RUWAN DAFA KAI 2

2.1K 142 1
                                        

RUWAN DAFA KAI 2
Na SUMAYYA DANZABUWA

6

Kodata farka hasken fitilar kwan dake dakin ne ya dallare mata idanu,dama daki ba daki ba,alamun har  dare yayi kenan,sabon kuka tafara don batasan meke faruwa ba,kanta ya riga ya kulle,wato abin nashi yakai innaniha daya siyar da ita ma kenan,tunda dai gata gidan yan yankan kai,babu tantama gidan nan gidan yan yankan kai ne,ita yanzu meye abinyi,ya zatayi?ahankali ta mike,tafara sanda,wai ta fito tagudu tunda ta tabbata dai yadda taji ko ina shirun nan kowa yayi bacci.

Tana  shirin fitowar ne taga an daga labulen kofar,an shigo,shi tagani sanye da yar jallabiya yana washe mata bakin nan na iskanci kamar yadda yasaba,hakan ne yasata share hawayenta ta tamke fuska,"Kai Abdallah,yafa zama dole kamin bayanin abinda yake faruwa,don bazai yiwu ba kamaidani mahaukaciya ta karfi da yaji "tace  batareda wata kwayar  tsoro ba cikin muryar tata,"inane nan ka kawoni?",ko kulata baiyi ba yacigaba da murmushi saima kwanon daya shigo dashi yazo ya dire mata agabanta,yajuya zai fita,"wai ba magana nake maka ba zaka maidani wata shashasha,taraka fa nake!"tace cikin tsiwa dakuma kuka,ganin yana neman yamaida ta wata kwar kwar don yamaki kulata,"au,toh,madallah wato harkinyi saurin mantani kenan ko?lallai kinada saurin mantuwa nace har kinyi saurin manta kowanene ni dakike wannan ihun,kicigaba kindai san sauran ai,"yace bayan ya dakata,"anyi makan,nace anyi makan kai waye inba macuci azzalumi ba mayaudarin banza da wofi mtsw"tasake cewa,"har yanzu tambaya kike wanene ni ko?bayanin dakikaji wajen mutumin nan(yallabai) bai isheki ba kenan?,to duk abinda yafada  hakane,namafi ga haka ai ke shaidace,ko kuwa duk wayannan abubuwan dasuke kan faruwa basu isa su zamto ansa ba ga tambayoyinki?mtsw"ya juya  zai sake fita abinshi,kuka tafara sosai ,"don Allah don Annabi meyasa kake min haka,mena maka,kaketa cutar dani,don meyasa danace kasakeni  kaki sakina bayan dani dakai  ayanzu munsan cewa ba kaunar juna muke ba,meyasa kazabi kacigaba da hukuntani akan abinda bansan hawa ba bansan sauka ba,meyasa kake wulakantani haka?"tacigaba da kuka,"ko?baki ma san ke kikayi ba?to zaki sani ne dasannu"ganin kukan nata bazai amfaneta ba ne yasa tafara share hawaye,"shege azzalumi wallahi sai Allah yasakamin"tace afusace,"ke!nikike gayawa  haka?tabas inda agaban idon jamaar garinnan  ne da sai an fille miki kai inbakiyi wasa ba,mijin naki?"yace a fusace tareda shako ta tafara numfashi dakyar,tana bada hakuri,don har kakari take,"wallahi idan kika sake fadar wani abu dabai gamsheni ba ko wata tambayar iskanci ta son ranki saina  karasaki,in karya wayannan tsinanun kafafuwan masu kamada muburgi"yace bayan ya sa kafa ya takesu,ta kwala wani  ihu kuwa,dogon tsaki yaja ya fice,tana jiyoshi yana turo wani abu daidai kofar da alamun rufeta yake kenan  tunda dai wagga kofa batada murfi.
"Nashiga uku,na lalace ya Allah kasa mafarki nakeyi"tacigaba da kuka.

