5

997 54 0
                                    

💥AHALAM💥
(Love story)
written by khairat up

          5

jim kadan aliyu ya shigo dakin gani AA

kasan me ahalam ta min? aa sai ka fada ci abincin nan kaji

loma daya yayi ya zubar yana wuri2 da idanuwa wannan yarinyar bata da kirki sam2 mesa ta yi haka?

saboda na fasa wayan ta a lec hall kuma na koreta

aliyu ya dau abincin ya ce muje gun nata

falo suka sameta da wayan umma tana waya da abin kaunar ta ganin su tare kuma da kwanon abinci seda ta girgiza duniya tana shakkar ya ya aliyu.

yawu ta hadiya da kyar ta gyara zama cikin dakiya da dauriya

umma na aiki a laptop

keee! yadda yaja ke din ma se da hawaye ya taru a idanta dan fargaba.

a hankali ta kashe wayar ta mike ta tsuguna a gaban shi ya ja kujera a dining ya zauna ya nuna kan sa tace wana ne kai, gud wannan fa? ta yamutsa fuska tana muzurai da idanuwa taki amsawa

tsawa ya daka mata are u mad ina tambayan ki kin min shiru ya adnan ne

gud dauki abincin nan na baki gud 10 min ki cinye shi tas if not kin san sauran.

rau2 tayi da ido tace yaya ali ni na koshi ciki na a cike yake gwara ka doke ni

in dake ki? ai baki isa ba se kin cinye tas in ba haka ba kin gama zuwa makaranta

wal tayi da 👀 ta amma yaya ali kasan shi me ya min wani mari ya zuba mata ta saki ihu dan marin ya shige ta

umma sai lokacin ta tanka aliyu me ya faru me kuma tayi?

ummi dandana abincin nan dan allah

dandawarta keda wuya ta tofar aliyu are u mad yaza ta ci wannan abun me uban yaji da gishirhi

umma ai ita ta bata shi abincin AA saboda ya hukunta ta shi ne ta masa haka naga rashin kirkin ta kara gaba yake yi we need to stop her

hajjar Abbu haka ne?
   tana matsar kwalla tace yes umma

ok ya miki kyau
umma ki bashi hakuri bazan kara ba

no jiya ma kin yi zaki kuma

ahalam kar na kirga uku baki fara ci ba

umma pls
1,umma ki basu hakuri,2, ya samha ki masa magana,

jin zai fadi 3 sai ta sa hannu lomar farko ta ji wani irin azaba ta yaji ta kuma sakin kuka sai da taci rabi duk tayi kace2 da majina da kuka sai ga muryan abbu ina hajiya ta yau bata taroni ba?

da gudu ta je gun abbun ta saki kuka yaga duk ta lalace me ya faru?

abbu ya aliyu ne da ya adnan suka mare ni

what ! mari kuma me sa?

abbu karya take yi ahalam bata da kunya kasan me tayi?

tell me ina ji

fada masa komai yayi
ya juya kan ahalam yace haba hajja mesa kullum se ance kin yi rashin kunya? ai adnan wan ki ne kamar su abubakar and malamin ki ne tell him sorry yanxu

am sorry
ta wuce
shi kenan UMAR
naam abbu ka amso mata wata wayar gobe irin wadda take so and ahalam ki kula lokacin lec waya a jaka kar a kuma kawo karar ki ok?

insha allah

hararar shi tayi a fakaice!

ya gyada kai
basma dafa mun indomie pls.

daki ya koma ya kira jannat din shi suna soyewa abun su.

a daki kau ahalam ta sha sweet ba adadi a ranta tace am not done with u yet.

💥💥💥💥💥💥

washe gari kusan tare suka shiga hall din

tambayoyi ya dinga yi a kan abunda ya masu jiya sannan ya dora sabo cikin nutsuwa yake musu darasin har lokacin shi ya cika ya fita.
wasu yanmata a kusa da ahalam suka dinga santin shi

malamin nan ba karamin haduwa yayi ba ya iya daukan wanka ga zuba kamshi kamar mace ke magangn shi ma abun sauraro ne tafiyan shi kai gashi gentle and cool ina ma zai min kallo sau daya ni kuma ya min magana ai ina ganin na more

ahalam ta ce uhm shirme wannan mutumin ake ma wannan kodin mugu ne in baku sani ba ko me abun burgewa a nan oho?

tsaki tayi ta mike ta musu kallon baku da aikin yi ta wuce hade da daukan wayan ta wadda dazu ya umar ya bata

dayar tace wannan yarinyar akwai izza, da isa da raini ko wacce oho ke ita ce jiya sir adnan ya fasa wayarta yayi out da ita
tab ai ga wata wayar a hanunta kirar wacan wato har ta sake?

lalai  ni da nice ai kuka zan na yi kuma sena dade zan recovring din wata wayar

ke muje gsp kar mu rasa gu

aiko dai

💥💥💥💥💥💥

cikin wata arniyan gwon ta fito ja da mayafi black tana zuba sanyanyan kamshi takalmin ta da jakar ta black su aysha take jira su fito su tafi amma sun yi nauyi yau

baba ali ya parker a gaban ta budewa tayi ta shiga kawai tana dadana waya

ahmad ya kira ta ya  guess what?
what?

ina right behind ur car

ohh ahmad kar ka min wasa irin wannan bana so

wallahi am serious da gaske nake miki

fita tayi daga motan ta juya baya wani ihu ta saki hade da tsalle ta je gun shi da gudu

kamar ta rungume shi haka take ji

ahamad when...... just some minutes ago na kasa zuwa gida ma gun ki na fara zuwa my lady haka kike zuba ado

ahmad kai kadai ahalam ke yayi amma kafin nan muje gida

no anjima zan zo da magrib ki girka dani zan yi dinner a nan kin ji?

to nazo ne dan na ma kai na alkawarin ke zan fara gani sannan su mum

naji dadi to anjiman ina jiran ka

to bye shiga motan kallon da ake miki ya isa haka

wani dadi ta dinga ji da annuri burin ta kawai taje gida ta fara tsara me zata ma ahmad din ta

AHALAMWhere stories live. Discover now