10

815 43 0
                                    

💥AHALAM💥
love story
written by khairat up

           

ina neman afuwar ku bisa mistake din page na jiya maimakon na sa 9 na sa 8 ina me baku hakuri.

       10

kar ku fada ma abbu abinda yake faruwa dan Allah ko  umma ma ban san su sani

tabe baki yayyun nata suka yi ki fara shirin komawa makaranta jibi dan za a fara daunkan darasi zai ma dauke miki hankali daga wannan kadaicin zamu na biyo miki da driver.

murmushin jindadi tayi dan taji dadin zuwan yan'uwan ta sossai ko ba komai ta fada musu abunda ke damun ta taji zuciyan ta tayi mata dadi har waje ta raka su sannan ta koma gida.

hakan nan taji ta a cikin wani irin nishadi ta dau wayarta ta hau wattsap sede me wata num ce ta mata magana tana shiga ta fara tozali da hotunan ahmad da wasu yan'mata da ga pant sai bra sai wanda ma ba kaya idanun ta kawai ta runtse ta nemi hawaye ta rasa lallai kuka ma rahama ne kuma samun wuri ne. lallai namiji mugu ne,mayaudari ne,rigar qaya ne hakika ta tsani kalmar so, ta tsani kalmar kauna, duk yaudara ce ahmad ya zalunci zuciya ta ya cuce ni me nai masa da zai saka mun da haka? dama manemun mata ne? ba me bata wannan amsar.

sauka tayi ta na jin zuciyan ta na kuna wani abu na mata suya daki ta fada ta shiga bandaki ta sakar ma kanta shawer tana me jin wani sanyi a ranta a ranta ta furta ME MAFARIN LAMARIN?.

💥waiwaye adon tafiya!💥

''ALHAJI MUHAMAD UMAR KUMU cikakken dan garin gombe ne dan kasuwa ne na gaske yana da kamfanoni na sarrafa robobi da kayan gini da kuma kamfani na sarrafa fata sannan dan boko ne alh.muhmd irin dattijan nan ne da suka san zafin kudi da kuma yadda ake samun kudi bada wasa ba sai Allah yasa masa albarka a kasuwancin sa yana samu sossai. yana da mata daya hajiya HAFSA wadda aka fi sani da hajja.bafulatana ce usul gashin ta da kyanta ma abun kallo ne mata ce me karamci,kawaici,hakuri, da wayo. tasan hakkin dan'adam ga kyauta, da tsafta ma'abociyar kamshi ce.

yaran su  uku kacal maza biyu mace daya babban dan shi sunan sa UMAR (mahaifin su ahalam) ya karanci kasuwanci shi ma,yana da nutsuwa da nasibi''

AHALAMWhere stories live. Discover now