34

715 42 2
                                    

💥AHALAM!!💥
love story
written by khairat up

F.O.W

🌳
impacting valuable knowladge and entertainment is what we concern🌳

  _HAPPY INDEPENDENCE DAY_

               34

"zauna wa ya yi gefen ta hannun sa na cikin na jannat ya sake ta ya na tapping bayan ahalam haba my heartbeat, kukan ya isa kina so ni da auntyn ki mu taya ki kukan mu ma? ki yi shiru zamu rike ki amana da hannu biyu stop crying kin ji"

"jannat ta kyabe baki ta bata rai sai ta kuma basar a ranta ta ce lokaci ne!"

"kanwar mu muyi hakuri da juna kin ji ai gida ki dawo me na kuka yaya adnan din ki ne fa  kar ki zo kina ciwon kai"

"adnan ya lallashe ta har seda tayi shiru tukun na ya samu ya musu fada aka kuma raba kwana biyu biyu kaman yadda aka ce ayi har daki ya raka jannat sannan ya dawo,rungume ahalam ya yi hade da mikar da ita ya zare mata mayafin jikin ta, je ki yi wanka ki zo mu ci abinci yunwa nake ji my heart"

"to kawai ta fada cikin sanyi ta shiga toilet!"

"tana gamawa ta sa wata yar riga wadda ya miko mata ta saka, ta fito ta zauna tare suka ci kazar da fresh milk,ya umarce ta da ja je tayo alwala tana fitowa shima ya shi shiga ya yo tasa alwalar ya ja su sallah irin wadda annabin mu ya umarta da ayi! daga nan kuma ya adnan ya koma adnan din sa sak, ya dinga sarrafa ahalam yadda yake so duk da karatun ya mata nauyi tana kunyan adnan haka ta daure"

"niko na ce asuba ta gari!"

💥💥💥💥💥💥

"da safe a break jannat dankali ta soya da kwai hade da dafa ruwan tea ta kai musu ganin basu tashi ba ya kara tunzura ta da hasala ta lallai adnan ba komai ae lokaci ne! kofar ta buga musu da karfi adnan daga kwance yaji kan sa ya sara masa, ya muskuta dan a gajiye yake dan be yi bacci ba da kyai ya bude idan sa ya tashi, ya na budewa ta fada dakin wanda tana sane so take taga yaya aka yi!"

"oh sorry my all na tashe ka ko? ka mun afuwa ga break can ya kammala nasan yunwa ku ke ji"

"my all bara mu kimtsa tukuna jiramu a falo muna zuwa"

"kaman tayi kuka ta ce to da yake a fuskarta!"

"wanka ya taimaka mata tayi shima ya yi wata shadda sky blue ya saka da aikin dark blue a jiki, ita kuma atampa ta saka zani da riga ta kashe dauri ta zuba kwalliya da wasu irin bangles da sarka da dan kunne!  wow madam kin hadu fa murmushi kawai ta masa ya kama dan yatsan ta na tsakiya suka fita"

"ta ko ina annuri ke fita daga fuskan adnan duk wanda ya gan sa yasan ya hadu karshe zaunawa yayi yayinda tun fitowar su jannat take kallan su tamkar wasu taurari masu haska sama! kishi ya kama ta dama ga ahalam da iya ado adnan kuma me san ado ai shi kenan kirjin ta na bugawa da sauri da sauri kawdi dakewa take yi."

"aunty jannat ina kwana?"

"lafiya lau ya ki ka tashi"

"alhamdulilahi,ya kwanan kadaici?"

"lallai wannan yar ayi ce!"

"mun sha shi kam ya jiki jiki?"

"to da sauki dai ta fada tana kallan adnan wanda yana jin su tamkar be san me suke yi ba haka ya koma musu dan kar ayo aika aika ya katse musu gaisuwar!"

"my all ki zuba mana abincin mana"

"zuba masu tayi saida suka ci sossai kuwa yana gamawa ya mike ya ce my wife's naje gidan umma sai na dawo ka gaida mana ita inji jannat zata ji ko zamu je tare my heart?"

"hararar wasa ta masa yana dariya ya juya sai na dawo!"

"a dawo lafiya allah ya tsare ya kare ka"
"amin".

💥💥💥💥💥💥

"ango ango kai ne? "

"yana sosa keya ya ce umma hada ke?"

"to na daina ina matan naka da fatan suna lafiya dai ko?"

"suna ma gaida ki umma"

"ina amsawa"

"umma zan wuce,"

"ina kuma?"

"makaranta zan je ai basu bani hutu ba!"

"ayya to a dawo lafiya ka kula ayi ta hakuri adnan yanzu ka kara samun responsibility ka yi adalci banda yawan fushi ko gaba in suma kar ka tanka musu fita waje ka yi formating sai ka koma ka dau mataki a tsanake ba cikin fushi ba yanzu kai zaka yi deciding zaman lafiya ka ke so ko akasin sa,kar ka sake ka dinga tona sirin da ke tsakanin ka da matan ka ga kowa ko kuma ka fadawa daya ai wance kaza take mun wance kaza take mun hada fitina ne hakan kaji ko?"

"zan kiyaye umma nagode, insha allah zan zamo adali me hada kan mata na"

"allah ya maku albarka gaba daya sannan in kun samu lokaci kuje gombe ku gaida dad dinka da mum dinka yana da kyau su saba suma"

"to umma yadda ki ka ce haka za ayi!"

AHALAMWhere stories live. Discover now