Saida tayi mai isarta cikeda danasani da nadama,sannan  tajawo kwanon daya kawo mata,da har zatayi ball dashi dazu,saboda bakinciki,saidai ta barshi don yunwar datake ji abin baa cewa komai,kamar taci babu,budewa tayi taga shinkafa fara,sai dan mai daaka yaryada, cikeda yunwa ta duma hannu ta farwa  abincin saida tacinye shi tas,dama kuma bawani yawa bane dashi sannan tanufi randar data gani a cen kuryar dakin ko murfi babu sai wani dan kofi aciki,da tun dazu tadinga kallo cikeda kyama tana mamakin yadda zaayi ace mutum ne zaisha ruwan ciki to ashe dai mallakinta zata zama,don idan ma tace bazatasha ba batasan mezai biyo baya ba wata kila kishirwa ta kasheta.

Kasancewar dakin kasace ta mamayeshi hakan yabata  damar yin  fitsarinta a kuryar dakin,ta watsa kasar akai,sannan tayi alwala duk da ruwan randar,sannan ta tada, sallah don bata ma san lokacin ko karfe nawa bane tasan dai kawai darene tabbas  ahalindaake ciki babu abinda yake sata nutsuwayake kuma kwantar mata da hankali  kamar sallah da ambaton Allah.

"Alhaji kunyi magana kuwa da yarinyar nan"mama take sake tambayar Abba,"wace yarinya?"yace cikeda rashin fahimta yana latse latsen wayarshi,"farida mana","yaushe kenan bamuyi ba meya faru?"ya jero mata tambayoyi,"bakomai,wayoyinta ne dai har yanzu shiru,kuma wallahi hankalina yakasa kwanciya haka kawai nakejin wani iri ajikina ina wasu mafarkau marasa dadi inaga zanje gobe inshaallah in ganota,don abin dai da mamaki  yau kwana kusan nawa ace duk wayoyi baa samu duk maitar wayarta kuwa...."dariyar Abba ce ta kastse mata zance,ta tsaya kallonshi shekeke,"sau nawa zan fada miki ne ki kwantar da hankalinki ki rabu da lamuran yaran nan,don Allah ji yadda kikabi kika tada hankalinki kamar wai bakisan halin yaran zamani ba,ai tashen dasukeyi  kenan inma bakisani ba kisani daga anyi aure sai akashe wayoyi anacin amarci, wai don ma kar ayita kiransu ana takura musu,ko wata kila ma irin honeymoon dinnan suka tafi,don shima kinsan sundaina shelar tafiya saidai aji sun dawo ko agansu suna posting hotuna a social media duk wannan babu wani abin mamamki aciki  gwara ma kicire duk wani abu daga ranki ki kwantar da halinki don ni kam inada tabbacin  komai kalau"yace har lokacin bai bar murmushin ba, "toh hakane,amma yanzu su sai su tashi su tafi har wata kasa bazasu fadawa kowa ba hakan ya kamata babu sallama bakomai?"tasake cewa,"a ahap,ai yaran zamani kenan,duk abinda kike tunani sun wuce nann"yace,"to Allah ya kyauta,amma dai wani hanzari ba gudu ba,kardai wai kaga na dage mai zai hana tunda ita tata wayar baa samu ka gwada kiranshi  shi abdallahn kaji tunda ni banida numbarshi" yar dariya kawai yayi,tareda girgiza kai na irin  kindai matsa dinnan kin dage,sannan ya zaro wayarshi,don ko wayar ma dai ba tabayi sukayi ba,kawai dai lokacin harkar neman auren yacewa faridan tabashi numbar shi,kiran numbar farko yafarayi  akace"the number you are trying to call dosent exist"dayar kuma switched off,"ahaf kinji dai dakunnenki ko? ai nagaya miki dama" yace kasancewar a handsfree yasaka,"shikenan kuma sai suka zabi su kashe wayoyi dukansu saboda shashanci? to ai shikenan wannan dai ba dabia bace" cewar mama cikeda rashin jin dadin  hakan,yar dariya Abba yayi  kawai.

Itadai intayi kamar ta manta saita tuno hankalinta kwata kwata ya gagara kwanciya duk iyaka bakin  kokarinta kuwa wajen ganin ta daure,amma inaa tana cikin damuwa,a halin daake ciki tariga tagama yanke shawarar zuwa gobe idan tasake kira batasameta ba  to zata tasa sauda agaba suje su ganota,tunda tasan gidan(saudan).

RUWAN DAFA KAI 2Stories to obsess over. Discover now