31

868 43 0
                                    

💥AHALAM💥
love story
written by khairat up

F.O.W

_🌳impacting valuable knowladge,and entertainment is what we concern🌳_

              31

"mu jima lafiya ,adnan ina sakina? dad tana gidan abbu,rabon da na sa sakina a ido na ya yi 3year's yanzu ance mun ma ta haihu ko? wani malolon bakin ciki  ya tokare adnan ya zame jikin sa daga na uban wai uba ke tambaya a kan dan sa da ya san ba a garin take ba rabon sa da ita shekaru uku anya ko dad be samu matsala ba ta asiri?"

"ko zamu je gidan umar din? na ganta da grandchild dina? ya tsinkayo maganan dad din"

"a ran sa ya ce ko ma dai meye uba na ne zan bi shi murmushi ya kakalo dad muje na kai ka dan umar karami har ya girma yana tafiya kuma yana magana ta na ma da wani cikin"

"lallai sakina ta girma muje son na gan su na shafa kan su ko da bana fada i miss u guys! kullum ina tunanin ku kawai yanayin aiki na ne ya sa ni a gaba."

"haka ne dad amma duk aikin ka ai ya kamata kana duba lamuran mu dad ai baka son mu baka damu da komai na mu ba dad har aka kusan kashe ni na gama zamana a asibiti baka zo ba wai kana aiki dad wato aiki ya fi ma yaran ka? dad babu shakuwa a tsakanin mu dad wasu neman ya'yan su ke basu samu ba kai ka samu amma ka butulcewa allah amanar mu fa amana muke a gunka,ba mu da uwa sai kai dad ka duba,"

"jikin dad ya yi sanyi ya juya daya gefen yana jin wani iri,tabbas ya san ba ya kyauta wa yaran tunda be damu da su ba shi kan sa be san me sa hakan ba amma yasan yana kewar su ,ya na kewar su,ya na san ganin su,amma kasawa yake!"

*KUMO RESIDENCE*

"Shigar su harabar ke da wuya ya hango su basma tare da sakina da small umar a zaune kan sallaya suna hira gefan su fruits ne an yanyanka su"

"karasowar su kusa da su ya tsananta bugun zuciyar sakina ganin dad wanda ta jima bata gan sa ba balle taji muryar sa"

"da kyar sakina ta bude bakin ta , ta gaida dad yayin da umar karami ya lafe a jikin adnan shi kuma ya daga shi sama ya dauke shi abbun mu wasa ka ke? yes uncle dad ya shafa kan sakina yna mata murmushi maida masa tayi tsakanin d'a da uba sai allai kuka ta sa ta rungume dad din ta soma magana dad me muka maka? ka manta damu? me ya sa ka wofantar da mu? dad baka san mu"

"shhhhh,sakina kawai aiki ne amma ina san ku ina tunanin ku ina kewar ku ki daina cewa bana san ku,bani jikana takwaran umar ne ashe? uhm ta ce kawai"

"ciki suka shiga suka zauna samarin gidan suka dinga zuwa gaida dad yana shi musu albarka suka zauna, nan aka koma tambayar adnan jikin ahalam ya ce da sauki ae an yi aikin tun dazu!"

"Allah ya bata lafiya ya kara sauki! amin! ina jannat ban gan ta ba tun shekaran jiya inji sakina!"

"ba ta rai adnan ya yi ya cigaba da wasa da umar karami,"

"basma ta shipa daki kenan taji wayar sakina na kara dauka tayi ganin num jannat ce"

"hello aunty jannat ba aunty sakina ba ce tana falo tare da su ya adnan"

"ok,basma ce kennan?"

"eh!"

"ok, ina ahalam?"
  "ya ahalam ai bata nan tana asibiti tun shekaran jiya aka kwantar da ita yau aka mata operation"

"haba dai ban sani ba ai yanzu kuna ina?"

"muna gida, yanzu haka su umma ne a asibitin amma muma yanzu zamu tafi asibitin kai abinci"

"to bara na zo na same ku sai mu wuce tare da ku kawai allah ya kara sauki"

"amin sai kin zo!"

     "yanzu muka yi waya da aunty jannat zata zo wai bata san ahalam na asibiti ba."

"aha kawai sakina ta fada"

_allah sa ta sheqa lahira yarinyar ashe shi yasa adnan ya rude,ya damu yar gwal din sa ba lafiya!zan je na yi ta addua ta mutu ina zaune na ji good news din da kunne na!😄_

"suna shiga mota jannat ta danno kan motar ka gidan adnan ya kuma hade rai ya ma mota key suma sauran haka ganin kaman zasu fita sai ita ma tayi reverse ta fita ta basu gu tana bin su a baya amma kunnen ta earpiece ne tana jin waka tana kada kai tana bi"
"tamkar wata mutuniyar arziki ko wata me kaunar ahalam ranan haka jannat ta kasance,kamar yadda dad ya fada ta na farfadowa ya kuma duba ta da kyau ya sa aka siyo magunguna aka bata abu me ruwa ta sha kaman tea haka, dakin da ba hayaniya ita kadai aka maida ta adnan ne kawai a cikin dakin yana rike da hannun ta"

"murza yan yatsun ta kawai ya ke yi idanunta a lumshe suke amma idanun ta biyu,wani irin kasala ta ke ji,a jikinta sam bata jin kwarin jikin ta saboda aikin da aka mata,ta na motsawa ya zabura sannu ahalam ! juyo da kan ta tayi kawai tana kallon sa ta kuma riko hannun sa ya bi ta da kallo yana jin wani kaunar ta na ratsa ko ina na ilaharin jikin sa."

"ya adnan ya matso saitin bakin ta ya kara kunnen sa dan yaji me take cewa, ya adnan zan sha ruwa! ok ina zuwa fita ya yi daga dakin da sauri, dad wai zata sha ruwa zan iya bata? of course amma me dumi zaka bata kaje nurse station ka samo mata sai a bata ta sha ko to dad.?"

AHALAMWhere stories live. Discover now