RUWAN DAFA KAI 2

1.5K 126 6
                                    

RUWAN DAFA KAI 2
Na SUMAYYA DANZABUWA

24

Cikin sanyin jiki Abu tafito tazo tazauna,tacigaba da tunane tunane,"aa Baby meya faru ne,naga kin shiga kin dade kuma kin fito haka"yace fuskarshi daukeda damuwa cikeda kulawa,yana mai tsareta da idanu,murmushin dole ta kakalo,don bata masan mezai tace dashi ba,kuma bataso koda wasa yagano abinda ta aikata,"bakomai, kawai dai kaina ne yake dan min ciwo"tace,tareda dan dafa kan,"Ayya sannu,bari in dauko miki magani to"yatashi a hanzarce yashiga daki don dauko mata maganin,"hmm,to nidai kokarina ya kare Allah yasani wannan shine abun dazan iyayi na karshe dama (na neman faridan a awaya dakanta )kuma nayi amma babu nasara, shin in fada mishi zancen auren nata ne ko kuwa in rabu dashi  har saiya ji dakanshi?"tacigaba  da shawara da zuciyarta  hardai yafito.

Farida na kitchen wayarta tafara kara alamun shigowar kira,bata duba bama saida tagama abinda take,tukunna sannan ta dauko wayar,numbar congo tagani,saida gabanta yabada ras,"to waye kuma zai kirata"tace aranta cikeda mamaki da tsoro, saida tagama adduointa na neman tsari daga sharri sannan tayi shahada bayan ta saki ajiyar zuciya tafara kira,saidai kuma me muryar sadiya taji,hakan neyasata sake ajiyar zuciya,cikeda farinciki da murna kuwa suka gaisa sosai,sannan suka shiga dan taba hira inda take tambayarta babu dai wata matsala ko yarinyar tace babu komai sauran matan gidan nema da sauran yanuwan sukace ta kirata su kara mata godiya sun gode sosai,saida kowannensu ya karbi waya suka gaisa yamata godiya sannan suka kara bata hakuri akan irin abubuwan dasuka faru abaya tace bakomai komai ya wuce abar tuna baya ma,sannan sukayi sallama sadiyan ta karbi wayar,harkar karatu da ibada,dakuma sauran alamura na yau da kullum Faridan ta tattambayeta  tace ai suna nan sunayi sosai babu wasa,kuma komai lafiya kalau suna cikin jin dadi da kwanciyar hankali,"'Mashaallah,Alhamdulilalh Allah ne abin godiya,shi zaku dinga godewa akoda yaushe kinji sadiya bawai ni ba"tace da yarinyar,saida yarinyar tadan kebe ita kadai sannan take bawa faridan labarin zuwansu gidan yari ganin babansu da kuma kakarsu,"wallahi sun zama abin tausayi sai cewa suke mu yafe musu,wai kema mufada miki suna neman yafiyarki don sunsan ba lallai su fito da rai ba,to mudai muce mun yafe musu saboda yadda suka bamu tausayi,kuma mun basu shawara su karbi musulumci suma kamar yadda mukayi sunce sunma karba ashe"cewar yarinyar,"Allahu Akbar,kun kyauta sosai sadiya Dakuka yafe musu,kuka kuma basu shawarar  dazata amfanesu,haka akeson musulmin kwarai ya kasance a kullum cikin yafewa dan uwanshi dakuma neman yafiyar shi kanshi,nikuma dasuke zancena ai agabansu nace nayafe musu sundai mantane,nawace ma duniyar damutum zai zauna yana saka abu aranshi,in mune yau fa gobe bamu bane rayuwar nan babu tabbas"tace da yarinyar,haka dai suka dan cigaba da taba hira sannan sukayi salllama.

Hakika taji dadin kiran nan  matuka, ashe dai basu manta da ita ba, Allah sarki itama takan tunasu lokaci lokaci kawai dai bataso ne tasasu aranta dayawa harta shiga wata damuwar,don ko ba komai idan ta tuno yadda tazama sanadin tsiransu takan godewa Allah taji dadi marar misaltuwa nacewar wai yau itace tayi sanadin wani ya karbi addinin musulumci,tazamo sanadin shiriyar wasu,kai tabbas babu abinda yakai wannan dadi,Alhamdulillah.

