RUWAN DAFA KAI 2

2K 145 6
                                    

RUWAN DAFA KAI 2
Na SUMAYYA DANZABUWA

17

Haka dai abubuwa suka cigaba da gudana,ahankali tanata samun sauki tana kara murmurewa don  yadda maaikatan lafiyar suka tashi tsaye dasu kansu iyayen nata akan lamarin abin dai sai wanda yagani agaskiya ba karamin kokari sukeyi ba tabbas,don yanzu magana ma ras takeyi su zauna ayita hira hakan  kuwa ba karamin dadi yake musu ba,tunda ta tabbatar dacewar yanzu, fa komai agaskene yake faruwa bawai mafarki take ba,Allah sarki.

Kullum saitace su yafe mata dubada irin halinda ta tsundumasu ciki,tunda gani take duk laifinta ne ita ta kawo musu Abdallah cikin rayuwarsu baki daya har abubuwan dasuka faru suka faru,ba abinda suke cewa sai sun yafe mata duniya da lahira,Abba kuma yace idan akwai babban mai laifi bai wuce shi ba,atakaice dai kowa ya yafewa kowa,haka zalika itada safeena sunyi sulhu anmanta da duk abubuwan dasuka faru ada,komai dai mashallah abin sai wanda yagani.

Ganin hakane yasa Abba yace to yakamata  ashiga kotun yanzu tunda tasamu  kwarin jiki zata iya magana dakyau takuma kare kanta,dukda dai ya daukar mata lawyer,kuma dai basa dawwama ba a congo yanaso ayi shariar dazaayi ne ayankewa wayancen shashashun hukuncin daya dace dasu,sukuma su samu su koma cen gida Nigeria,hakan kuwa akayi.
Asibiti ma sun sallameta sun hadata da magunguna,tareda bata shawarar tarage tunane tunane takuma manta dakomai dukda dai hakn bawai abu bane mai sauki.

Babu bata lokaci aka shiga kotu kuwa,aiko da  aka gurfanar dasu shida iya gaban kotun jikinta ne yadau karkarwa farat daya  tafara kuka,cikeda tsoro don ganinsu ma  kadai yasa ta tunoda  da duk abubuwan dasuka faffaru akauyen nan gani take kamar zasu kara tafiya da ita.

Saida su mama suka  dinga bata baki suka kuma tabbatar mata dacewar  karyar su dai,su suna  nan wani abin yasameta,kar taji komai  suna nan a tareda ita babu inda zasuje,kuma kada tabari su bata tsoron komai tafadi duk abinda yakamata ta fada,shi daniskan ma ko lawyern ma bashida shi,yace baya bukata,shi zai kare su shida uwarshi tunda dai sufa akan gaskiyarsu suke,atunaninshi.

To abubuwan dai dasuka faru a wannan kotu bazasu fadu ba a wannan dan rubutun,don yadda yaga dama yadinga bada ansa waishi tantiri,yana wani babbad fadi yana zakewa,kuma yace bai taba ganin mugun mutum ba mai tsananin son kai Azzalumi irin Abba,ya aura mishi yarshi maana ya mallaka mishi ita kenan har abada,to nameye nashi dazai zake akan duk abubuwan dasuka faru,idan ba yankata yayi ya cinyeta ina ruwanshi,bayan kuma yarinyar nan itama tun farko azzalumar ce ta aureshi ne shima saboda cimma wani buri nata to donme zaa dinga ganin laifinshi shi kadai?,hmmm dukan dayaci a kotun nan bazai fadu ba,kuma alkalin yace koda faridan batace musu komai ba wayannan halayen dayake nunawa karara agaban kotu ma su kadai sun ishesu shaida da kuma hujjah.

Duk yadda lamura suke gudana acen kauyen nasu Alkali yace ta zayyaneshi mishi,ai kuwa babu bata lokaci tafada mishi komai babu abinda ta rage babu kuma wanda ta kara,da yadda suke rayuwa cikin jahilci,hasalima bama su da addini,ai ana zuwa nan,kowa akotun sai aka fara kuskus ana magana kasa kasa,"basuda Addini a wannan zamanin tab ?"shine abin mamaki,ko daakazo ta fannin irin rayuwar datayi tadai fadi abinda zata iya fada ragowar kuwa sai ta fashe da kuka,don ita kadai tasan meta gani,duk shariar fa anayinta ne cikin harshen turanci,tsakaninta da alkalin,saboda bayajin hausa,shikuma dan iskan da french din suke magana sai a fassara musu su da turanci.

