23

781 55 0
                                    

💥AHALAM💥
love story
written by khairat up

 
F.O.W

              23

"my all ina kuma zaka je?"
   "my all,ina zuwa kin ji zan je gun su ahalam ne"
"a koda yaushe jannat taji ya ambaci sunan da baya shayin kira a gaban ta wato ahalam sai taji zuciyar ta kaman an soka mata kibiya ko ruwan dalma a ciki,be jira kuma cewar ta ba ya yi gaba tare da zare rikon da ta masa."
      "be fi taku daya ya karasa gun su ba, ahalam ta zabura ta mike,ajmal ya ce ahalam ina zaki haka? ina zuwa tuni ta juya ta nufi gun su umma da sauri da sauri"

       "lips din sa ya ciza da kin bari na same ki a gun da kin mamakin me zan miki"

"sakina ta kalli jannat dake rike da faruk tana masa wasa,ahalam na tambaye ki mana? me fa? wai me ya ke faruwa tsakanin ke da ya adnan? ni kuma ? eh ke ,kaman ta mare ta haka ahalam taji amma ta dake ta sha mur ta ce me ze hana ki je ki tambayi wan naki kila ya sani!"

"sakina ta kama bakin ta a ranta ta ce ayi dai mu gani"

    tuni dj ya sakar ma kannen amare kid'a su kadai ta ko ina ana sakar musu kudi musaman ma mutuniyar wadda ta ke bawa ko ina hakkin sa wajan yin rawar! ajmal beyi kasa a gwiwa ba ya dinga manne mata yana zuba mata kudi be damu da yawan su ba burin sa kawai ya samu ahalam yarinyar da abokan me gaskiya suke zuzuta kyan ta da ajin ta ba be taba tunanin cewa karya suke fadi ba dan kyanta ya wuce misalin su.

    waje ta samu ta zauna tana taunar cingum me dadin kamshi tuni takaici ya kama adnan ya ja matar sa suka bar gun bikin wani irin gudu yake zubawa wanda jannat ta tsure ta dafa kafadan sa, adn..nan...ka tafi...a hank.... keee kar ki dame ni da magana ki mun shiru gum tayi da bakinta cike da mamakin adnan dan be taba mata tsawa ba lallai akwai matsala"

yau sister's day wata gown aka dinka ma ahalam fited ta bi jikin ta daga kasa kuma a bude ta baje tamkar ita ce amaryar,wani irin abun dauri ta dauko ta yi daurin nan (zahra buhari) daga baya aka yi wa gashin ta mani irin tufka sai ya sa daurin ya zauna mata das tayi kyau"

flat ta saka ta zura agogo da wasu irin awarwaro purpul mudubi ta kuma kalla ta saki smile ta juya ta dau wata kwalbar turare ta juye kusan rabi a jikin ta,

   a waje kowa yaba wannan ado na ahalam yake ya yin da wata yar uwar su ta ce me kyau yau kin bama kyau ma kashi,lumshe idanuwan ta tayi tana kallan wayarta ta dago a gadaran ce ta ce amal kenan ai wannan tatsuniya kenan ina ni ina gabzawa da kyau? ki sauya tunani akwai rashin jituwa a maganan ki, amal zata yi magana kennan ta hango aliyu duk duniya shi take so shi ko in beyi karya ba da se ya ce be ma san ta a family ba dan bata gaban sa.
  
   "aslaf,usman ,muhammad,arfat ,aliyu,abubakar,adnan,muhd,saifullahi,yusuf, suka nufo su cikin ankon wata farar shadda da aikin baki a jiki,hulunan su ma iri daya,yan'mata suka fara wow zaratan maza kenan lallai akwai kyau a familyn nan na kumo.

ahalam ta sakar musu murmushi ta dakatar dasu gaskiya kun fita selfie suka yi kusan guda goma,yayin da maryam ta nufo su tana dariya sai kuma ta cuno baki, ban yarda ba a sake !
   ke kuma a su wa?
aliyu ya ce korafi ya karbu ke me kyau sake mana wani

   gaskiya banda lo.....
me ki ka ce?
ba komai wani suka sake guda biyar tayi.

aliyu ya ja hannun maryam muje kin ji sis!

  "hah,ya leee no wonder zan fadawa umma ashe ashe inyeee sede baka iya zabe ba,wannan mumunar!"

"kokarin kamota yake ta yi baya tana dariya tsam taji ta a jikin mutum kafadun ta ya matsa da karfin gaske ta yi yar karamar kara,"

"kokarin kwacewa take ta kasa har ga allah da zafi rikon da ya mata,ya adnan da zafi cika ni,wa na kama? me nayi? adnan be damu da mutanen gun ba da ke ta aikin kai kawo wajan shiga mota ba shi da gudun magana ko shakka,nan wata ta fara gulma ta na zuga jannat,mijina ya kama wata a gabana ai sena tsinke ta da mari!harara jannat ta mata ta ce ba kanwar sa bace ban san hadi"
         "hannun ta ya ja har gaban motar sa ya bude mata ya sa ta a seat din baya, da hannu ya yafito jannat alamar tazo su tafi duk da ranta a dagule yake haka ta daure ta karasa.tana murmushi ta ce kanwar mu yau muna tare?"

   "yake kawai ahalam ta mata tana ji kaman ta hada ta da mijin ta zane. ya fara shiga rayuwan ta"

   shi ko yayi haka ne saboda ya ga take taken samarin gidan nasu, baya san ta shiga motan kowa.

   jannat ta dinga jan sa da hirar luv tana wani mane masa

ahalam ta dinga tsaki kaman bata ganin su wani abu ya tsaya mata ya dauko ta ne dan ya nuna mata yana da mata wadda yake so ne?

AHALAMWhere stories live. Discover now