26

772 48 0
                                    

💥AHALAM💥
love story
written by khairat up

F.O.W

                *26*    

"Dariya yan dakin suka sa ma ta sakina ta ce ni dama nasan akwai abu tsakanin su suke boye wa suna basarwa to yau dai gashi alkawari ya cika."

   "jannat kam mikewa tayi ta yi waje dan tafiya gun adnan likita ya ce ya farka, tana fitowa sai me? adnan ta gani cikin angwaye fuskan nan kaman gonar auduga ya sha wata shadda blue light, sai baza kamshi yake mamaki ma ya hana ta magana,kawai kuka ta fashe da shi wanda bata san ma ta sake shin ba, so masifa ne,wato..... adnan ne ya sa tattausan hannun sa yana goge mata hawayen yana girgiza kai stop crying am ok my all kar ki sani a cikin damuwa kin ji? zo muje samarin gun suka dau shewa yayi me mata biyu na uwargida jannat ga kuma amarya ahalam kana wuta me zamani."

"ko ta kan su be bi ba ya ja hannun matar sa suka hau sama falo ya zaunar da ita a kan kujera ya tsuguna shi kuma ya hada hannun su gu daya ya matsa a lokacin wasu hawaye suka kuma zubo mata,shihh haba my all! kar ki ba wa marada damar da zasu yi mana dariya mana ki kwantar mun da hankali. auren ahalam ba yana nufin bana san ki ba ne ae ke ce all dina,first dina kuma ga baby na a jikin ki kuma! don't worry kin ji? "

"my all, a kanta fa ka kamu da ciwo ai kaga kuwa ka fi san ta dubi fa jiya mun bar ka ba yadda ka ke amma ynxu ka mike har kana zuba ado ka kasa boye murnar ka"

_"to ai jannat in na ce miki bana san ahalam ai na miki karya kuma kema in na ce bana san ki na miki karya dukkan ku ina sanku kuna raina bazan iya affording rasa ku ba, mu hada kan mu ai kodan umma me kaunata da abbu me jin 'kai na zan nuna farin ciki na a kan aura mun ahalam da suka yi balle kuma ina san ta_"

   "insha allah zan yi kokarin danne kishi na, youwa my all.a ranta ko cewa tayi namiji kanin ajali,amma ahalam zaki san kin auri mijina da kissa zan gama da ke sai na nuna miki ke sabuwar zuwa ce a wannan ajin."

"ahalam na can taji an ce adnan ya dawo gida amma be neme ta ba.wanka samha ta sata ta yo ta sa wata atampa me kyau ta yi light make up sakina ta shigo tana dariya kun ga ya ya kuwa? tamkar dama jira yake ya sha ado yana zuba kamshi dama ciwon na rashin ahalam ne,kuma tunda ya same ta ai ya warke,yanzu kuma yana can gun uwargida me jarumta. dam gaban ahalam ya buga taji wani banbarakwai ta saki guntun tsaki kaman ba ita ba toilet ta shiga ta wanke face din ta fuu ta fito ta yi waje yan dakin suka bita da kallo amira kawar samha ta ce me kyau kennan ai yanzu zaman kishi zaki yi ai uwargidan ma tayi kokari ni ina zan iya"
"wata iriyar harara ahalam ta sakar mata sai tayi shiru dama ta dawo daukan wayan ta ne ta dauka tayi waje,wata ta ce ahalam na da charisma. dakin umma ta shiga ta kwanta tana jin haushin adnan ai ita ya kamata ya fara tinkara ba jannat ba, aikin kawai ta fada tana tsaki, ba sai ka gan ni ba."

        _yana rike da hannun jannat suka shiga dakin yan matan dakin ya dau sowa ga ango ga ango aka ta masa tsiya murmusawa yayi ya ce naga alama kun raina ni zan dawo kan ku badan kun gama ba da na ja muku co ku koma baya. aka dau ihu aaaaaahhhh ai ba za ayi haka ba sir barin maki ya kamata ayi yau ka zama angon AHALAM  to naji ina amarya ta? ae amaryar ka bata nan ta ce se anyi budar kai tukuna za a ganta 😜 wato amira na san inda takardun ki suke...... ayi hakuri sir amarya ta bar nan bamu da labarin tana ina! hannun matar sa ya ja suka fita duk inda ya bi ace ango, duk inda ya yi ace ango me mata biyu wasu ya amsa wasu ya basar.kwarai yake san haduwa da ahalam ya rungume ta ko ya ji sanyi ya tsotsi lebban ta ko ya ji dadi a ran sa amma be ganta ba,text ya tura mata "AMARYA TA WHEPHE ARE U?" tana karanta wa tayi tsaki ta bagarar da wayar.jannat ko ta gama yarda adnan is in love with that small gurl._

AHALAMWhere stories live. Discover now