chapter 46

1.8K 49 3
                                    

💥AHALAM💥
written by khairat up

F.O.W

impacting valuable knowladge and entertainment is our concern!

_vote for me @wattpad khairi_muhd_

48

"turaruka ta kuma fesawa ta sa wasu rikitattun kaya wani wando ne ya matse ta da riga iya cibi ta sha makeup amma light make up ta dau hijab burmeme ta saka ta dau twins ta kai wa iya tani,kitchen ta fada ta fere dankali ta soya masa da plantain da kwai tana juyewa a flask ta ji motan shi murmushi tayi hade da ajiyar zuciya!ta dora a dining ta yi waje."

"a kofar falo suka yi ragas da juna a tare suka saki fara'a ya lakce mata hanci ,see u, sai wani doki ki ke ko? ta waro idanuwa ta ce eh din na love,ya bude baki ya ce hah, ya halin ki da haka matas? irin naka ne?"

"i miss yuh, i miss yuh too walahi ahalam fada miki irin kewar ki dana yi ma aiki ne,bn san ina miki irin wannan true love din ba sai sanda ki ka juya mun baya kar ki kuma my heart horon ba kyau ba dadi matas kar ki maimaita dan next tym ina ganin sede mu kwashi yan kallo dan kuka zan ta miki a titi"

"dariya ta sakar masa ta ce bazan kuma ba my D na tuba na bi allah na bika"

"rungume ta yay a jikinsa ya ja ta ciki.ina yarana? suna gun iya, a kawo su ko? aa my D a fara cin abinci tukun,ke ni ai abinci daya nake bukata,me kenan ta fada tana kanne ido daya kin sani ai my heart ina labarin zuciya? yana gun ka my love"
"my heart wallahi ina san ki,ina kaunar ki,ina ji da ke,ki daina bata ranki a kan wasu daban har ki dinga bata mun nima kin ji?"

"an gama nawan abban 2!"

"abinci ya ci yay wanka aka dauko twins ya gama harkokin sa labari ya sha ban ban kuma a gun masoya biyun."

"a wannan rana ahalam ta kuma yarda adnan nata ne ita kadai,sannan fushi baya maganin komai ta kuma godewa iya tani da shawarar ta"

cikin shekara shidda ahalam ta kamalla karatun ta,ta fito da sakamako me kyau,yaranta uku bayan twins,ta zamo babbar mace da kuma mace daya tilo a gun adnan ta ko ina ji yake da ita, saukowa take daga benen falon dafe da kai ta hade rai kuwa abdulhalim,khalil,maheer aikin da kuka mun kenan a falon? duk suka nutsu suka fara kwashe filalukan da suka zubar a kasa sai suka nutsu baba (muhammad) harda kai? katan kawai yay kasa da kan sa ,lokacin adnan ya dawo dukkansu suka je gun sa da gudu oyoyo daddy oyoyo, ya shafa kawunan su ya kalleta ya na ganki haka, yaranka mana, au sun fara rashin jin kenan? eh man,har maheer ma sun koya masa da yan kafafuwan sa da basu gama kwari ba, suka sa dariya ta ce ka gani ko ka gani, kai ku bari kar anjima a hana mu chocolate ku raka ni daki, du suka bi shi, fu'ada da ke zaune tana kallan su kawai dayan bayan daya ta ce daddy welcome, ya juya yauwa ni mantawa nake da wannan salihar baiwar wallahi, ahalam ta ce ai baban ta aliyu ta gado sanyi da miskilanci ko ni ban kula da ita ba a kan kujerar wayanan hudun kawai nagani wai harda fu'ad katan kawai"

"fu'ad ya zumburi bakin sa ya ce mommy!"

"me wani mommy ai in kun kuma kunnuwan da basa ji zan cire na yar a shara"

"su abdul suka tsure harda rakubewa a jikin daddyn nasu"

"yana dariya yace mummy mun tuba mun daina a yafe mana dan allah"

"ta gyada kai ta ce last warning kowa yaje yay wanka ya zo muyi dinner!"

"ok mummy! gaba daya suka fada suka yi ciki."

"ahalam ni ma naje nayi wankan?"

"hararar love ta masa ai kaima bka ji din"

nan suka ci abinci suka kwanta bacci. daddy gobe muna san zuwa mu gaida umma a mana izini.

AHALAMWhere stories live. Discover now