25

815 48 0
                                    

💥AHALAM💥
love story
written by khairat up


F.O.W

"a zabure ahalam ta  mike ta bi umma da kallo gaban ta na dukan uku2 da kyar ta dan saita tunanin ta gu daya ta hadiyi yawu ta kalli jannat, aunty jannat wace iriyar magana ce wannan ki ke fada? me hadina da damuwan shi,ai tuntuni na daina masa rash......ke ki mun shiru umma ta fada, jannat idan na fahimce ki adnan na son ahalam? gyada kai jannat tayi wasu hawaye suka biyo kuncin ta,ahalam ta ce umma ni fa ban san sa ban ma san yana yi ba"

     "wayar umma ke neman agaji masu abincin gobe ne na daurin aure suke mata waya bayan sun gama magana ne,umma ta kalli abubakar tayi waje bayan ta ya bi dan ya gane nufinta."

_ka fada mun me ainihin damuwan adnan kasan amana ne a guna yaran nan? bashi da  waru makusantan bayan mu ,sannan adnan ya wuce ya yi kukan rashi a gu na_

     *haka ne,umma adnan ahalam yake so kuma ya jima yana mata san wanda har aka yi bikin ta ma ya hakura ni kadai na sani dan ran daurin auran su ni na kai shi asibiti aka duba shi jinin sa ya hau sossai!dana matsa masa da tambaya sai ya fada mun dalilin sa na yin hakan amma kada na fadawa kowa tunda tayi aure,to da auran ya rabu kuma sai...... shiru ya yi kawai dan ya kasa karasawa ma umma ta ce je ka ka ce su fito kowa ya tafi gida a bar shi ya huta da safe a dawo*

_kai duk ku fito mu tafi gida umarnin umma ne jannat ta ce zan kwana pls,ina tunanin ke ganau ce yau umma ranta a bace yake sossah kar ki musa mata ku taho mu tafi.ba dan jannat ko ahalam ta so ba suka tafi._

     "aunty jannat tasan ya adnan na santa dama? me sa zata roke ta a kan ta auri mijin ta wanda in ita ce bazata taba yarda ba,wai a kan ta yau aka kwantar da ya adnan lallai so abun tsoro!."

💥💥💥💥💥💥

"ya jikin adnan din?
da sauki dai za a ce amma besan ma inda kan sa yake ba!     allah ya sauwake amin amma me musababin ciwon?
   AHALAM!
ahalam kuma? eh abbu ahalam, ta ya ya kennan?"

"wai saboda yana san ta ita kuma tace bata san sa yaran nan ya fadi ya suma wanda har yanzu be farka ba"

"subahanalahi, banda abun adnan in ya fada mun ai zan yi kokarin ganin na bashi ai da shi da ahalam duk yaya na ne ina da iko da dukkanin su amma kar ki damu zan san abun yi bara yaji sauki"

"amin, abbu ina labarin barrista?"

"ai ina jiye ma M. KUMO haduwar sa da Allah,ace yayan ka bata su ka ke ba ta neman duniya yake, hakkin su ma baze bar shi ba wlh, dan in ban manta ba ko kar na masa karya, ya manta ma yana da wasu yara adnan da sakina"

"ai abbu bokon ce ta ratsa su sossai"

"iskancin banza, ai shi bature tattala dan sa yake yana jan sa a jiki yasan darajar dan nasa akidar banza ya ke da kawai ai na sa ma sa 👀 ne kawai akwai ran da na sani ae"

"haka ne Allah ya yafe mana ya shige mana gaba amma ba ya tsoran Allah ba shi da imani kaga kwanakin da adnan ya yi a asibiti har operation aka masa amma be ko yi waya yaji ya jikin sa ba ko nawa yake nema ai da yafi gaban wasa wani nema ma yake be samu ba shi da yake dasu kuma ya wulakanta ka duba fa ita sakinar bata ma san zancen uban har gwara adnan din yana zuwa ko da be gan shi ba"

"duniya ai makaranta ce ta ishi kowa"

"gaskiya ne kam wannan"

💥💥💥💥💥💥
"RANAN WANKA BA'A BOYEN CIBI"

11:00AM
_UMAR KUMO RESIDENCE_

"Harabar gidan ta cika makil da mutane ta ko ina ba masakar tsinke kowa ka gani yana cike da farin ciki da annashuwa a tare da shi,an babaza malun malun wasu iya yar ciki.

    a ranan aka shaida daurin auren aysha, samhatu,ta re da ahalam kowa ya cika da mamakin ahalam a ciki dan sun san mutum biyu za a aurar daga samhatu sai aysha to ga karin ahalam,
   ba yan waje ba kadai familyn kumo ma gaba daya sun sha mamaki.

sanda aka sanar a cikin gida ba kamin kaduwa mata suka yi ba,

  wata mata ta ce "ayiriri alkawarin Allah ya cika an shaida auran yan mata uku"

"yan mata uku kuma"

eh ai sun yi arziki aurar da yan mata biyu da bazawara a rana daya.

  umma ta sha mamaki harda ahalam aka daura auran?

eh hajjau harda ahalm me kyau fatan Allah ya zaunar dasu lafiya
alhaji adnan ya kara girma mata biyu ina uwargida ta bani tukuici matar ta fada.

jannat kam danne zuciyar ta tayi wani irin kishi ne yake taso mata da kuma takaicin wai adnan a kan wata zai kwanta ciwo ba ita ba ashe san na karya yake mata!

ahalam kam na jikin tagar dakin su kawai jikin adnan take sanin ya yake amma ba hali umma ta hana kowa zuwa wai hutawa yake wani kwalla ne ya zubo mata ina amaren?

gamu nan aunty nabilah!

albishirin ku!
goro
fari ko ja?
fari kal kal aunty!

abbu ya yi nasarar sawa a daure ku cikin igiya uku uku da fatan kin kuncewa har abada
   yan dakin suka amsa da amin aka hau shewa da gud'a

ahalam ta fusata wai me haka baku san muna da mara lafiya ba ne sai ihu ku ke mana da shewa kaman......

amarya ba kya laifi kiyi hakuri indai angon ki ne zai mike yau din nan dan an sama masa magani me saurin aiki quick action!

kan ta ya kulle aunty nabilah ni ce amarya ko su ya samha?

ae kema an daure ki da adnan kumo.

jingina tayi da bango ta ja wata ajiyar zuciya, ta yi hamdala hade da jin wani sanyi a ranta

ita ce yau matar _ya adnan_

siraran hawaye suka zubo mata,

AHALAMWhere stories live. Discover now