21

791 57 1
                                    

💥AHALAM💥
love story
written by khairat up

F.O.W

         22

"kallon kallo aka koma yi tsakanin adnan da ahalam wanda jannat na hankalce da su tsaki tayi hade da danne bacin ran ta ,hannun adnan ta kama ya juyo a sanyaye yana kallon ta murmushi ta masa muje my all kana bukatar hutu,haka ne ya fada ya na shiga mota"

"motar su umma ta shiga ta kwantar da kan ta a jikin kujera, ta lumshe idanun ta masu rikita yan maza,masu dauke da wasu irin sirri a cikin su,hoton abu daya kawai take gani a cikin su ADNAN, da sauri ta bude su ta dinga nanata innalilahi a ranta,hakan nan wasu hawaye suka zubo mata a fuska"
     "ahalam me ya saki kuka?"
"umma kawai ina kukan farin ciki ne na samun kubuta daga sharrin dangin su ahamad!"
       "ahalam ni fa mahaifiyar ki ce when did all this start disturbing you? kina boye mun wani abu ki fada mun am your mother zan yi kokarin magance miki matukar zan iya ok?"

       "umma ba komai da gaske,"
  "Allah sa hakan ne,dan ban yarda da ke ba bakin ki na furta wani abun idanuwan ki na karya ta ki still in kina da damuwa tell me ok?"

   murmusawa kawai tayi a ranta kam cewa tayi is to late ba wanda ze iya ban abunda nake so dan ya mun nisa kawai ni kadai nake hauka na yana da matar son sa ni kuma kanwar sa ce _zuciya ta baki min adalci ba da son wanda baya sona!_
_cikin kankanin lokaci komai ya kwace wa ahalam kwata2 ta sauya kaman ba ita ba karatun su ya kankama duk wata hanya da zata nesanta ta da adnan bi take in ya gama musu lec ta fita,in yazo gida bata fitowa.cikin jannat watan sa uku lokacin samhatu da aysha sun gama degree din su har ma ana shirin bikin su a karshen wani watan.anko kala hudu aka fitar tsadaddu bikin yan babban gida wannan karan sakina ta dira a nigeria da faruk dinta da wani babyn a ciki wanda ya tasa ma,umma na mata fada tace umman mu bikin samhatu guda ai na zo ko ina labour room,dariya umman tayi ta ce sakina kenan se kuyi ta tsare2n ku an fitar da event hudu,mother's eve,kamu ,dinner,da kuma sister's day.jannat ma ta gama yarda adnan nata ne ganin irin nesanta juna da suke yi shi da ahalam.shi ko adnan besan yana san ahalam ba sai wannan karon gaba daya ta daina kula shi ko hira take tana dariya in ta gan shi gimtsewa take yi hakan na damun sa har sim ta canja duk saboda shi,yanzu ma tana zaune cikin yan'uwan ta suna tsara adon ajima ya shigo fuskar nan murtuk,ya bita da kallo tamkar ita ce amaaryar ta yi kyau se sheqi take sakina ta katse shi, ya adnan me za a baka? aunty jannat?aka sa dariya,ya sha mur zan tatataka ki yanzun nan ni sa'an ki ne?ah ta fada Allah baka hakuri da alama ranka a bace yake,ke ahalam zo nan? ta yi kaman bata ji shi ba gabanta kau dukan uku uku yake kawai,ahalam ya fada a tsawace ba shiri ta mike ya juya ya fita ta bisa tana kunkunai mutum na zaman sa ze daga mun hankali,jannat ta raka su da harara tace gulmamu kun yi kadan wlh ku kusance tare har abada.kai amare ku tashi muje gun make up din nan time yana tafiya yanzu sai kuji yamman tayi a zo ana african time._

"_me ki ke nufi? kamar ya fa?, oh tambayata ma ki ke? to ya bazan tambaye ka ba tunda ban san maganan me ka ke yi ba,bani wayar ki ni na baro ta a ciki kuma kana bata mun lokaci kasan cewa zan je gun kwalliya saboda funtion din anjima"

"ahalam are u trying to be naive? kaman baki san me nake ciki ba,"

    "ah'ah ya adnan zuciyar mutum birnin sa ka sani sarai ban san me kake sakawa ba"

"ok naji zan kira ki sa mun num ki zan fada miki sirrin da ke raina ina son fita yanzu"

"badan taso ba ta bashi num ta koma cikin gida abunta komai a kan idan jannat aka yi shi yatsa ta ciza sannan ta gyada kai zan maganin ka!"

_gun kwalliya suka je su biyar ko wacce ta sha kyau cikin ankon su na wani less dake ranan ta su umma ce da golden din head fadar irin kyan da amaren ma suka yi bata baki ne bare ga me kyau ahalam_

hall din ko ya cika makil da mutane ana jiran amare su zo basu wani dade ba suka hallara a gun.

adnan da ya sha wani arnen shadda ash ya sha aiki dinkin ya masa kyau wankan ya hau ba karya jannat direct gun sa taje ta zauna tana masa dariya gefen fuskan ta ya shafa hade da taba cikinta yau bamu gaisa ba,kun mun nisa wani dadi taji (ni ko na ce namiji kennan)

ita ko ahalam da idan mutane yake a kan ta duk saita ji mani iri ta hade rai ta koma tebur din da aliyu yake,bro irin mannan kyau haka? ashe kuma anko kuka yi?
   uhm umma ta sa mu dole if not me zamu yi da anko mu ba mata ba.
   amma kun yi kyau ina ya usman? da su ya arfat?
"ya yamutsa fuska alamun ya fara kosawa da maganar ya dai daure, kin san su ze wuce sun tafi neman yan'mata!

   aiko gasu can ya dau wayar sa yana duba wa,

"wani matashi ne ya zauna kusa da ahalam hade da yin sallama, amsawa tayi tana gyara zaman ta,

me gaskiya ara mun kanwar ka man
    aliyu ya ce gaka ga ta ni me na wa dama ta dameni da magana!
   ahalam ta bude baki haka ne ya leee?
   tunda ta fadi haka yasan da magana a bakin ta indai ta ce ya lee to akwai wata a kasa basarwa ya yi du yadda taso ya kalle ta ki ya yi ya maida kan sa kan waya.

yake kawai take yi,ahalam, na'am ta amsa a dararre ganin irin kallon da ADNAN ke mata dan a bayan su seat din su yake.

suna na ajmal imam ni abokin aliyu ne a wajan aiki kuma aboki na na gari

murmushin dole tayi ta kagu ya barta sako ne ya shigo mata waya

_"ahalam ki bar seat din nan tun kan na bata miki ni zaki ma wulakanci kina ma wani murmushi a gabana?_

    "to ikon Allah kai kuma a wa? kana hira da matar ka ban ji haushi ba sai kai ne zaka dame ni wani ne ya kuma shigowa

  _look at me ahalam_
         "kallon sa tayi ya kuma mata warning da idanuwan sa kallon bar wurin."

wata iriyar harara ta sakar masa

ya nuna kirjin sa ni?
  uhm ta gyada kai

mikewa yayi ya nufi gun su

    ku biyo alkalamin khairat ❤.
    yawan comment yawan page 😜

ina yan team #adnanahalam😍?ku fito yanzu za a fara

AHALAMWhere stories live. Discover now