Page 28

921 54 0
                                    

           ★ MAHAQURCI ★

By the Applomb writer:Hamagee

     Wattpad @Hama_gee

Page 28
    Bayan sun bar gida kai tsaye gidan Sumayya suka nufa,suna shiga yaran suka taso da gudu suna yi musu oyoyo,musamman ma Sugrah,yaran na sonta sosae,yanzu kowannensu yyi wayo dan Khaleel harda y'ar qanwarshi meh suna Khazanah,shekarunta 4 yanzu ya bata 4 yrs kenan dan yanzu he's 8yrs old,Khairat kuma 10,sae babbar sis 13yrs old yanzu tana Jss2 a International,Khairat kuma na primary 6,sae Khaleel a pri4,Khazana kuwa yanzu pri2 take,yanzun suna hutu neh shiyasa basuje school ba yau. Bayan sun nutsu guri guda sae Khausar taje kitchen inda ta d'auko musu abinci ta kai kan table,Sugrah tace "lallae y'ar tawa ta kusa kaiwa na aure har girki kke yi?",cikeda jin kunyar maganar Khausar tace "nikam aunty ban wani iya girki ba kwae naga Mommy bata nan neh shiyasa",Sugrah tace "toh Allah yasa yyi dad'i",ta fad'a neh cikeda zolaya,Khausar taje ta qarasa setting table d'in.Ana cikin haka saiga Rayyan ya dawo,Khaleel da Khazana neh suka fita a guje suna fad'in "oyoyo daddy!!oyoyo daddy",Khazana koh cewa tayi "ai ba daddynka bane daddy nane ni kad'ae",cikeda yarinta tayi maganar,Khaleel kuma abunka da shima ba wani wayon saeya ce "wallah qaryarki yarinya,daddy nane nima",fad'a suka cigaba yana fad'i tana fad'i har daddyn da aka jeh yima oyoyo ya shigo yyi parking harya fito daga motar ya nufo inda suke amma fad'a suke kamar ya'ya'n kishiyoyi 😂.. "Haba Abbana wannan ba qanwarka bace kke sa'insa da ita",Khaleel yaje yayi hugging Rayyan da gudu yana fad'in "ae ban san ka iso bane Daddy,wae ce mun fa tayi kai ba daddy na bane",yah qarasa maganar cikeda hali irinta yarinta,Khazana ma da gudun tazo tana fad'in "ka sake mun daddy nah nikaaam",kamar zatayi kuka,Rayyan yah tsuguna a wajen ya janyo su dukansu jikinshi yana fad'in "kunga bana son rigima,daddynku neh ni duka kunji? So banda fad'a dan nazo da chocolates kuma bazan bama me fad'a ba",nan da nan Khazana ta sauko dan tana mugun son chocolate tace "wollaah daddy na bari,kuma ai nace na sanma shi kai d'in koh",wata irin dariya ta bama Rayyan wae ta sanmashi ni,toh ana sanmar da ubane?,a ranshi yyi maganar.Yace "toh shikenan mu shiga ciki sae munci abinci zan baku koh",bbu musu suka shiga yana riqe da hannun kowannensu abun sha'awa. Suna shiga kuwa saiga su Khairat ma sukayi mishi oyoyon kamar wani yyi tafiya meh nisa yah dawo.Sumayya da Sugrah sukayi mishi sannu da dawo wa,Sumayya ta karb'i jakar labtop dake hannunshi ta kai mishi d'akinshi,dawowa tayi suka had'u gaba d'ayansu sukayi having lunch,abun ya mugun bada colour. **************************** Around qarfe hud'u na yamma megadi yah zo yyi sallama,Khausar ceh taje duba waye dan lokacin bbu kowa a main palourn,Sumayya da Rayyan na side d'in Rayyan sukuma da Sugrah suna palourn Sumayya suna kallo,koda ta bud'e saeta gaidashi yah answer sannan yace wae sallama ake da Sugrah,tace toh bari ta fad'a mata sannan ta nufa palourn da suke kallo earlier. Koda Khausar ta sanarda Sugrah cewa ana nemanta,Sugrah taji mamaki sosae dan a iya tunaninta batada wanda zaizo gunta at this time infact batada saurayi inba Sagir ba,wato fiance dinta.Miqewa tayi taje d'aki ta d'auko hijabi sannan ta fito taceda yaran idan mommyn su ta fito suceh mata ta d'an fita waje yanzu zata dawo,sukace toh sannan ta fita,fitarta keda wuya,saetaga wannan mutumin d'azun neh,mamaki neh ya isheta kafin ta qarasa gurin..


     hghausanovelseries.blogspot.com

MAHAQURCIWhere stories live. Discover now