24

737 50 0
                                    

💥AHALAM💥
love story
written by khairat up

F.O.W

             24

"jannat tayi wani shu'umun murmushi ta gyara zaman ta ,ta na sane ta taba adnan ba wai iya taba shi tayi ba har ma da wata jaha ta taba a jikin sa wanda hakan ya yi sanadiyan shidewan adnan yana kokarin sakin kan mota fakawa yayi be shirya ba,ahalam ta dago a tsorace,jannat! ya furta a hankali so ki ke muyi hatsari? ta kama kunne tana dariya am sorry my all na tuba,duk sai yaji dama be dauko ahalam ba yanzu me zata yi zato? ahalam kam ihu ne kawai bata yi ba tayi kasa da kai tamkar bata ma san me suke yi ba,amma kasan ranta ji take kamar ta tsine musu wannan ai CIN FUSKA NE."

    "duk yadda jannat ta so taga yanayin da ahalam take gazawa tayi haka ta hakura har suka karasa hall, kallo daya zaka yi wa ahalam ka san ranta a bace yake!".
haka aka gudanar da biki fuskan ahalam a murtuke shi kan sa adnan seda ya sha jinin jikin sa,ajmal duk yadda ya so ya samu ganawa da ahalam bega fuska ba wani kwarjini ma ta masa yau dan yau miskilancin ta sossai ya tashi jannat kam wani dadi taji ganin tarkon data dana ya kama walwalar da ta dinga yi ya bawa adnan dariya ma da mamaki tamkar tafi amaren ma murma,farin cikin me ki ke yi ne? baza ka gane ba my all yau ina cike da farin ciki,a fili yace thank God a cikin ku an samu wadda take cikin farin ciki! me ka ce? tunda baki ji me na ce ba ki bar shi a ran ki."

da aka tashi motan saifullahi ta shiga, duk yadda ya so su yi hira ki tayi taki magana har suka je gida.

washe gari dinner,material suka sa wannan karan maroon da head baki sun yi kyau jannat ma shi ta sa mazan ko bakin yard suka samo me kyau suka dinka suka sa huluna irin karin yarabawa a karkace, 

   yau ma motan saifullahi ta shiga sun sha hira guri daya ma suka zauna dashi wanda ya bakanta ran adnan har seda ya tashi ya fita waje jin zuciyar sa na suya kirjin sa na masa zafi nan da nan idanuwan sa suka yi jajamur, cikin mota ya zauna ya maima kujerar baya ta kwanta ji yake a kan ahalam ba abunda ba ze iya ba shi yasan yana san jannat amma ba irin wanda yake ma ahalam ba yadda yake ji a kanta ba irin na jannat ba ne fiye da haka ne a ran sa."

    "be ma san an tashi ba har seda yaji hayaniyan mutane na tashi ta ko ina, alamun an fara tafiya kenan,wayar sa ta fara kara yayi tsaki ya dauka,hello jannat ya ne? kana ina an tashi fa,ya kuma kallan wajan da take dan ya hango ta ya ce karaso inda muka yi parking ina cikin motan na gan ki ni ae.ok ina zuwa! daga gaban sa ya ga ahalam jikin motan saif tana jingine gefenta ajmal ne wanda yake mata hira tana masa dariya innalilahi ya dinga nanatawa yaji kaman ya yi kuka jannat na shiga tace muje my...fita ya yi be ma mata magana ba ta hangame bakin ta tana jin haushin sa wai da gaske adnan yake san wannan yarinyar yake me kama da aljanun ruwa. malam ajmal ya juya, na'am adnan, ina san magana da kai!ok ina ji, mu koma gefe aa ba komai muyi a gabanta ba matsala ae,tunda ka zabi hakan to hakan za ayi! ina san fada maka ka kiyaye shiga harkar matar wani excuse me a iya sani na nasan ban taba kula matar aure ba, ga ta kuwa a gaban ka ajmal ya murmusa ai ahalam bata da aure allura ce a cikin ruwa me rabo ka dauka! haka ka ce? yes! ai tunda tana sona ina san ta magana ta kare ko ahalam? ta gyada masa kai hannun sa ya daga ya zuba mata mari ajmal ya harxuko zai rama mata ,ahalam ta dakatar dashi bar shi ba komai so ne kai nake so,aure ne kai zan aura, hannun ta ya murda ta yi kara tuni jannat ta fito da sauran wanda basu tafi ba, karya ki ke ya fada cikin karaji ni ki ke so kuma ni zaki aura baki isa zama da wani na ba, kai kuma ba kai ba ahalam na muku katanga daga yau daga wannan lokacin. ya adnan me sa ka ke shiga rayuwata me ruwan ka da saurayi na! ban taba cewa ina san ka ba,dan ba na yi kana zaune lafiya da matar ka zaka bata muku farin cikin ku, ahalam kece farin ciki na dam jannat taji ,yake ahalam tayi to in dai ni ce farin cikin ka gwara kaje ka sauya kasan inda dare ya maka! kirjin sa ya kama yana yamutsa fuska, abubakar ya dafa shi adnan ya juya cikin hawaye, halifa ahalam bata so na, ahalam bata so na, ahalam....sai ji suka yi ya fada kan abubakar jannat da ahalam tare suka saki ihu"

"tashin hankali kennan (litaffin aunty rukky), ahalam tsuguna ma tayi ta dora hannu a kai yayin da jannat ta ruga gaban mijin ta, ta rungume ta saki kuka ya abubakar taimaka min mu je asibiti ya adnan ka tashi, abu ya ma rasa me ze yi usman ne ya yi kokarin daukar sa ya sa a mota jannat ta bishi tana shiga ya ja motar, ya ya mu bisu dan Allah da kyar ya saita kan sa ya ja hannun ta suka nufi motan sa."

    "taimakon gagawa aka yi masa da kyar likitan ya yi nasarar shawo nufashin adnan wasu dube2 aka kuma masa."

    "likitan sanda ya fito ya zare hular kan sa ya ce gaskiya dr. yana cikin matsanancin damuwa wanda ya haddasa masa kamuwa da ciwon zuciya amma if care is taking za a samu maganin abun da wuri tunda bata ....... ahalam ta saki kuka umma ta zuba mata tsawa yi mun shiru. jannat dake zaune jikin sakina du su biyun kukan suke yi ta dakata a ranta tace ciwon zuciya a kan san ahalam wannan wane irin so ne? in bata san rabuwa da adnan ya zama dole ta fadawa umma makasudin ciwon dan tana san mijin ta."

  "dr.zamu kiyaye da yardar allah ya kada kan sa ya tafi."

  _akwai wanda ze iya fada mun me ya faru a gun ko kuma kukan zaku cigaba tunda hawayen ne zai bashi lafiya,cikin bacin rai umma ke maganar._

   jiki a sanyaye jannat tace umma matsalan ya adnan ahalam ce, ita ce damuwan shi

AHALAMWhere stories live. Discover now