"Mine in maka wata yar tambaya mana"Abu tace ganin dai takasa daurewa,itafa dolene tafitoda abinda yake ranta,tunda tayi tayi taga ta fuskantar dashi yaki fuskanta,wani kallo yafara mata don sanin inda ta dosa tunda sararta ce kwanan nan indai zatayi zancen farida sai tafara tahaka,"to yau kuma menene kar dai kicemin zancen f...."don Allah don Annabi abar abinnan haka"takatseshi ahasale,sai kuma tayi shiru,baki bude kawai yabita da kallo cikeda mamaki,sai kuma ta sunkuyi da kai,don ita kanta batasan tayi ba,"zainab!ni kike dagawa murya yau akan wata?"yace cikin sanyin murya don yusuf baya fada barema ya daga murya,komai coool,"Don Allah don Annabi kayi hakuri,wallahi ba manufata ba kenan,ka yafemin"tayi narai narai da ido tafara hawaye,"kin bani mamaki wallahi,abinda baki tabamin ba,amma  akan wata wai kike daga mun murya,saboda ina neman in kareki in tseratar dake ko?yayi kyau"Shiru tayi ta kalli kasa ,harga Allah  tarasa ta indazata bullowa lamarin,to yaki ya chanja yakuma janye bakanshi akan abin,ya yakeso tayi,shi yasa tafara  hasala  kuma,"mine"tace dakyar bayan ta share hawayen dake zubowa,ko kallonta baiyi ba,"Muma mutane munayiwa Allah laifi ya yafemana,mu aikata manya manyan zunubai da hankali ma bazai dauka ba,Allah kuma  ya yafe mana batareda ya dauke ko ya hanamu wata niima daya mana ba,kamar iskar damuke shaqa,ko idanuwan damuke gani,ko kafafauwan damuke tafiya,ko kuwa kunnuwan damuke ji ba,ton don Allah don Annabi kai kace ka yafewa baiwar Allahn nan,to meye aciki don ka dawo da ita,koba komai fa kadaina mantawa tanada  da tareda kai,kuma tanada hakki akan yaron  nan itama,wane irin fushine kakeyi haka da ita da ni nakasa ganewa?"tace cikeda ladabi,murya kasa kasa,kallonta kawai yayi ya saki murmushin dole,cikeda mamakinta dakuma tausayinta tunda ya fuskanci tsantsar yarinta ce take dawainiya da ita bata gama sanin me takeyi ba bare tasan me duniya take ciki,"zainab kenan"yafara" nifa don ke nakeyin duk abubuwan nan danakeyi ba don wani ba,ke baki san wacece farida ba,shiyasa har kike marmarinta,kike kuma neman ma ki bata min raina  ki kuma bata naki akan sabgarta"naji bansan wacece ita ba,amma kuma kai da bakinka kacemin duk abubuwan data aikata maka ka yafe mata su ko?"gyada kai yayi alamun eh kawarai ma kuwa,"to idan dagaske kayi yafiyar to ka aureta mana"tasake cewa,"wai tsaya,kece mijin?nace kece mijin?"tayi shiru,"aifa sai kin bani ansa"ya titsiyeta,girgiza kai tayi alamun aa,"yawwa,tunda kin bada ansa dakanki,nidai nine mai auren ko?to nace bazan iya aurarta ba,idan baso kike kiga bacin raina ba zainab karki sake min zancen farida agidannan kinjini ko?, ke da har yaushe kika santa ma dazaki bada shaida,macen da saboda  tsananin kishi zata iya kasheki takuma kasheni da hannunta batareda wata damuwa ba,shine har kike fatan in kawo miki ita kuyi rayuwa tare,ko kuwa ba agaban idanunki komai ya faru ba,kina gani fa akan tazauna dake ta gwammace ta rabu dani da dan data haifa gabaki dayanmu,sanna ta watsra da lamuranmu,haba zainab ya kike magana ne kamar wata zainab din tadaban,dabatasan me takeyi ba?"ganin yana neman  ya hasala ne yasa tafara bashi hakuri,amma inaa tariga ta taboshi sai mita yake ta inda yake shiga bata nan yake fita ba,"Shikenan,Allah yabaka hakuri,inshaallahu daga yau bazan sake maka zancenta ba inshaallah"tace tana hawaye.

Shifa yusuf tsakani da Allah akan gaskiyarshi yake masu karatu,shi bazai taba gane wannan chanji ba na farida, tunda shidai yasan wace irin macece ce har zuwa rabuwarsu,bai hadu da ita ba har yanzu bare yace ga chanjin dakaa samu,shiyasa bazai kuskura yabari  ya tafka  kuskure ba,haka kawai,kudaina ganin laifinshi yariga yasan wahalar dayasha abaya shiaysa,kuma kunsan hausawa nacewa mai halifa baya fasa halinshi,ko kune a matsayin dayake abinda zaku aikata kenan.

RUWAN DAFA KAI 2Where stories live. Discover now