21

982 49 0
                                    

💥AHALAM💥
love story
written by khairat up

F.O.W

   
             21

jannat ce ta shigo dauke da abinci ta zauna bayan sun gaisa da umma tana sanye da hijab pink,fuskan nan tayi fayau ba make up sai hasken ta da ya fito sossai,tana zama ya maida mata murmushi ta maida masa umma ta mike bara na leqa dakin wancan yaran da aka kawo jiya,allah ya sauwake umma amin.
  'ni zan je gida na huta gobe zamu shiga kotu,cike da tsokana adnan ya ce manyan likitoci sannun ku da aiki suka sa dariya duka

'ahalam dake gefe kawai kallon shi ta ke tana wani irin murmushi me kayatarwa bata ma san sanda aliyun ya fita ba, kawai tozali tayi da hannayen adnan cikin na jannat yana murzawa yana mata dariya kawai ji tayi wani abu ya tokare mata kirji kaman dutse ya ki sauka nan da nan ta sauya fuska bata kuma ankaarewa ba ta ga jannat a tsaye adnan na shafa cikin ta zata fita kennan ya ce ahalam zo ki shafa kan babyn ki ya fara gaisawa da aunt din shi tukuna, jannat tana murmushi tace kanwar mu kalli yayan ki wai ina da ciki daga ganin hannu na da kyar ahalam tayi murmushi,ta ce kin manta yayan mu bayan lecturer likita ne,likitan ma na mata? me bazai gani ba?
    'da biyu jannat ta mata wannan maganan dan ta ga a wane yanayi ahalam take kuma tayi nasara dan har wata yar kwalla ta taru a idan ta'.murmushi ta kuma yi.
      _bara naje allah ya raya mana unborn baby ya fito lafiya duniya mu sha wasa!_

'amin small aunt ko small mum?
     kai kawai ta gyada ta fita direct office din umma ta shiga kawai kuka ta saki sai da tayi me isar ta tukuna ta shiga toilet wanke fuska, _me ya sa nake damuwa a kan ya adnan? me sa in na gan shi da jannat nake jin haushi? me sa bana son yi nesa da shi? wayyo Allah zuciya ta kar ki mun haka ya adnan ba tsaran soyayyar ki bane yana da mata wadda yake mugun so, ga shi ze fara family ke fa kanwar sa ce AHALAM kar kije inda Allah be kai ki ba! ki nesanta kan ki daga gare shi ita ce masalaha._

ahalam kina nan?
uhm fitsari nazo yi!
oh to abinci fa kin ci?
ta yamutsa fuska aa umma na koshi ne sai anjima
   to kina wasa da cikin ki fa bara na sa a siyo miki  yogourt me sanyi da nama ki ci, to umma amsawa tayi dan bata san tana ma umma musu.

tana gama ci ta ce umma mu tafi gida ko?
    'ahalam me ya same ki ne na ga yanayin ki ya sauya gaba daya what's wrong?'

'umma na gaji ne wlh, kai na ciwo yake mun,'

''ayya sannu kije kuyi salama da yayan ki sai mu tafi tare ok?''

''ok''.

daga kofa ta tsaya ya adnan se gobe na wuce gida,

yau da wuri da fatan dai lafiya ko?

"kai na ne yake min ciwo kawai, sannan kuma u need privacy kai da auntyn mu dan ku samu damar kebewa da babyn ku"

"jannat ta dube ta sannu ahalam se da safe"

"juya wa tayi, yayin da adnan ya bita da kallo ya na jin kaman ya ce ta dawo hannun sa da jannat ta taba shi ya dawo da shi daga inda yaje ya mata murmushin nan me tsada wanda ke sa yan'mata rudewa a kan sa adnan kumo kenan *namijin duniya*.
💥💥💥💥💥💥

"da daddare kira ta shigo cikin wayan aliyu yana kan laptop yana nazarin wani case daban na wasu mutane da suka yi wa wata yarinya yar shekara goma sha uku fyade su hudu kattan maza yana kuma nazartar abin ne ba ta case din adnan yake ba dan ya gama samo shedu da yardar allah a gobe zasu gama case din dan yana da solid proof na garkame ahmad, dama da biyu ya shigar da karar dan ya tozarta alh.lawan ahmad irin su basu cancanci su mulli kasa ba in ba haka ba bala'i zeyi yawa a kasa,tashin hankali,kashe rayuka, lalata yaran mutane maza da mata,daukan wayar ya yi ganin bakuwar number sai yaki dauka can aka kuma kiran sa ya dauka a fusace"

AHALAMWhere stories live. Discover now