama_gee

Page 25
    Qarasowa palourn Rayyana tayi cikeda nuna isa da gadara ta kashe socket d'in tv,ran Sumayya yyi mugun b'aci yanzu kam,tashi tayi tana magana "keh wace irin y'ar tasha ceh kam? Kwata-kwata bbu alamun tarbiyya a tattare dake",Rayyana kuwa daman jira take Sumayya ta tanka mata dan haka tayo kanta kamar kura tana fad'in "yau koh zaki ga aikin y'an tasha",Rayyana na isowa wajen Sumayya ta dakatar da ita da hannunta tana fad'in "dakata malama,ban san cewa jakantar har ta kai haka ba ae,yanzun dambe kke shirin yi dani koh meh?" Hannu rayyana ta kai zata mari Sumayya inda tsawan da Rayyan ya daka mata yasa ta nutsuwa,"bakida hankali neh? Sa'ar kice ita?koh kuma tvn nakine? Iyeee?!",inji Rayyan d'in,kanshi tayo tana fad'in "ohk yanzu nuna mun kkeyi cewa matarka ta fini matsayi a cikin gidanka koh? Kuma kasan meh ta fad'amun neh?",a fusace Rayyan yace "kema ae kka ceh matata,sannan ban damu da sanin abinda tace miki ba dan koma miye keh kja janyo dan ba shiga harqarki take ba",ranta yyi mugun b'aci,wae ace a gaban wannan abun yake ci mata mutunci instead of yabi bayanta,ta dube shi tace "lallae Rayyan kai butulu neh,bakada mutunci koh kad'an kuma bakada adalci,inba haka ba daga fitowarka baka san meya faru ba kawae kabi bayanta" Rayyan yace "sae yanzu kka san cewa banida adalci?",a fusace tace "eh,gashi ka gwada mun akan wannan karuwar",hannu Rayyan ya watsa mata a kunci badan yaso ba saedan zuciyar data d'ebe shi wae dan ta kira Sumayya karuwa. Rayyana ta d'ago tana kallon cikin idon shi cikeda takaici ta shaqo wuyan rigarshi tana fad'in "toh idan ka cika d'an halak,a yau inaso in san matsayi na da nata a wajenka dan haka ka sallamen ko ka sallameta",wurgi da ita Rayyan yyi yana fad'in "yau na dad'a tabbatar da rashin tarbiyyarki a fili,kin manta cewa zaman haquri nake dake? Koh kin d'auka ban san halinki bane? Dan na rufa miki asiri ina zaune dake batare da nuna qyama ba koh? Toh a yau ni Rayyan Salis na fito qarara na nuna miki Sumayya tafi ki komai a wajena dan haka kije na sakeki saki d'aya,buyi,uku",wani irin uhu Rayyana ta kurma,Sumayya kuwa da tunda suka fara abunsu bata ceh komai ba ta tattari i nata i nata tabar musu palourn. Rayyana cikin kuka take fad'in "ni zakayi wa wulaqanci Rayyan?",Rayyan bece mata komai ba sae tsakin daya jaa ya bar palourn shima,Rayyana kuwa kuka tayi ta sha ita kad'ae,tareda nadamar yin hakan,a ranta kuma tana ta mamakin yadda akayi Rayyan ya gane cewa she isn't a virgin,after all abubuwan da tayi tayi,kuma meyasa ya haqura be fad'a mata ba sae yanzu,lallae yanzu kam ta yarda Komai daren dad'ewa akwae ranar qin dillanci,abunda take gudu yau ya faru.Ta jima tana tararradin irin wannan gorin daga gurin Rayyan gashi yau taja ma kanta harda saki uku a take. Nadama bbu irin wacce batayi ba yau,gashi saki uku yyi mata bbu damar ta roqeshe koda iyayen su neh ma bbu yadda suka iya,tayi kuka kamar ranta zae fita,gashi ba kad'an ba tana son Rayyan,barinma data aure shi ta qara sanin daraja da muhimmancin shi,yanzu a dare d'aya ta rasa shi har a bada in bawae wani auren zatayi ta fito ba,kuma tasan ko tayi hakan ba dawo da ita zaiyi ba.Tsantsar tsanar Sumayya take ji yanzu,a haka tayi bacci ranan. Sumayya kuwa data shigo d'akinta fitsari tayi tazo tayi addua sannan ta kwanta,a ranta mamakin abunda Rayyan yyi take,lallae yanzu tasan cewa ya dawo hanya,a haka har bacci yyi gaba da ita.

   hghausanovelseries.blogspot.com

MAHAQURCIDonde viven las historias. Descúbrelo ahora