"Munji munkuma yarda da hujjojinku"alkalin ya juya garesu shida iya,dasuketa faman zuba su adole masu gaskiya,"inda ace baka taba shigowa birni bane,tunda aka haifeka a wannan dajin kake to don abubuwa irin wayannan sun faru zamu iya maka uzuri akan cewar ka aikata ne cikin rashin sani,amma aa tun kana yaro kashigo duniya hasalima bama a kasar taka ka zauna ba kafita ka tafi wata kasa cen ta daban kanka ya dade da wayewa kaga rayuwa amma kacigaba da bari kuke rayuwa ahaka?kai wane irin azzalumi ne mugu?"Alkalin ya hayayyakomai cikeda bacin rai,"shikenan rayuwarmu  tun kakanni da kakanni sai ace zaa chanja mu rana daya?sai mu watsar da aladarmu  kenan bazai yiwu ba"iya ta kara,"wato kinsan dakomai kema kenan amma kuka biyewa son zuciya kuka cigaba da aikata abinda rankunyakeso ko"kwarai ma kuwa nasani sarai,aladar mu tafi mana komai dadi"ta kara,"addininku ko rashin addininku bashi bane damuwata anan,damuwata  shine yadda kuka dunkufe kanku babu ko ilimi na zamani,ga yara kunadasu dayawa kun dawwamar dasu cikin rayuwar kunci,ga yadda kuke gudanar da rayuwa da yadda kuka dauki mace baa bakin komai ba,tabbas yazama dole a hukun taku"to akan me memukayi dazaku wani ce zaku hukuntamu kusuwaye baku isa ba"ya hayyako"batareda wani bata lokaci ba alkali ya yanke musu hukunci daidai dasu don bama zai tsaya yana bata lokaci ba akan wayannan jahilan suna abu kamar mahaukata duk hujjojin dayake bukata don gano hukunci daya dace dasu  sunma fada da bakinsu don haka kuma zai  yanke musu hukuncin daidai dasu,"zaa muku hukunci ne dangane dawayannan  dalilai dazan lissafo,"yafara"an kama ku dumu dumu da  laifin satar yarinyar mutane,sannan kuma da horar da ita dakukayi kuka azabtar da ita har kuka kusa kasheta,an kamaku da laifin azabatar da yayan dakuke haifa dakanku wajen danne musu hakkin dayazama dole agaresu,ga kuma laifin sanin komai dakukayi amma kuka zabi  kucigaba da rayuwa cikin jahilci,wayannan ne manya manyan banda kanana  kanannan"yayi yan rubuce rubuce sannan yacigaba,"don haka kotu ta yanke muku hukuncin  zaman gidan yari na shekaru 20,tareda horo mai tsanani,sannan hukuma tanada damar dazataje cen din(kauyen nasu)ta kwashe dukkanin mutanen dasuke rayuwar a wannan wajen ta maidasu inda zasu waye sukuma sami rayuwa  mai inganci,nagaya muku ne don ku sani,amma  bawai neman izininku ake ba abinda yakamata ne zaayi,"wanann zalumci ne,bazamu yarda ba"yacigaba  da hayayyakowa,wane irin shekara ashirin kashemu kukeso kuyi?","bangane ba inane gidan yarin?"cewar  iya fuskarta daukeda damuwa,"Nagama magana",alkali ya buga wanann dan abin dasuke bugawa  dazarar an gama sharia,ya tashi ya tafi sauran  jamau  aka fara  watsewa.
Iya dai sai kuka take,don bata masan meke shirin faruwa ba tadaiji ance horo mai tsanani.
Har sunzo zasu fita saikuma ta tsaya,
"Kun cutar dani,kun wulakantani, kun kaskantar dani,saboda duk kunyi tunanin shikenan mafita bazata taba zuwar min ba ko?haka kawai kuka zabi ku kasheni bayan ban muku komai ba,koda nayi din ma ai na nemi yafiyarku amma kuka cigaba da cutata,hmmm inaso in kara tabbatar muku dacewar Lallai ku yarda akwai Allah,don da babu shi da duk abubuwan nan dasuke kan faruwa basu faru ba,kusani shi mai ji ne kuma mai gani,Shine kuma yacetoni daga hannunku ya kuma tona muku asiri,duk abubuwan dasuke faruwa daku yinshi ne bayin kowa ba,kunsan gaskiya kuke takewa"hawaye yafara zubowa,"Gaya musu dakyau,idan masu rabone su dace"Cewar safeena,"shawarata ta karshe agareku shine idan har kunason  ku dace,kar ku kasance kunyi  zuwan banza duniya zaku koma abanza to kuyiwa kanku fada ku rungumi musulumci,idan kuma zaku cigaba da zama ne kan bakanku yadda kuke so to rayuwa ce dai,gatanan,zaku shiga kangin dayafi wanda kuka sakani aciki,ni na yafe muku,dukda kuwa ku bazaku nemi yafiyar ba,abinda  kuke ciki ma ayanzu ya isheku,Allah ya shiryeku yakuma ganar daku",suka fice batareda sun jira jin wata ansa ba daga garesu.

RUWAN DAFA KAI 2Where stories live. Discover now