RUWAN DAFA KAI 2
Na SUMAYYA DANZABUWA10
Malamai fa an dage da addua,da sauran alummar gari,don duk mai imanin dayasamu labarin abinda yafaru da ita saiya tausaya mata,dukda dai wasu suna ganin laifinta dana iayenta sakamakon kuskuren dasuka tafka dakansu,na rashin bincika ko shi wanene,wasu kuma suce ai kudi tabi maganin irinsu kenan,masu auren namiji saboda abin hannunshi,hm zantuka dai kala kala kowa da abinda yake fada.Haka zalika,hukuma suma baa barsu abaya ba sun dage da bincike ba dare ba rana don kusan duka police stations din dasuke garuruwan Najeriya sun sami hotonta,dakuma lambar Abba,tayadda daga andan samu wani labari zaa sanar,Allah sarki Su mama suna cikin wani hali abin dai sai wanda yagani kawai abin tausayi duk sun rame,don har sun fara fidda rai ma,duba da yadda lamarin ya shallake hankalinsu.
Suna zaune da yamma dukkaninsu,sunyi jugum,kamar dai makoki akeyi,duba da yadda fuskar kowannesu take kunshe da tsantsar damuwa,babu wanda yake cewa komai,hakika komai yadaina musu dadi.
Kirane yashigo wayar Abba,yadauka yafara magana murya kasa kasa,don rayuwar ma duk ta fitar mishi arai,babu abinda yake birgeshi,kamar dai kowa agidan,wanda ya kira wayar ne ya sanar dashi cewa daga cen ofishin yan sanda ne dake garin Maiduguri,ai wata zabura da Abba yayi dukkaninsu saida suka tsorata,har muryarshi chanjawa tayi farat daya ya fara in i na,saboda dimaucewa,ya tabbata zaa gaya mishi wani abu ne gameda diyar tashi,duk yadda aka fasalta musu motar tata,da kala dakomai,don harda hoto ma,Abban ya rarraba dama,to an gani amma fa,ba da numbarta ba,an chanja num,"eh tabbas dole an chnaja num tunda tsohuwar ganinta akayi ai sharar gidan yallabai,"to anganta ne itadin?Tunda kace anga mota"Abban yace arikice don su mama ma dakowa dake wajen duk an rikice ana jira aji mezaice,"aa fa,baa ganta ba,don an ma saidawa wani motar,saboda wanda mukagani da motar bashida wata masaniya gameda hakan"kai innalillahi waninna ilahihi,rajiun,to ku tsareshi karku sakeshi,ku kamashi ku daureshi,harsai yagaya muku inda yasamu motar dakuma wanda ya siyar mai da ita,karya yake bazai rasa masaniya akan inda ya ta take ba"Abba yace cikeda dimaucewa,don gani yake kamar yansanda basa aikinsu yadda yakamata,"Alhaji calm down,shima yace wai a wajen wani yasiya,wanin ma damuka ganoshi yace a wajen wani yasiya kumabama dan garin nan bane"Haba officer, kadubi zancenka mana,wannan wace irin maganace haka,tayaya zaayi don yacemutumin yabar gari ku kyaleshi ai ku nemoshi harsaiya fada"yace cikin fada,"Alhaji you have to take it easy,wannan aikinmu ne fa,kuma munsan me mukeyi yanzun ma dabazan kira ka ba,har saina jira mun gama bincike tukunna mun kammala komai, but saboda yawan kira danake samu,shiyasa nace bari in sanar da dan cigaban daaka samu,muna kuma fatan muji Alkhairi ka huta lafiya ,"Amma dai off...."Officer ya kashe wayar,"ya kashemin waya,wallahi kashewa yayi"yace tareda dafe kanshi yanemi waje yazauna don wani jiri ne yake dibarshi,, su kuma su mama dukda dai agabansu akayi wayar amma so suke suji takamaimai me officer yace dashi,inda suka shiga bin baasi,duk yadda sukayi din ya kwashe musu,inda aka fara sallalami aka cigaba da kuka tunda dai baaganta dinba kuma mota ma ance an siyar.
Babu bata lokaci Abba yayi booking flight don tafiya maiduguri,don yace ko bakomai yaga dai motar tata wani abune.A cen kuwa,banda gana mata azaba da wahalar da ita matuka babu abindaakeyi,harta fara sabawa.
Ga shiga bandaki da da yake tsoratar da ita yanzu kam tasaba,don wani dan loko ne aka dan zagayeshi da kara,kasace kuma aciki sai dan rami daakyi dasunan masai,haka dai kowa yake shiga,kana wanka kasa tana fantsalo maka.
Tun washegarin zuwanta,tasamu ya kawo mata sabulu,data tambayi brush da toothpaste,yace mata gasucen a murhu,maana ta dandaka gawayi ta goge hakoran kowa ai haka yakeyi,watafi,amma fa shi yanada toothpaste dinshi da toothbrush.kullum dai aikin karuwa yake,don an kara mata ma akan diban ruwan,su girki tun tana kuskure tanacin duka harta iya,tunda iya tace iskanci ne abin tana sane take kin yimusu mai dadi,don kar asata gobe,ga wanki da wanke wanke,da yiwa yara wanka wanda yazama aikinta daiman,babu mai musu dole sai ita din,ga sharar tsakar gida, dukda dai sauranmatan ma sunayi amma fa nata yafi yawa.
![](https://img.wattpad.com/cover/179970084-288-k235625.jpg)